dankwambo ne uban ’yan PDP a Gombe ba Goje ba- Junaid Usman

Junaid Usman Abubakar shi ne mai ba Gwamnan Jihar Gombe shawara kan harkokin yada labarai, ya mayar wa tsohon Gwamnan Jihar Alhaji danjuma Goje martani bayan ya ce shi ne shugaba kuma uban ’ya’yan Jam’iyyar PDP a Jihar. Ya ce dankwambo ne uban jam’iyya ba Goje ba. Aminiya: A kwanakin baya ne aka ce tsohon […]

dankwambo ne uban ’yan PDP a Gombe ba Goje ba- Junaid Usman

Junaid Usman Abubakar shi ne mai ba Gwamnan Jihar Gombe shawara kan harkokin yada labarai, ya mayar wa tsohon Gwamnan Jihar Alhaji danjuma Goje martani bayan ya ce shi ne shugaba kuma uban ’ya’yan Jam’iyyar PDP a Jihar. Ya ce dankwambo ne uban jam’iyya ba Goje ba.

Aminiya: A kwanakin baya ne aka ce tsohon Gwamna danjuma Goje ya kasa shiga jihar a dalilin komawarsa sabuwar PDP. Me za ka ce a kan haka?
Junaid: Da farko ina so ka sani babu wata aba wai sabuwar PDP a Gombe. PDP kawai muka sani don haka babu batun an hana wani shigowa Gombe don abin da babu shi. Har yanzu akwai shari’ar Goje a kotu a nan Gombe amma yanzu ya rubuta wa jami’an tsaro cewa rayuwarsa tana cikin hadari.  Yana so ya nuna wa jama’a har yanzu shi wani ne da zai iya hayar ’yan baranda su rika ta da hayaniya. Haka ya sanya mahukunta suka kawo dauki domin Gwamnan ba zai nade hannunsa yana gani ana taka doka ba, domin babu wanda ya fi karfin doka komai girman mutum a Gombe, kada a manta Gombe na daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya.
Duk da cewa ya yi haka amma me ya faru washegari? Fiye da mutum dubu 500 suka yi zanga-zangar adawa da Goje. Kowa ya ga hotunansu. Damuwarsu Goje ya kare kansa daga laifin da ake tuhumarsa ba ya kaddamar da kamfe ba. Ina gaya maka wadannan mutane da suka yi zanga-zangar suna neman a yi gaskiya da adalci ne cikin gaggawa.
Aminiya: Takaddama ta barke a kan wane ne uban ’ya’yan PDP a Jihar Gombe inda Goje ya ce shi ne uban ’ya’yan PDP. Mene ne ra’ayinka kan haka?
Junaid: Wadanda suka kafa PDP tare da su Sunday Awoniyi su ne Dokta Suleiman Kumo da Ambasada Yerima Abdullahi dukkansu mutanen Gombe ne kuma hadin kan da suka samu daga mutanen Gombe ne ya sa suka kafa PDP, kuma sakamakon hadin kan wadannan dattawan ne mutanen Gombe suka rungumi PDP hannu bibbiyu. Idan kana maganar siyasar yanzu ne sai mu ce duk wanda ya zama Gwamna shi ne uban jam’iyya a jiharsa kuma haka za a ci gaba. Haka ya sanya wadansu su tafi; wadansu su zo a kuma ci gaba da ayyukan jam’iyya. Jam’iyya ce da kullum take kara girma, jam’iyya ce da take maraba da kowa. Ita ce jam’iyya mafi yawan jama’a a Afirka, tana karbar jama’a kowace rana a Jihar Gombe. Amma Goje ya manta akwai dattawa irin su Dokta Suleiman da Ambasada Yerima. Su ne suka kafa Jam’iyyar PDP a Gombe.
Aminiya: Amma Goje ya ce Gwamna dankwambo ba ma dan siyasa ba ne, shi ne ya koya masa siyasa a lokacin da ya nemi ya shiga Jam’iyyar PDP. Me za ka ce?
Junaid: Ai shi Goje ya ga wadansu halayen kwarai a tattare da dankwambo ne da ba kowa yake da su a Najeriya ba. dankwambo yana da halayen da ya kamata ya taka kowane irin matsayi a Najeriya. Ya kuma rike matsayin Babban Akanta Jihar Gombe. Ya yi aiki da tsohon Gwamna Hashidu, haka da Goje, sannan cancanta ta sa ya zama Babban Akanta Tarayya, inda ya rike mukamin har ya yi zamani da shugabannin kasa uku. Kuma duk wadannan shugabannin kasar ’yan PDP ne. Don haka a cikinsu wane ne ya fi kwarewa da sanin makamar aiki?
Aminiya: A wasu jihohi akwai siyasar ubangida kamar a Jihar Kwara inda Gwamnan Ahmed ya amince Bukola Saraki shi ne uban jam’iyya. Mene ne ya bambanta can da Jihar Gombe?
Junaid: Ba mu san wata siyasar ubangidanci a Gombe ba. dankwambo ba ya da wani uba a Gombe idan ba mahaifinsa ba. Kowa ya san wane ne marigayi Talban Gombe a Najeriya. Marigayi Talban Gombe sanannen dan kwangila ne da ya horar da ’ya’yansa suka kuma yi karatu tun daga nan Najeriya har zuwa makarantar kasuwanci ta Harbard da ke Amurka. Don haka dankwambo ba ya da ubangida.
Aminiya: Idan haka ne wane ne uban ’ya’yan PDP a Gombe?
Junaid: Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim dankwambo ne shugaba kuma uban ’ya’yan PDP a Jihar Gombe, saboda shi ne Gwamna a halin yanzu, kuma a karkashin PDP bayan halattaccen zabe ya zama Gwamna. Sun shirya masa gadar zare don ya fada tarko har a bata masa suna amma ba su samu nasara ba. Bayan ya zama Gwamnan sai ya zo da dabaru da tsare-tsaren da suka sanya yanzu Jihar Gombe ta zama daya daga cikin kyawawan jihohi a Najeriya. dankwambo ya gina tituna 116 cikin shekara biyu, ya hada gwiwa da Bankin Masana’antu inda ya zuba hannun jarin Naira biliyan hudu don inganta masana’antun jiharmu. Ya bunkasa harkar noma inda ya sayo sabbabin taraktoci 220 kowace a kan miliyan uku da rabi.
Don haka idan wani ya shiga gari yana kwarmaton shi ne shugaban ’ya’yan PDP a Gombe domin a cewarsa a lokacinsa jama’a da yawa sun yi aure, sun je aikin Hajji, ya biya ’yan kwangila kudinsu, ya gina filin jirgin sama da jami’ar jiha sai na ce bai yi daidai ba domin ba da kudinsa ya yi ayyukan ba, domin haka jama’a suka zabe shi. Ana magana ne a kan ayyukan da za su amfani jama’ar Gombe kuma su ne Talba yake yi a halin yanzu. Idan ka gina jami’a sannan akwai dalibai dubu 20 da suka kasa samun sakamakon da zai ba su damar shiga jami’a to mene ne amfanin gina jami’ar? Bayan Talba ya zama Gwamna sai ya samo kwarrarun da za su karantar da wadannan dalibai dubu 20 din wadanda suka fadi jarrabawar WAEC.
Yanzu idan ka tafi kogi ka kama kifi sai ka samu wani mutum a gefe ka mika masa kifin sai ka ce ka taimake shi? A’a, ba ka taimake shi ba, idan kana so ka taimaki mutum sai ka koya masa yadda zai kama kifin. dankwambo bai gaji komai a Gombe ba amma a yanzu Gombe tana daya daga cikin jihohin Najeriya da suka bunkasa. Babu wanda zai zo ya rika gaya mana ya taimaka wa daidaikun mutane.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50