danmadamin Kano ya shekara 30 yana jagorancin al’umma

Idan Allah Ya so gobe Asabar garin bakwai Hedkwatar karamar Hukumar bagwai da ke cikin Jihar Kano, kuma kimanin kilomita 75 zuwa 80, a Arewa maso Yammacin Kano, ake kyautata zaton zai yi cikar kwari wajen karbar bakuncin jama`a na kusa da na nesa dangane da bikin cika shekaru 30 cif-cif akan karagar mulkin gundumar […]

danmadamin Kano ya shekara 30 yana jagorancin al’umma
danmadamin Kano ya shekara 30 yana jagorancin al’umma

Idan Allah Ya so gobe Asabar garin bakwai Hedkwatar karamar Hukumar bagwai da ke cikin Jihar Kano, kuma kimanin kilomita 75 zuwa 80, a Arewa maso Yammacin Kano, ake kyautata zaton zai yi cikar kwari wajen karbar bakuncin jama`a na kusa da na nesa dangane da bikin cika shekaru 30 cif-cif akan karagar mulkin gundumar ta bagwai da Hakimin masarautar kuma danmadamin Kano Alhaji Nura Shehu Ahmad zai yi.

Kafin in yi nisa ya kamata in dan waiwayi baya kadan cikin tarhin rayuwar, dan Madamin na Kano, Alhaji Nura Shehu Ahmed. dan Madamin na Kano, shi ne da na uku cikin `ya`yan shararren Madakin Kanon nan Alhaji Shehu Ahmed dan Madaki Muhammadu dan Yusuf. Madaki Shehun da yake shararren dan boko, kasaitaccen Basarake, kuma kuma Attajiri da ya share shekaru 31 yana rike da Sarautar Madaki (1953 zuwa 1984) da Allah Ya amshi ransa.
An haifi Alhaji Nura Ahmed a ranar 10 ga watan Yulin 1957, a unguwar Yola ta cikin birnin Kano Shine kuma babban da namiji ga Madaki Shehu, domin kuwa dukkan `ya`yunsu biyumata ne. A bisa ga al`ada irin ta addinin musulunci a kasar Hausa, Alhaji Nura, ya fara karatunsa na allo a makarantar Malam Audu, da ta Markaz ta kasar Misira a Kano, kana ya fara neman ilminsa na boko daga makarantar Firamare ta Shahuci da ke cikin birnin Kano a shekarar 1964, karatun da ya kammala a makarantar Firamare ta kwana ta danbatta a shekarar 1969. Ya samu shiga Kwalejin gwamnatin tsohuwar Jihar Kano da da a yau ake kira da sunan Kwalejin Romfa tsakaninshekarar 1970 zuwa 1974.
Bayan kammala Kwalejin Rumfa ya tafi karo ilmi a Landan a can kasar Birtaniya tsakanin shekarar 1974 zuwa 1977, a nan cikin gida ya samu yin karatu a Kwalejin Kimiya da Fasaha ta Kaduna, wato Kadu Polytechnic tsakanin shekarar 1979 zuwa 1981. Ya sake komawa birnin Landan a Makarantan Akantoci ta birnin Landan, sannan kuma a shekarar 1995, ya shiga Jami`ar Bayero da ke birnin Kano inda ya samu shaidar babbar Difloma akan fannin shari`a.
Idan ka koma akan batun yin aiki danmadamin na Kano ya fara aiki da Hukumar kula da asibitocin Jihar Kano a shekarar 1977, inda aka tura shi asibitin Nassarawa a matsayin mataimakin jami`in gudanarwa. A tsawon shekaru bakwai da ya kwashe yana aikin gwamnatin jihar 1977 zuwa 1984, ya zauna wurare irin su Ofishin gwamna da Ma`aikatar Yada Labarai har zuwa lokacin da Allah Ya karbi ran mahaifinsa Alhaji Shehu Ahmed Madakin Kano, kuma babban Kansila a masautar Kano a shekarar 1984, wanda shi kuma Alhaji Nura Shehu Ahmed akai masa Hakimain bagwai kuma dan Madamin Kano a ranar 4 ga Satumban 1984, mukamin da yake kai har zuwa wannan lokaci, ba karin girman sarauta bare kuma canjin kasa yana dai bagwai dinsa, tare da Talakawansa dare da rana in ka gan shi birnin Kano gaida Maimartaba ko wani sha`ani na mulki ko al`ada irin su hawan sallah ko daurin aure ya shigo da shi amma dai ba don wani abu na dabn ba.
Tarihin dan Madami rayuwar ya tabbatar da cewa tun yana matashinsa dan shekaru 27, kuma yana da shekaru 25, da yin auren fari, Allah ya ba shi nauyin mulkin tafiyar da jama`a, al`amarin da ya sanya a wancan lokacin shi ne mafi kankantar shekaru a cikin Hakiman Masarautar Kano masu kasa kaf, kuma tun daga wancan lokacin zuwa yau babu wani labari da aka taba samu akan ya yi wa talakawansa wani abu na ba daidai ba, bare har su kawo shi kara ga gwamnan jiha ko ga Masarautar Kano, hatta harka irin ta kuruciya da ya ratso cikinta yana da rawanin Sarki, ba ta sa shi aikata wata badala irin ta masu mulki ba, ko kama karya ko kwace gonaki ko filaye, bare sayar da burtaloli ko samun sa da hannu cikin ruruta rikicin Fulani Makiyaya da Manoma da makamantan ayyukan ashsha, babu tarihin faruwar haka tsakaninsa da su kansa, bare a ceanji kansu.
danmadamin na Kano, ya fadi cewa da tainakon Allah da tarbiyyar addinin islama da ta magabata da ya samu tun farko, da tuntuba wajen neman shawara akan kusan dukkan abin da ka shige masa duhu daga jama`ar da ya taras a bagwai walau Fadawa ko mutanen gari da sauran magabata, su suka taimaka masa a yau yake zaune da kowa lafiya, ba cuta ba cutarwa tsakaninsa da mutanensa. Hakan kuma yake fatan garin dorewa wato jagoranci a aikace, ba abin da za a fadi daban ba abin dakuma za a aikata daban.
A cikin jibantar rayuwar Talakawansa wajen ganin ana kara samun zaman lafiya kwanciyar hankali da karuwar arziki a gundumar ta bagwai da jihar Kano da kasa baki daya, danmadamin na Kano ya yi nasarar duba matsalolin zaman takewar al`umma irin ta auratayya da samar da ilmi na addini da na zamani a karkashin shirye-shiryen gwamnatoci irin na Adaidaita Sahu da na Zakkah da Hisbah, Kwamitocin da duk suke karkashinsa.
Ya sa idanu sosai wajen zakulo `yan asalin karamar Hukumar ta bagwai na ciki da wajenta da suke ba da gudummawa don ci gabanta da mutanenta gwargwadon iko, wajen karramasu ta fannoni daban-daban, don karfafa masu gwiwa da kuma neman ’yan baya su rika koyi da su.
Ya zuwa yanzu akwai kimanin tsayayyun kananan Kwamitoci biyar baya ga babba na karamar Hukuma da yake shugabanta. Biyar din, sun hada da na samun kyakykyawar zamantakewa a dukkan Unguwannin karamar Hukumar 145, da na kasuwanni da tashoshin mota da na Assibitocin Mazabu da wanda ke sa idanu akan abubuwan da ke gudana a Makarantun Firamare da Sakandare a gundumarsa. Sannan sai Kwamitin Fadama, saboda kasancewar ana noman rani a yankunan Dagatai takwas na karamar Hukumar.
Ta wadannan Kwamitoci ana samun saukin aikata ayyukan masha`irin na sha da fataucin miyagun kwayoyi da fyade da rikicin Fulani makiyaya da Manoma da makamantansu.
Wannan fili na taya Mai girma danmadamin Kano, kuma Hakimin bagwai Alhaji Nura Shehu Ahmed, murnar ciki shekaru 30, akan karagar mulkin Gundumar bagwai da addu`ar Allah ja zamani da daukaka a gama lafiya. Sannan da rokon Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na II, da Masarautar Kano da Gwamnan Kano, su duba yiwuwar kara wa danmadami girma daga kan wannan mukami da yake kai yau shekaru 30, koda kuwa ba za a yi masa canjin kasa ba. Da fatan a yi biki lafiya.