dankwambo ya nada Mukaddashin Sakataren Gwamnati

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ya nada Mista James Pisagih, a matsayin Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar. Wata takarda da aka raba wa manema labarai dauke da sanya hannun shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Ahmed Usman, ta ce nadin ya fara aiki ne nan take.Kafin nadin Mista James Pisagih a matsayin Mukaddashin Sakataren Gwamnatin, […]

dankwambo ya nada Mukaddashin Sakataren Gwamnati
dankwambo ya nada Mukaddashin Sakataren Gwamnati

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ya nada Mista James Pisagih, a matsayin Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar.

Wata takarda da aka raba wa manema labarai dauke da sanya hannun shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Ahmed Usman, ta ce nadin ya fara aiki ne nan take.
Kafin nadin Mista James Pisagih a matsayin Mukaddashin Sakataren Gwamnatin, shi ne Babban Sakataren Ayyukan na Musamman a Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar.
Mai shekara 59, Mista James Pisagh, ya samu digirinsa ne a Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya, kuma ya amshi ragama ne daga tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Abubakar Sule bage.
Mista James Pisagih, ya fara aiki ne a matsayin mataimakin sakatare na II har ya kai matsayin Babban Sakatare kafin a nada shi a wannan mukami.