Darajar Naira ta sake faduwa a kasuwa

Darajar Naira ta kara faduwa a kasuwar hada-hadar kudi ta bankuna inda aka canjata kowacce Dalar Amurka a kan N430. Adadin dai na nuna an samu ragin kaso 0.16 cikin 100 idan aka kwatanta da N430 da aka canja a ranar Litinin. Ban gamsu da sakamakon zaben Kenya ba, an tafka magudi — Raila Odinga […]

Darajar Naira ta sake faduwa a kasuwa

Darajar Naira ta kara faduwa a kasuwar hada-hadar kudi ta bankuna inda aka canjata kowacce Dalar Amurka a kan N430.

Adadin dai na nuna an samu ragin kaso 0.16 cikin 100 idan aka kwatanta da N430 da aka canja a ranar Litinin.

Canjin Dalar da aka yi kan N432 shi ne mafi daraja da aka yi a ranar Talatar, kafin ta daidaita kan N430.

Haka kuma an canja Dalar kan mafi karancin kudi na N417.

Jimillar Naira miliyan 50.40 ne dai aka yi canjinsu a kasuwar musayar kudin ta ranar Talata.