Dantata: Yadda na san Sarkin Bichi Nasir Ado Bayero

Tasowar Sarkin Bichi daga bakin aminin mahaifinsa.

Dantata: Yadda na san Sarkin Bichi Nasir Ado Bayero

Alhaji Aminu Alhassan Dantata

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dantata, Alhaji Aminu Dantata, makusantan marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ne. A wannan hirar, attajirin ya bayyana wasu abubuwa game da tasowan Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, daya daga cikin ’ya’yan marigayin abokinsa.

Ku biyo mu ku sha labari game da sarkin wanda ake bikin mika wa sandar mulki a ranar Asabar, 21 ga Agusta, 2021:

Dangantakar da ke tsakaninku da marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero sananne ne ga mutanen Kano. Za mu su ka bayyana mana yadda dangantakar ta kasance?

Dangantakata da marigayi Sarkin Kano, Allah Ya yi masa rahama, tun daga yarinta ce.

Kuma tun kafin a haife mu duka, akwai dangantakar da ke tsakanin danginmu koyaushe.

Don haka, mun taso muna ganin irin alakar da ke tsakanin iyayenmu. Saboda haka dangantaka ce mai kyau tsakaninmu tun daga kuruciya.

Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, shine da na farko ga marigayi sarkin. A matsayinka na babban abokin mahaifinsa, me za ka iya tunawa game da lokacin haihuwarsa?

Haihuwar da abin farin ciki da biki da murna ne. Na tuna cewa marigayi sarki ya yi farin ciki sosai; haka ma danginsa da masu yi masa fatan alheri. Farin cikin ya kasance wanda ba zai misaltu ba.

Ka yi tunanin a ce dan fari da aka haifa wa sabon sarki da aka nada ya kasance na miji. Babban bin farin ciki ne ga kowa da kowa kuma mutane sun yi farin ciki sosai.

Kana daga cikin mutane kalilan da Sarkin Bichi ke dauka a matsayin ubanninsa. Don haka, yana da mahimmanci a ji wani abu daga gare ku game da shi. Yaya za ka bayyana halayensa tun yana karami?

Haka ne, ya kasance mai biyayya da aminci ga mahaifinsa tun yana yaro.

Hakanan, a al’adance, a cikin dangin sarauta, kowane yaro yayin da yake girma yana da baiwarsa da Allah Madaukakin Sarki Ya ba shi. Ta haka ne zai yi girma ya zama abin da aka kaddara masa ya zama.

Hakanan Zai ba shi wadanda za su kasance abokansa na kusa tun daga dangi har ma da mutanen waje. Na san shi, yana da abokai da yawa.

Hakanan, yana da kima sosai kuma yana da juriya. Lokacin yana karami, nakan gan shi koyaushe tare da mahaifinsa.

Mahaifinsa yana aiko wurina a duk lokacin da aka samu wata matsala, duk da cewa yana matashi a lokacin. Da haka na fahimci cewa yana da hankali sosai kuma yana da kirkira.

Yana son mutane kuma mutane na son shi. Wannan hali ne ko siffa da Allah Ya albarkace shi da ita.

Lallai ni’ima ce daga Allah kuma har yanzu ina iya ganin wannan ni’imar sosai a tare da shi.

Yanzu, da yardar Allah, ya kara samun daukaka a rayuwa; yana da iyali kuma yanzu ya aurar da ’ya’yansa. Har ma muna da alakar aure da su. Iyalanmu sun yi auri juna.

Marigayi Sarki Ado ya nada Alhaji Nasir Ado Bayero a matsayin Tafidan Kano, daga baya ya zama Hakimin Nassarawa, da Tarauni da Nassarawa a karo na biyu. A matsayinka na uba, me za ka ce su ne manyan gudummawar da Alhaji Nasir Ado Bayero ya bayar ga zaman lafiya da ci gaban al’umma a wadannan lokutan?

To, wajen samar da kyakkyawan jagoranci, ya yi abubuwa da yawa. Wannan ne ma dalilin da ya sa mahaifinsa ya ci gaba da motsa shi daga wannan masarautar zuwa waccan.

Da a ce bai gamsu da salon shugabancinsa ba da hakan ba zai faru ba. Ya yi kokari wajen sauke nauyin da aka dora masa.

Mahaifinsa ya yi gamsu da abin da ya yi shi ya sa ya ci gaba da kai shi zuwa masarautu daban-daban don ingantawa da adana masarautun.

A yau, da yardar Allah, shi ne Sarkin Bichi. Mutane na farin ciki kuma mu ma muna farin cikin ganin sa a matsayin sarki. Don haka ne muke rokon Allah Ya taimake shi.

Yallabai, a matsayin uba, me kuke tsammani daga gare shi a matsayin Sarkin Bichi?

Muna sa ran irin kyawawan halayen da yake nunawa a koyaushe don tabbatar da cigaba da wadata a masarautar.

Abun da muke addu’a ke nan, domin a matsayin uba kuma babban aminin mahaifinsa marigayi, abin da ya fi dacewa shi ne yi masa addu’a da ’yan uwansa da kuma yi musu fatan alheri.

Don haka koyaushe muna addu’ar Allah Ya ci gaba da kare su da inganta su.

Da fatan Allah Ya albarkace su kuma Ya inganta su ba kawai a Najeriya ko Afirka ba amma a duk duniya kamar yadda Ya yi wa mahaifinsu.

Mahaifinsu ya yi abubuwa da yawa don zaman lafiya da ci gaban al’umma. Don haka, ’ya’yansa ne za su kiyaye mutuncinsa kamar yadda su ma suke kiyayewa da kiyaye mutuncin kansu insha Allah.

Da fatan Allah Ya ganar da su, mu ma Allah Ya ganar da mu. Ina kuma rokon Allah da Ya sa Aljannah Firdausi ta zama makomar wadanda suka rasu.