danwanzam: Ta’aziyya da tariyar rayuwar dan wasan barkwanci
Shahararren dan wasan Hausa, daya daga cikin wadanda da suka yi fice a wasan kwaikwayon barkwanci a Arewacin Najeriya, wanda kafin rasuwarsa yake zaune a Sakkwato; Alhaji Abudurrahaman Muhammad danmalam, wanda aka fi sani da danwanzam ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata.An yi jana’izar fitaccen dan wasan a ranar Asabar da ta gabata […]
Shahararren dan wasan Hausa, daya daga cikin wadanda da suka yi fice a wasan kwaikwayon barkwanci a Arewacin Najeriya, wanda kafin rasuwarsa yake zaune a Sakkwato; Alhaji Abudurrahaman Muhammad danmalam, wanda aka fi sani da danwanzam ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata.
An yi jana’izar fitaccen dan wasan a ranar Asabar da ta gabata da safe kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada. An binne shi a makabartar Unguwar Nakasari a cikin garin Sakkwato. Ya rasu yana da shekara 101 a duniya kuma ya bar matar aure daya da ’ya’ya bakwai da jikoki 20. Kafin rasuwarsa, Aminiya ita ce kafar watsa labarai ta karshe da ta zanta da shi kan rayuwarsa, inda a lokacin ya musanta jita-jitar da wasu suka yi ta yadawa, cewa ya kwanta dama.
“Lallai na yi jinya sosai a kwanakin da suka gabata amma yanzu Allah Ya kawo min sauki, garau nake jin kaina. Ina sanar da al’umma cewar ina raye, ban mutu ba kamar yadda ake fada a gari. Ciwo ba mutawa ba ne.” Abin da marigayi danwanzam ya fada wa wakilinmu ke nan da bakinsa a wancan lokaci.
Da ya juya kan rayuwarsa, sai marigayin ya gode wa Allah da halin da yake ciki na rayuwar godiya, duk da ba wani abin kirki a hannunsa. Ya koka musamman da Hukumar Kula da Al’adu ta Jihar Sakkwato, cewa sun watsar da shi kwata-kwata, inda ba su ma san yadda rayuwarsa da ta iyalinsa suke ba, duk da gudunmawar da ya ba jihar wajen bunkasa al’adu da tattalin arziki, yau shi ne a walakance, ba wani tallafi ko tunawa da gwamnati ke yi masa. “Ni ba na zuwa kofar gidan kowa don neman wani abin sanyawa bakina, mu ne, ku ne, kun sani, na sani; Allah Yana nan kuma na tabbata bai manta da ni ba,” inji shi cikin rawar murya.
Ya kara da cewa: “Kana son ka san shekaruna a wannan duniya? Zan yi maka Daushe waton Dausantaka. Matata na aure ta ne tun tana budurwa, a lokacin na fi shekara 40. Yanzu kuma ina tare da ita sama da shekara 40. kila zan yi kai 90 ke nan ko? Ina godiya da ’yan wasan kwaikwayo, musamman wadanda ke kawo mini ziyarar ban girma; saboda sun kasa mantawa da mafari. Abokan wasana da suka yi saura a raye, muna tare da su cikin zumunci da godiyar Allah.”
Bayan rasuwarsa, wakilinmu ya sake garzayawa gidansa, inda ya zanta da iyalansa da kuma abokan sana’arsa.
Malam Abubakar danjuma, dansa ne wanda ya wakilci sauran don zantawa da Aminiya. “An haife ni a Sakkwato a 1971. A yanzu ina aiki da Ma’aikatar Jin Dadi da Walwala ta Jiha. Dangatakata da margayi, shi ne mahaifina. Ina daga cikin ’ya’ya takwas da ya haifa, ni ne na biyu. A halin yanzu mu bakwai ne, domin wanda ke bayana ya rasu kafin rasa mahaifin namu.” inji shi.
Ya bayyana mahaifinsa da cewa: “A sanin da na yi wa rayuwarsa, zan iya cewa na dace da mahaifi kwarai da gaske. Mutum ne abin koyi ga jama’a, don a gaskiya na samu tarbiyya tagari wajensa, wadda cikin ikon Allah hudubar da yake mini koyaushe, yana nuna mini cewa in ji tsoron Allah a lamurrana, in daraja na gaba da ni, in kasance mai hakuri ga duk abin da aka yi min in janyo jama’a kusa da ni da kyauta da kyautatawa. A kullum kalmomin da yake yi min ke nan kuma cikin ikon Allah na fi kusanci da shi fiye da sauran ’ya’yansa, duk matsalar da yake ciki yakan gaya mini. In wanda zan warware ne in aiwatar, in kuwa sai na samo wata gudunmawa, a hakan zan yi sai na warware cikin ikon Allah.”
Ko ka san dalilin da ya sanya mahaifinku ya jingine wasan kwaikwayo kafin rasuwarsa? “Ai dalilin da ya sanya ya daina wasan kwaikwayo, yanayin jihar ne yadda ya koma tsawon lokacin da yake da rayuwarsa da hankalinsa da lafiyarsa ba don gwamnatin jiha ta fita batun abin ba, da zai dauki tsawon lokaci yana yi amma sai ya jingine wasan a 1987. Sai dai a kan kira shi jefi-jefi a gidan rediyon jiha, Rima Rediyo suna yin shirin Zauren Mai Unguwa. Hakan ya ci gaba, shi ma daga baya ya daina.
“Abin takaici, kuma duk tsawon lokacin da mahaifinmu ya dauka zaune a gida, bayan ya daina wasa; ba wata gudunmawa da gwamnati ko wata kungiya ta taba aiko masa. Wannan abin ya bata mana rai kwarai da gaske. Irin yadda mahaifina ya bauta wa kasar nan, ba wai Jihar Sakkwato kadai ba, dubi irin yadda yake; ba don Allah Ya albarkace shi da daukaka mu ba na samun tarbiyya da madogara, da ba mu san iya halin da zai shiga ba. A hakikanin gaskiya, duk lokacin da na tuna da abubuwan, sukan bata mini rai kwarai da gaske. Ko mun yi yunkurin korafi ba zai yarda ba, don koyaushe yakan kawo Allah a lamurransa da yawa; ’ya’yansa ke ba shi shawara na kusantar gwamnati don ya samu taimako. Ya ce shi ba zai je ba, Allah Ya san halin da yake ciki kuma Shi zai taimaka masa. Ni ban san gida ko ofishin wani da mahaifina ke zuwa don biyan wata bukata ba. Zan rika tuna mahaifina da saukin hali da daukar kowa abokin wasansa, ba ruwansa da zamanka karami ko babba ko mai iko, gwargwado zai ba ka girmanka. In Allah Ya sanya ka kasa gare, shi zai daraja ka ya kuma girmama ka. Na koyi haka a wurinsa, abinsa kuma na mutane ne ba nasa shi kadai ba. Wannan halin nasa ya sanya har Allah Ya yi masa cikawa bai mallaki gidansa na kansa ba. Gidan da yake ciki kafin rasuwarsa na matarsa ce saboda taimaka wa jama’a da yake yi.”
Hajiya Safiya, ita ce matar da marigayin ya bari. Ta nuna bacin ranta kan wannan rashin da ta yi kuma ta ce ba za ta taba mantawa da mijinta ba, don fiye da shekara 40 suna tare amma bai taba bata mata ba. Ta ce tana alfaharin zama da shi da fatar Allah Ya gafarta masa kura-kurensa.
A dukkan sa’o’in wasan kwaikwayonsa, mutum biyu ne kawai suka rage, waton ’Yar Mai Albasa da Boka Mai Kunkeli.
Wakilinmu ya samu zantawa da ’Yar Mai Albasa amma ta ki amincewa ta yi magana kan rayuwar marigayin, domin a cewarta, tana ganin ba ita ce mafi dacewa ta yi magana kansa ba. “Ni sanina da shi kan harkar dirama ce kawai. Ni kuwa gani a nan, wanda kake iya fadin halinsa, shi ne wanda zaman aure ya hada ka da shi, shi kake iya fada amma wanda sha’anin aiki ya hada ka da shi; da an kammala ku waste, ba za ku sake haduwa ba kuma kwana ko wata nawa za a yi sai aikin ya sake fadowa. Duk tambayar da za ka yi min, an yi ta a gidansa kuma sun ba da amsa; don su suka fi cancanta. Ni daga baya na shiga dirama a wurinsu, ta hannun hakimi a lokacin da rediyo ake yi ba a fara ta talabijin ba; sai daga baya ne kuma ci aka gaba da yin ta talabijin. Ko mene ne kake so kan rayuwarsa, ka samu dansa Abubakar.” Kamar yadda ta bayyana.
Duk yunkurin da Aminiya ta yi don ta samu yin magana da dan wasa Boka Mai Kunkeli, abin ya ci tura; sai da ta samu zantawa da wani karamin dan wasa a lokacinsu amma yanzu yana cikin uwayen masu gudanar da wasan kwaikwayo a Jihar Sakkwato, wato Alhaji Ahmad danjummai, inda ya tofa albarkacin bakinsa kan rayuwar marigayi danwanzam da ya sani.
“Kamarr yadda ka sani dai sunana Ahmad S. danjummai, an fi sanina da Baba danjummai. Ni ne shugaban MOPAN a Sakkwato, mataimakin shugaba na uku a kasa. Gaskiya mun yi rashi babba, ina tuna ranar Jumu’a ne muna gidan wasa aka kira daya daga cikin ’ya’yansa Ibrahim da muke harkar wasa da shi, aka gaya masa rasuwar. Haka ya sanar da ni a farko, lamarin da ya kada mu. Daga baya na tara jama’a muka tafi gaisuwar ubanmu a wannan harkar, ga shi kuma muna tare da ’ya’yansa biyu a cikin wannan harkar; dayan ne ke tare da mu, dayan Lala, yana Kano. Marigayi malaminmu ne, ya koyar da mu abubuwa da dama a tare da shi, musamman ni da na san shi tsohon sani. A lokacin yana wasa, karami ne ni a cikinsu sosai, yana da saukin kai da hali nagari, kowa ya san da haka. Akwai wata karramawa da aka yi masa a Zariya, kan gudunmawarsa ga ci gaban ilimi da gargajiya. Ni na je na karbo masa kyautar.”
Ya kara da cewa: “Mun shirya farfado da sha’anin wasa a nan, har muka sanya marigayin a matsayin ciyaman, ’Yar Mai Albasa kuma shugabar mata, duk da ta yi aure, mijinta ya amince. Boka a matsayin Sakatare, kungiyar, wacce muka sanya wa sunan wasansa, waton “Idon Matambayi.” Za ta fara ne sai ya kamu da rashin lafiya, haka dai yau ciwo gobe lafiya, muna jira ya warke a fara aiki; ashe ciwon na tafiya ne. Mun yi rashin uba a kasar nan baki daya.
“Idan muka yi la’akari da gundunmawar da ya bayar, ya kamata Gwamnatin Jihar Sakkwato ta duba yiyuwar karrama shi. Ko bayan ransa kuma su sanya wa wani ginin gwamnati sunansa da za a rika tunawa da shi, kamar yadda aka yi wa Ahmad Maigero kuma a tallafa wa iyalansa don suna cikin halin nema. Da fatar Allah Ya gafarta masa, Ya kyautata bayansa.