Darajar Naira ta fadi
A ranar Talata ne wani kwamitin hada-hadar kudi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da faduwar Naira, inda farashin Dala ya tashi daga Naira 155 zuwa 168.Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ne ya bayyana wa ’yan jarida haka a Hedikwatar bankin bayan sun fito daga ganawar kwamitin hadar-hadar kudi na bankin a ranar […]
A ranar Talata ne wani kwamitin hada-hadar kudi na Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da faduwar Naira, inda farashin Dala ya tashi daga Naira 155 zuwa 168.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ne ya bayyana wa ’yan jarida haka a Hedikwatar bankin bayan sun fito daga ganawar kwamitin hadar-hadar kudi na bankin a ranar Talata.
Bankin ya kuma kara kudin ruwa da kashi 1, inda ya karu daga kashi 12 zuwa 13 cikin 100.
Emefiele ya ce babu yadda za su iya ci gaba da kare darajar Naira tun bayan da kudin mai ya fadi.
“Darajar Naira ta fadi ne sakamakon faduwar farashin mai, hakan ya sanya ba za mu iya ci gaba da kare darajar Naira ba, sannan darajar Naira ta fadi ne sakamakon dokar takaita fitar da Dala da Hukumar Ajiye kudi na Amurka ya yi, tun a ranar 29 ga Oktoba, 2014.
Gwamnan ya ce tattalin arzikin kasar ya samu kansa a tsaka mai wuya ne, tun bayan da aka dogara a kan shigo da kayayyaki daga kasashen ketare.
Ya ce bai kamata a rika shigo da shinkafa da madara da jus da sauransu kasar nan ba.
Ya ce: “Mun fahimci za mu fada cikin mawuyacin hali tun da asusun ajiya ya ragu daga Dala biliyan 39 zuwa 36, mun samu kanmu cikin wannan matsalar ne saboda ba mu samar da wadansu hanyoyin bunkasa tattalin arziki ba. Da a ce mun dauki matakan bunkasa hanyoyin masu yawa da ba za mu fada cikin wannan halin ba. Me ya sa za mu rika shigowa da shinkafa? Me ya sa za mu rika shigowa da jus? Ko madara? Tun kafin a haife ni ake shigowa da madara kasar nan. Wane abu muke bukata kafin mu iya samar da madara a kasar nan? Ya kamata mu mayar da hankali a kan noma da kiwo ne kawai.”
Tsohon Shugaban Hukumar Samar da Haraji na Jihar Benuwai Mista Andrew Ayabam ya ce an shiga wannan matsala ce sakamakon dogara da shigo da kayayyaki daga kasashen ketare.
Ya ce a yanzu da Dala daya ta koma Naira 168, farashin kayayyaki zai karu, sannan hakan ba zai haifar wa tattalin arzikin Najeriya da mai ido ba.