Daraktan fim din Sangaya ya rasu

A ranar Talata da ta gabata da dare, Allah Ya yi wa Aminu Muhammad Sabo rasuwa, kamar yadda abokin sana’arsa, Bala Anas Babinlata ya bayyana a shafinsa na Facebook. Marigayin, wanda shi ne ya ba da umurni a fitaccen fim din nan mai suna ‘Sangaya’ da kamfanin Sarauniya da ke Kano ya shirya, an yi jana’izarsa […]

Daraktan fim din Sangaya ya rasu

Marigayi Aminu Muhammad Sabo

A ranar Talata da ta gabata da dare, Allah Ya yi wa Aminu Muhammad Sabo rasuwa, kamar yadda abokin sana’arsa, Bala Anas Babinlata ya bayyana a shafinsa na Facebook.

Marigayin, wanda shi ne ya ba da umurni a fitaccen fim din nan mai suna ‘Sangaya’ da kamfanin Sarauniya da ke Kano ya shirya, an yi jana’izarsa da safiyar Laraba da ta gabata a Unguwar Gwammaja Kano.

Allah Ya jikansa da rahma, amin.