Darajar Naira ta ci gaba da faduwa
Darajar kudin kasar nan wato naira ya ci gaba da faduwa kasa warwas duk da matakan da Babban Bankin Najeriya na kaucewa hakan a farkon makon jiya. Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ce an samu farfadowar darajar kudin da fiye da kashi daya cikin 100 bayan da Babban Bankin Najeriya da wasu kamfanonin man […]

Darajar kudin kasar nan wato naira ya ci gaba da faduwa kasa warwas duk da matakan da Babban Bankin Najeriya na kaucewa hakan a farkon makon jiya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ce an samu farfadowar darajar kudin da fiye da kashi daya cikin 100 bayan da Babban Bankin Najeriya da wasu kamfanonin man fetur biyu sun sayar da dalar Amurka ga masu bukata. Daga bisani ne kuma sai ta ci gaba da faduwa. An dai kwashe lokaci mai tsawo ba a ga irin wannan ba. Kodayake, hakan na da nasaba da yadda farashin gangar danyen man fetur yake ci gaba da faduwa a kasuwannin duniya.
Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin Total ya gabatar da bukatar sayar da dala miliyan 80 ga masu bukata a ranar Litinin. Hakazalika, kamfanin Shell ya sayar da dalar domin sayan naira saboda gudanar da al’amuransa na yau da kullum.
A kasuwar canji ana sayar da dala akan naira 205 zuwa 208 a Jihar Legas da Babban birnin Tarayya Abuja, lokacin hada wannan rahoton. Masana kan harkokin tattalin arziki na sun bayyana cewa farashin dala zai ci gaba da kasancewa fiye da naira 200 saboda yadda bukatar dala ya zarce yawanta.