danliti da soja
Wani saurayi ne ya dauko kakarsa a mota zai kai ta anguwa, yana sanye da wandon sojoji, sai aka zo wajen da soja ke duba ababen hawa. Sojan da ke duba motocin mutane ya ce masa: “Ka fito a duba bayan motarka.” Sai ya ki fitowa. Aka yi, aka yi ya fito, ya ki. Da […]
Wani saurayi ne ya dauko kakarsa a mota zai kai ta anguwa, yana sanye da wandon sojoji, sai aka zo wajen da soja ke duba ababen hawa. Sojan da ke duba motocin mutane ya ce masa: “Ka fito a duba bayan motarka.” Sai ya ki fitowa. Aka yi, aka yi ya fito, ya ki. Da kyar dai aka samu daga karshe dai ya fito. Yana fitowa ya falla wa sojan nan mari. Soja ya tsorata, ya kame, ya sara masa gaisuwar soja, domin ya dauka ko wani babban soja ne.
Ana haka can sai wani soja daga nesa ya hango abin da ke faruwa sai ya taso ya zo, ya ce: “Me ke faruwa ne?” Shi ma saurayin nan ya falla masa mari. Kwatsam sai kakar saurayin nan ta fito daga mota a firgice, ta ce: “danliti, kai ba hukuma ba, amma kana marin hukuma!” Kafin tsohuwar ta gama magana, tuni matashin ya cika wandonsa da iska.
Daga Aminu dankaduna 07065654787