danmajen Daura ya soki masu yi wa Buhari yarfen siyasa

An bayyana dan takarar shugabancin Najeriya a karkashi jam’iyyar APC Janar Buhari mai ritaya da cewar ba mutun ba ne dake nuna kabilanci a tsakanin al’umma. danmajen Daura, Alhaji Kabir Salisu Daura ne ya bayyana wa manema labarai, a wani taron gamayyar kungiyoyin da suka fito daga masarautar Daura da suka kunshi kananan hukumomi biyar […]

danmajen Daura ya soki masu yi wa Buhari yarfen siyasa
danmajen Daura ya soki masu yi wa Buhari yarfen siyasa

An bayyana dan takarar shugabancin Najeriya a karkashi jam’iyyar APC Janar Buhari mai ritaya da cewar ba mutun ba ne dake nuna kabilanci a tsakanin al’umma. danmajen Daura, Alhaji Kabir Salisu Daura ne ya bayyana wa manema labarai, a wani taron gamayyar kungiyoyin da suka fito daga masarautar Daura da suka kunshi kananan hukumomi biyar da ke masarautar.
danmajen wanda kuma shi ne shugaban gamayyar kungiyoyin da tun farko su ne suka fara yin wani gangami don kiran Buhari da ya fito, ya sake tsayawa takarar da yanzu ya yi nasara akanta, ya ce,”shaci fadi ne kurum kuma tare da yarfen siyasa suka sa ake nuna Buhari akan cewa mutum ne wanda ke kokarin nuna kabilanci, muddin ya hau shugabancin kasar nan. Amma yana da kyau jama’ar Najeriya su tuna da irin yadda shugabancinsa a lokacin mulkin soja. Kowa ya sanshi mutum ne wanda ya dauki ‘yan Najeriya duk daya, babu ruwansa da bambancin yare, ko addini.
“Ba sai na yi dogon bayani ba, don haka muke mamaki a duk lokacin da muka ji ance,wai yana nuna bambanci. To kuma yanzu ba mu san abin da za a ce ba kasancewar wanda ya dauko domin ya yi masa mataimaki, inda kuwa yana da nuna bambancin da hakan ba ta faru ba”,inji Danmajen Daura.