dankwambo ya yi wa kwamishinoninsa garanbawul

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo, ya yi garambawul ga Majalisar Zartarwarsa inda ya nada sababbin kwamishinoni shida da sabon Shugaban Ma’aikata naJiharA lokacin da yake rantsar da sababbin kwamishinonin a gidan gwamnati, Gwamna dankwambo ya hore su da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu don sauke nauyin da aka dora musu.Gwamnan ya nemi […]

dankwambo ya yi wa kwamishinoninsa garanbawul
dankwambo ya yi wa kwamishinoninsa garanbawul

Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo, ya yi garambawul ga Majalisar Zartarwarsa inda ya nada sababbin kwamishinoni shida da sabon Shugaban Ma’aikata na
Jihar
A lokacin da yake rantsar da sababbin kwamishinonin a gidan gwamnati, Gwamna dankwambo ya hore su da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu don sauke nauyin da aka dora musu.
Gwamnan ya nemi sababbin kwamishinonin su hada kai da manyan sakatarori da daraktocin ma’aikatu don ba wa kowa ’yancin ya tafiyar da aikinsa yadda ya dace.
Ya ce daga lokacin da aka nada kwamishinoni sun zama dattawa a tsakanin al’umma inda ya ce ba sai mutum ya tara shekaru ne zai zama dattijo ba.
Da yake jawabin godiya a madadin sababbin kwamishinonin Alhaji Bakura Muhammad Bajoga, dan Amar din Funakaye, tabbatar wa Gwamnan ya yi cewa ba za su ba shi kunya ba wajen sauke nauyin da aka dora musu.
Sababbin kwamishinonin sun hada da Alhaji Shehu Abubakar Durbi, Kwamishinan kasa da Safiyo sai Alhaji Bakura Muhammad Bajoga Kwamishinan Ciniki da Masana’antu sai Asma’u M. Iganus Kwamishinar Tattalin Arziki sai Alhaji Abdullahi Kulani, Kwamishinan Jam’iyyun Gama-kai da Yaki da Fatara sai Misis Rabi Daniel Kwamishinar Muhalli da Kare Gandun Daji sai Hajiya Sa’adatu Mustapha Kwamishinar Mata da Walwalar Jama’a.
Kwamishinonin da aka yi wa canjin wuraren aiki kuma sun hada da Hajiya Fatima Shehu Abubakar daga Ma’aikatar Mata zuwa Ma’aikatar Tsara Birane sai Alhaji Babagoro Abdulkadir Yahaya daga Ma’aikatar Bunkasa Tattalin Arziki zuwa sabuwar  Ma’aikatar Kula da Dabbobi da Walwalar Makiyaya, inda kwamishinonin jihar suka zama 25.
Gwamnan ya rantsar da Alhaji Aliyu Kamara Alhaji a matsayin Shugaban Ma’aikatan Jihar.