Dansarauniya ya nemi afuwar Ganduje kan bata masa suna a Facebook
Babu tabbas ko da son ran Dansarauniya ya ba Ganduje hakuri ko kuma kotu ce ta umarce shi
Tsohon Kwamishina Ayyuka da Tsare-tsare na Jihar Kano, Muazu Magaji, ya nemi afuwar Gwamna Abdullahi Ganduje kan wani sako da ya wallafa a Facebook wanda ake zargin shi da bata sunan gwamnan.
Idan ba a manta ba, a watan Janairu, kotu tsare Muazu Magaji, wanda yanzu dan jam’iyyar PDP ne, a gidan yari saboda ya wallafa wani sakon a Facebook.
- Alarammomin Kano sun gudanar da addu’o’i na musamman don samun tsaro da shugaba na gari
- An ga dan Saurauniyar Ingila yana tallan mujalla a kan titi
An gurfanar da Muaz Dansarauniya, wanda Ganduje ne a gaban Kotun Majistare ta 58 bisa zargin cin mutunci da gangan, munanan karya da kuma tada hankali ga Ganduje.
Laifukan sun saba Sashe na 392 da 399 da na 114 na Hukumar Shari’a ta Jihar Kano ta shekarar 1999.
Sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, Muaz Dansarauniya ya nemi afuwar Ganduje, yana mai cewa shi ba da nufin cin mutuncin gwamnan ko makusantansa ya yi ba.
Kawo yanzu babu tabbacin ko kotu ce ta umarci Dansarauniya dan jam’iyyar adawa ta PDP ya ba Ganduje hakuri, ko kuma ya yi hakan ne da son rai.
Ga sakon na Muaz Dansarauniya, dan siyasa mai yawan tayar da kura a Facebook:
“Biyo bayan bata maka da na yi a shafina na Facebook na ga dacewar na sake zuwa na baka hakuri da iyalanka a irin wajen da na bata maka.
“Ina so na rubuta wannan sako na ban hakuri ga Mai Girma Gwamna da kuma iyalansa bisa ga abin da na wallafa a farkon watan Janairu, 2022 wanda zai iya jawo bacin ran da ba shi na yi nufi ba ga mai girma gwamna, iyalansa da kuma duk wata fassara da ban yi nufi ba da za ta iya bayuwa ga kimar Mai Girma Gwamna ko kuma shugabancinsa.
“Ba tare da ba da wani uzuri ba wannan hoto ba ni na fara wallafa shi ba, [amma] cikin dakiku kadan daga wallafa jawabaina a kan hoton aka jawo hankalina kan cewa jawabin nawa da na wallafa za a iya yi masa mummunar fahimtar cewa na yi ne domin taba mutunci da kimar Mai Girma Gwamna.
“Cikin gaggawa na cire daga shafina domin ni ban wallafa ta kowacce hanya da nufin yada batanci ko ja wa Mai Girma Gwamna zubewar daraja a jagorancinsa ba.
“Ina mai bada hakuri ga zafi ko daci da abin da na wallafa ka iya jawowa ga Mai Girma Gwamna da iyalansa.
“Gaskiya ita ce, ni mai godiya ne ga Mai Girma Gwamna bisa ga soyayya da amana da ya nuna gare ni, hade da damar da ya ba ni na yi aiki a gwamnatinsa.
“Ina mai fatan alkhairi ga mai girma gwamna da kuma iyalansa.
“Allah ya kara daukaka,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis.