Darakta Tantiri ya tsallake rijiya da baya
A ranar Talatar da ta gabata ce fitaccen Daraktan fina-finan Hausa Ilyasu Abdulmumini Tantiri ya tsallake rijiya da baya, a lokacin da motarsa kirar fijo 407 ta kama da wuta a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Kano don zuwa karasa aikin wani fim mai suna ‘Kwamandan Mata.’ Daga baya daraktan ya […]
A ranar Talatar da ta gabata ce fitaccen Daraktan fina-finan Hausa Ilyasu Abdulmumini Tantiri ya tsallake rijiya da baya, a lokacin da motarsa kirar fijo 407 ta kama da wuta a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Kano don zuwa karasa aikin wani fim mai suna ‘Kwamandan Mata.’
Daga baya daraktan ya shiga shafinsa na Instagram ya sanar da mummunan al’amarin da ya faru da shi.
Ya ce: “Innalillahi wa Inna Iaihi Raji’un, wannan hoton motata ce take cin wuta a yanzu nan a kan hanyata ta zuwa Kaduna. Allah Ya kara tsare mu.”
Bayan wadansu awowi ne ya sanya hotonsa a shafin Instagram, sannan ya gode wa masoyansa da ’yan fim kan yadda suka nuna damuwarsu sakamakon mummunan al’amarin da ya faru da shi.
“Ina gode wa abokaina da ’yan uwana da masoyana da duk wadanda suka yi mini jaje, suka yi mini addu’a, suka yi mini kalaman karfafa gwiwa da kuma wadanda suka taimaka mini. Wannan hoton ya bayyana muku ina raye cikin koshin lafiya. Allah Ya ci gaba da kare mu. Na gode.” Inji shi.