Dankwambo ya himmantu wajen dukushe Buhari a Gombe – Hon. Yusuf
Tsohon dan takaran dan majalisar Jihar Gombe, Hon. Yusuf Ahmad ya bayyana cewa kananan hukumomi 11 sun gagari Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, amma yake hankoran fitowa takarar shugabancin kasa a 2019. Hon. Yusuf ya fadi haka ne a yayin ziyarar da ya kawo ofishin Aminiya a Abuja a ranar Talatar da ta […]

Tsohon dan takaran dan majalisar Jihar Gombe, Hon. Yusuf Ahmad ya bayyana cewa kananan hukumomi 11 sun gagari Gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, amma yake hankoran fitowa takarar shugabancin kasa a 2019.
Hon. Yusuf ya fadi haka ne a yayin ziyarar da ya kawo ofishin Aminiya a Abuja a ranar Talatar da ta gabata, inda ya nuna takaicinsa game da yadda Gwamna Dankwambo ya umarci ‘yan sanda da bindigogi da su rika cire fatocin Shugaban kasa, Muhammadu a ko’ina cikin birnin Gombe da kewayi, yana fakewa da cewa wai lokacin siyasa bai yi ba.
Matashin dan siyasar ya ce suna da tabbacin Gwamnan Jihar Gombe ne ya dauki nauyin gudanar da zanga-zangar cewa Buhari ya sauka a kwanakin baya, “Muna da tabbacin cewa Gwamna Dankwambo ne ya dauki nauyin zanga-zangar ta da zaune-tsaye da aka yi kwanakin baya cewa Buhari ya dawo ko ya sauka, inda ya kashe miliyoyin kudaden al’ummar jihar.”
“Sannan a yanzu kuma da wancan hakar tasa ta gaza cimma ruwa, ya sake fito da wata hanya wacce a zatonsa za ta dusashe hasken Shugaba Buhari, inda ya umarci ‘yan sanda da bindigogi ana ta cire fastocin Buhari a duk inda aka gansu a fadin jihar baki daya. To muna yi masa hannunka mai sanda cewa ya bi a hankali, domin fada da Buhari fada da al’umma ne, fada da al’umma kuma kowa ya san babu nasara, to muna tsaorata masa yin faduwar bakar tasa,” in ji Yusuf.
Haka zalika Hon. Yusuf ya kara bayyana cewa “Tun da farko ma gwamnan ba cin zabe ya yi ba a jihar, sannan kuma yake ci gaba da mulkin kama-karya, ya hana albashi, ya daina biyan ‘yan fansho, sannan ya daina bada kwangoli ga ‘yan jihar sai yarabawa da inyamurai, wadanda kuma ya suka yi kwangilar a baya ya hana su kudinsu. Sannan wahalar ruwan sha ta dawo, sannan babu wutar lantarki, sai zaluncin cinye kudaden jiha da sunan kwalta,” a cewar Hon. Yusuf