Danne-dannen waya don samun kuɗi: Yadda matasa da tsofaffi suka rungume shi hannu bibiyu

A wani bidiyon TikTok, Mista Gentle Boi ya bayyana yadda ya samu Dala ɗari 260 (kimanin Naira dubu 416) daga Notcoin.

Danne-dannen waya don samun kuɗi: Yadda matasa da tsofaffi suka rungume shi hannu bibiyu

Malam Ibrahim Ɗanlami, mataimakin babban manaja a wani kamfani mai zaman kansa da ke Abuja, ya ɗauki mahaifiyarsa daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe, wadda ta zo garin don ta zauna tare da jikoki.

Yayin da yake tuƙa kakar zuwa gida ne ya lura tana ta faman danna madannan wayarta.

“Ina tunanin tana buga wasan ‘candy crush’ ne wanda ni kaina nake nake yi idan na samu dama. Amma bayan wasu kwanaki, sai na lura cewa, danne-dannen bai tsaya ba. Dole na ce mata, ‘Mama, kin manyanta sosai, kin ɗauki wasan waya kamar yarinya,’ Amma ta amsa da cewa, ‘Jira sai na samu miliyan ɗina,” in ji shi.

Wannan ya ruwan dare a sassa daban­daban na ƙasar nan, inda mutane da dama suka kama da danne-dannen wayoyinsu da fatan samun kuɗi daga gare.

Ɓullowar wannan sabuwar hanyar samun kuɗin ta ratsa tsakanin dukkanin rukunin shekaru. Ko a gida ko kasuwa ko ma a cikin bayan gida akan kama harkar danna waya da fatan samun miliyoyin da ake tsammanin za su zama kuɗin gaske a gaba kaɗan.

Yadda aka fara

Za a iya bin asalin wannan harkar ne daga nasarar wata manhajar haƙar ma’adanai ta intanet (crypto mining) mai suna Notcoin. An ƙaddamar da Notcoin a watan Janairu 2024, inda ta ba da damar tsarin dannawa da ake yi, ana samun alamun NOT. Wannan manhaja ta shahara sosai, inda sama da mutane miliyan 35 suka shiga cikin a ’yan watanni kaɗan.

A nan ne mutane da dama a Nijeriya suka fara ɗaukar Notcoin ba kawai a matsayin wasa ba, har ma a matsayin hanyar samun kuɗi ta gaske.

Rahotanni sun nuna cewa, masu amfani da manhajar da suka himmatu wurin “haƙar” alamun NOT sun samu kuɗi mai yawa, har wasu sun samu fiye da Dala dubu ɗaya ($1,000).

Mutane da dama a Nijeriya, ciki har da wani mai suna Mista Gentle Boi, sun ba da labarin nasararsu da Notcoin.

A wani bidiyon TikTok, Mista Gentle Boi ya bayyana yadda ya samu Dala ɗari 260 (kimanin Naira dubu 416) daga Notcoin.

Wannan labarin nasarar ya ƙara ba shi sha’awar wata manhaja mai suna TapSwap, wadda ya ce ta ba shi fiye da kwabbai miliyan 15 na kuɗin manhajar, kuma ba ta nuna alamar tsayawa ba.

Labarin nasarar ya ƙara fitowa ta hannun wani matashi wanda ya nuna wata na’urar sanyi (Air conditioner) da ya siya daga ribar Notcoin tare da ƙarfafa mutane su shiga haƙar TapSwap.

Yaya TAPS ke biya?

Jaridar Aminiya ta gano cewa, tsari ne da ake yi na tara kuɗin manhajar ta hanyar buga wasa da kuma samun kuɗin TAPS ta hanyar dannawa da kammala ayyukan da aka ba ka.

“Da zarar ka tara isassun kuɗi, za ka iya mayar da su zuwa alamun TAPS a cikin tsarin TON blockchain bayan ƙaddamar da alamun TAPS,” inji shi.

‘Yadda haƙar kuɗin Kirifto ya canza rayuwarmu’

A Jihar Kano, matasa da yawa sun rungumi kasuwancin kuɗin Kirifto ko don samun abin yi ko don ƙarin hanyoyin samun kuɗi.

Malam Abdulsalam Ɗahiru, mai shekara 26, wanda yake haɗa kasuwancin POS da haƙar kuɗi, ya shaida wa wakilinmu cewa, haƙar kuɗi ya canza rayuwar mutane da dama kuma yana ganin kansa a matsayin mai kuɗi a nan gaba.

“Na san wanda ya samu fiye da Naira miliyan 50 daga kasuwancin kuɗin Kirifto. Daga DOGS kaɗai. Wani abokina ya samu Naira miliyan 3,’’in ji shi.

Da aka tambaye shi ko nawa ya samu, Malam Abdulsalam Ɗahiru ya ce, ba zai faɗi adadin ba saboda tsaro.

Malam Idris Sarina, wani dillalin gida da ke zaune a Titin Court Road mai shekaru 60, yana zaune a ofishinsa, yana haƙar kuɗin Kirifto da wayarsa. Yana cewa, da kuɗin Kirifto ne yake biyan buƙatunsa, duk da cewa bai bar kasuwancin gidaje ba.

“Na koyi haƙar kuɗin Kirifto daga matasa kuma na gane cewa gaskiya ce kuma yana ba da damar samun kuɗi cikin sauƙi. Saboda haka na rungumi wannan da hannu biyu,’’ in ji shi.

Wani mai haƙar kuɗin Kirifto, Malam Abubakar Ɗanzaria ya ce, duk da cewa bai samu kuɗi mai yawa daga haƙar kuɗi kwanan nan ba, yana fatan cewa zai samu riba mai yawa a nan gaba.

“Na samu Naira dubu 12 daga DOGS, Naira dubu 16 daga CAT har ma daga HAMSTER, na samu Naira dubu 4,”in ji Ɗanzaria kamar yadda shaida wa Aminiya.

Ya ce, matasa da dama sun rungumi kasuwancin kuɗi saboda rashin aikin yi, yana mai jaddada cewa ko da gwamnati ta samar da ayyukan yi, matasa da dama za su ci gaba da shiga wannan kasuwancin Kirifto don ƙarin samun kuɗi.

Wata matashiyar mai haƙar kuɗi, Malama Halipa Salihu ta ce, kuɗin Kirifto ya taimaki mutane da dama, daga masu ƙarancin jari har zuwa marasa aikin yi.

Ta ce, haƙar kuɗin na Kirifto ba kawai ya sauya rayuwar mutane ne ba ta hanyar samar da damarmaki na tattalin arziƙi, yana ma samar da nishaɗi ga masu yi, duba da cewa yana buƙatar warware matsaloli masu sarƙaƙiya, tare da haɗin gwiwa da wasu mutane.

Malama Halipa Salihu ta ce, kasuwancin kuɗin na Kirifto yana kuma haɓaka ilimi tsakanin mutane, saboda yana buƙatar fasahar kwamfuta mai sauƙi da jagoranci daga waɗanda suka saba da yadda tsarin yake aiki.

Ta ce, “a cikin shekara guda da ta gabata, na samu kusan Naira miliyan 2 daga kasuwancin kuɗin Kirifto. Ya yi tasiri sosai a rayuwata. Ni ma na amfana daga kasuwancin kuɗin na Kirifto,”in ji ta.

Shi kuwa Mista Steɓen Nwafor, wani akawu a wani kamfani mai zaman kansa a Kano, shi ma yana cikin haƙar kuɗin Kirifto sosai.

Mista Nwafor ya ƙirƙiri wani zaure a wasof mai suna Digital World Opportunity da ke da mambobi 64, inda suke raba bayanan da suka shafi wannan kasuwancin don amfanin mambobin.

Ya ce, duk manufar ita ce sanar da al’ummar da ke bincikar damarmakin da wannan sabuwar fasaha ke bayarwa, yana mai cewa kusan mutane miliyan 40 sun shiga DOGS, lamarin da ya sa ya samu karɓuwa sosai a tsakanin masu haƙar kuɗin na Kirifto.

Kodayake wasu malamai na addinin Musulunci suna da ra’ayoyi masu karo da juna a kan halacci ko haramcin kuɗin Kirifto, kasuwancin kuɗin na ci gaba da samun karɓuwa a tsakanin mutane, musamman matasa.

Yadda manhajojin daddannawa suka karya mana gwiwa – Mai haƙar Hamster Kombat

A cikin wata mota ƙirar “bush” a Iyana Oba, Legas, wakilinmu ya lura da wani mutum mai matsakaitun shekaru da ya mai da hankali kan wayarsa da hannu biyu, yana daddannawa a kan Hamster Kombat, manhajar Kirifto da ta shahara a tsakanin ’yan Nijeriya da dama.

Yayin da yake amfani da ƙarfinsa, ya mai da hankali ba tare da wani abu ya shagaltar da shi ba, kuma kiran fasinjoji da hayaniya ba su sami damar karkatar da hankalinsa daga wannan aiki na neman kuɗi ba.

Ba shi kaɗai ke yin haka ba, an lura cewa a cikin motocin haya da ke tafiya a cikin Legas, mutane da dama na yin wannan aiki na danne-dannen waya, musamman yayin da suka maƙale cikin cinkoson ababen hawa a birnin.

“Ina sha’awar samun kuɗi ta hanyar wani abu da ya zama kamar wasa,” inji wata mai yi wa ƙasa hidima da ke aiki a Abeokuta, inda ta nemi a sakaya sunanta, yayin da take magana da wakilinmu.

Ta kasance tana haƙar tsabar kuɗi kusan wata biyar ke nan. Wasu daga cikin manhajojin da ta yi amfani da su sun haɗa da Hamster da Memefi da Blum da kuma DOGS.

Wannan budurwa ’yar shekara 25, wacce ta kammala karatun lissafi, ta shaida wa wakilinmu cewa, tsarin ba da la’ada yana bambanta ne dangane da manhajar, amma “ba kuɗin da zai canza rayuwa ba ne, wanda hakan bai gamsar da ni ba idan aka yi la’akari da lokaci da ƙwarin gwiwa da kuɗin da aka zuba a ciki.”

Ta ce, “yanzu na tara Dala 38 kuma ina ganin hakan a matsayin asara”.

Da aka tambaye ta ko ta taɓa rasa kuɗi kai-tsaye a cikin manhajojin kirifto, sai ta ce, “ban rasa kuɗi kai-tsaye ba, amma na na ɓata lokaci a cikin wata manhaja wacce ba ta yi nasara kamar yadda nake zato ba, wanda hakan ya sa na ji kamar asara ce,” in ji ta.

Mai yiwa ƙasa hidimar ta ce ta fi damuwa da tsarin ba da lada na Hamster Kombat.

“Hamster Kombat ya zama abu mai gauraya a gare ni. Wasa ne mai nishaɗi, amma na gano cewa damar samun kuɗi ta yi ƙasa da yadda na yi tunani. A ƙarshe dai ban samu gamsuwa ba,” in ji ta.

Wani masani ya bayyana cewa, Hamster ya ba wa mutane kunya saboda mutane sun danƙara masa zato.

Malam Abdullahi Abubakar ya ce, an gabatar masa da manhajojin ne ta hanyar abokai, duk da cewa ba shi da cikakken yarda da tsarin.

Ahmad Datti (Kano), Peter Moses (Lagos), da Hassan Ibrahim (Bauchi) Fassara: Ahmed Ali, Kafanchan

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC