Darajar kudin Syria ta yi faduwa mafi muni a tarihi
Darajar Fam din Syria ta fadi zuwa 5,000 a kan Dalar Amurka daya
Darajar kudin kasar Syria ta yi faduwar da ba ta taba yin irinta ba a kasuwar canjin kudade ta bayan fage a ranar Talata.
Fam din Syria ya karye zuwa 5,000 a kan Dalar Amurka daya, wanda shi ne karon farko irin hakan ke faruwa tun bayan barkewar yaki a kasar shekara 10 da suka gabata.
- Rasha ta sace Daraktan Masana’antar nukiliyar Ukraine
- NAFDAC ta bukaci a kaurace wa magungunan tari da suka kashe yara a Gambiya
Tun a watan Satumba farashin canjin Dala a hukumance a Syria ya kai kimanin Fam 3,015, sabanin Fam 47 da ake canjin gabanin yakin.
Karyewar farashin Fam din Syria a kasuwar bayan fage na nufin darajarsa ta ragu da kusan kashi 99 cikin 100 idan aka kwatanta da farashinsa kafin fara yakin.
Sama da shekara 10 ke nan da tattalin arzikin kasar ya karye sakamakon barkewar yakin basasa.
Yakin ya yi tasiri kan tattalin arzikin makwabciyarta, Lebabon, wadda a yanzu haka ta takaita shigar Dalar Amurka a yankunan da ke hannun gwamnati.
Karyewar Fam din Syria ya sa kayan masarufi tashin gwauron zabo gami da kuncin rayuwa ga ’yan kasar, Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawancin matalauta ne.
Shirin Abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP), ya ce, kimanin mutum miliyan 12.4 — kusan kashi 60 cikin 100 — na al’ummar kasar na fama da karancin abinci.
Yakin basasar kasar ta yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 500,000, tare da raba kimanin rabin al’ummar kasar da muhallansu.