Darasai ga masu son auren jari
A auratayya, akwai wani salo da wasu daga cikin mata suka shahara akan shi wanda masu sharhi suka sha yin sharhi a kai. Wannan ba wata halayya ba ce face ta aurar namijin da aka auna cewa yana da maiko, wato mai hannu da shuni kamar yadda ’yan salon magana ke cewa. Wannan wata halayya […]
A auratayya, akwai wani salo da wasu daga cikin mata suka shahara akan shi wanda masu sharhi suka sha yin sharhi a kai.
Wannan ba wata halayya ba ce face ta aurar namijin da aka auna cewa yana da maiko, wato mai hannu da shuni kamar yadda ’yan salon magana ke cewa. Wannan wata halayya ce da ake ganin gilmawarta a tsakanin mata da yawa. A wasu lokuta ya kai akan samu yanayin da ke nuna gudummawar da iyaye kan bada wajen ruruwar wannan lamari a zukatan matasan namu (mata).
Abin tambaya a nan shi ne wannan irin salo a kan mata kawai ya kebanta? Ko kuwa su ma mazan sukan yi fatan ganin zakaransu ya ba su sa’a a kan wasu matan da suke wa kallon nama-da-kitse?
Bari mu haskaka wannan matashiyar da wani al’amari da ya faru kwanakin baya a birnin Kano inda wani magidanci ya yi wa kansa gadar zare.
Shi dai wannan mutun ma’aikacin gwamnatin jahar ne wanda kuma yake zaune a wani rukunin gidaje mallakar gwamnati. Ya samu sa’ar shiga wani tsari da ya bai wa ma’aikata irin sa damar mallakar gidan da suke ciki ta hanyar sayar musu da shi a cikin sauki inda su kuma za su rika biya ta wani tsari da gwamnatin ta fitar.
To shi wannan magidanci ashe lissafi ne da ya zo masa a daidai, domin kuwa yana da nasa burin da yake ganin hanyar cikar sa ta zo.
Zan so in koma baya domin sanar da mai karatu cewa shi fa wannan bawan Allah yana da mata biyu. Ta farko tana da yara biyar, hudu daga ciki mata ne. daya matar kuma tana da nata yaran guda uku amma a wani gidan haya daban. Wato sun raba muhalli ke nan da uwargidan.
Da aka sanar da shi cewa gwamnati tana son su mallaki gidajen da suke ciki sai ya yi azama wajen nemo wanda zai sayi gidan a hannunsa tunda shi ba zai iya biya ba. A haka ne uwargidan ta nuna mahaifinta zai saya. Kamar wasa dai haka aka yi ciniki kuma aka biya kudin gida. Mai gida kuma ya amshi gida a matsayin haya daga surukinsa.
Da kudi suka shigo hannu sai ya biya gwamnati kudin ta a kan farashin da ta ba su, ribar da ya samu kuma sai ya sayi sabuwar mota ta alfarma. Sauran kudi kuma ya shiga shirin tabbatar da mafarkinsa da su.
To ashe dama wata bazawara ya hango mai hannu da shuni, watau kudi. Ma’aikaciya ce a wata babbar ma’aikatar gwamnatin tarayya. Gogan naka ya fara zawarci ba kama hannun yaro. Abokanai masu lissafi irin nasa suka shiga zuga shi cewa ai ya more in ya aure ta domin ba wata wahala da zai ci karo da ita, musamman idan an dubi irin alatun da bazawar ke rayuwa a ciki. A takaice dai yana ganin zai yi auren jari.
Bayan an daura aure kuma amarya ta tare da agololinta har uku. Ita take kula da kusan duk dawainiyar gidan, shi kuwa sai dai ya wanke goma ya tsoma biyar.
Kafin wani lokaci ya daga motarsa a kasuwa ya sayar. Wannan ya biyo bayan juya bayan da amaryar ta rika dandana masa bayan idonta ya bude. Ma’ana ta daina daukar dawainiyar gidan tun da ba alhakinta ba ne dama. Jim kadan bayan ya sayar da mota kuma sai ga notis daga surukinsa cewa zai sayar da gidan domin biyan wasu bukatu. Dole haka ya kukuta ya kama wani gidan domin ya mayar da uwargidan tare da ’ya’yanta biyar.
Hakika rayuwa ta yi masa zafi, don an kai lokacin da hatta biyan kudin makaranta na ’ya’yansa abin yana neman ya gagare shi.
Ba a yi nisa ba sai labari ya ishe shi ai wancan gidan da surukinsa ya fitar da shi daga ciki ya sayar ashe uwargidansa ce ta saye. Majiyar labarin nan ta tabbatar min da cewa da aka nuna wa uwargidan ba ta nuna halin dattaku a kan abin da ta yi wa maigidanta ba na korarsa daga cikin gidan da ta mallaka ba sai ta ce: “wannan shi ne irin abin da ya dace da duk mutumin da bai san Allah Ya yi masa rufin asiri ba. Haka ya fi dacewa da wanda ya samu dama amma ya banzatar da ita maimakon inganta makomar rayukan da suke wajibi a wuyansa”.
Wani abin bakin ciki da maigidan ta sake fadawa ciki shi ne yadda bayan ya sake samun tallafi daga abokai da ’yan uwansa sai amarya ta yashe duk abin da ya mallaka kuma ta kara gaba ita da ’ya’yanta. Ashe ta yi ritaya daga inda take aiki, kuma ta karbe kudinta ta kara gaba kuma har yau ba a ma san inda take ba.
Daga nan al’amura suka rincabe wa maigida, rayuwa ta yi muni sakamakon bibiyar son zuciya da kuma rashin hangen nesa. Wannan kuma darasi ne ga duk masu tunanin cewa ga giwa ta fadi bari su je su ci “banza”. Allah ya ganar da mu, amin.