Darasi da kalubalen da ke gaban harshen Hausa a yau
Takardar da aka gabatar a Taron kasa-Da-kasa domin karrama marigayi Farfesa Muhammadu Hambali Jinju a matsayinsa na Gwarzon Masani kuma Manazarcin Harshen Hausa, wanda kungiyar Marubuta Harsunan Nijar da takwararta ta Najeriya suka shirya daga 19 zuwa 21 ga Fabrairu, 2014, a Emir Sultan benue, Yamai, Jumhuriyar Nijar. Tsakure: Akwai shaida kwakkwara daga tarihi da […]
Takardar da aka gabatar a Taron kasa-Da-kasa domin karrama marigayi Farfesa Muhammadu Hambali Jinju a matsayinsa na Gwarzon Masani kuma Manazarcin Harshen Hausa, wanda kungiyar Marubuta Harsunan Nijar da takwararta ta Najeriya suka shirya daga 19 zuwa 21 ga Fabrairu, 2014, a Emir Sultan benue, Yamai, Jumhuriyar Nijar.
Tsakure: Akwai shaida kwakkwara daga tarihi da kuma zamanin da muke ciki da ke nuna mana cewa harshe, kamar al’ada, kan rayu ne ta hanyar yawaita amfani da shi. Haka nan kuma harshe, yana tafiya ne tare da zamani, ki da son masu amfani da shi. Wannan takarda tana da kudurin yin tsokaci kan tarihi da abubuwan da wannan zamani da muke ciki na karni na 20 da na 21 suka kawo, domin ta bayyana darussan da harshen Hausa zai karu da su, sannan ta kuma fito da irin kalubalen da harshen ke fuskanta domin masu amfani da shi, musamman Hausawa, su gyara zama. A karshe, takardar za ta kawo shawarwari don tunkarar wannan kalubale.
Gabatarwa: Tabbas harshen Hausa ya samu kulawar masana a tsawon zamunna. A nan cikin gida, kasar Hausa, malaman addinin Musulunci su ne na farko a wannan kulawar. Tarihi ya nuna mana cewa tun a wajajen karni na goma sha bakwai ne wannan harshe ya tsotsi tawwadar alkalami, ya kuma hau kan karagar takarda. A lokacin ne malamai suka zayyana tunaninsu da ilmin da suka samu a kan takarda, albarkacin rungumar Musulunci. Saboda wannan al’amari ne harshen Hausa ya samu bunkasar da wasu takwarorinsu ba su samu ba, ya kuma zama tangam da wasu da suka riga shi kamar Fulfulde. A karni na 18 har zuwa karshen na 19, rawar da masu Jihadin da Shehu Usmanu danfodiyo ya jagoranta ce ta kara yi wa harshen Hausa ado, musamman ta tabbatar da daidaitaccen tsarin rubutattun wakokin Hausa. Wadannan inganci da bunkasar harshen Hausa sun karu a karni na 20 lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka karfafa mulkinsu a kasar Hausa.
Tun kafin kafa mulkin mallaka da Turawa suka yi a farkon karni na 20, harshen Hausa ya sami wata kwalliya ba tare da su Hausawan sun sani ko nema ba. Wannan kwalliya ita ce yunkurin da wasu Turawa ’yan leken asirin kasashen Afirika suka yi na koyon harshen Hausa da rubuta shi kan takarda. Wannan kuwa ya faro ne tun wajajen karni na 18.
Malamanmu na cikin jami’o’i a Nijeriya da Nijar, su kuma ba karamar gudunmawa suka bayar ba wajen tabbatar da wannan kawa da harshen Hausa ya samu, da kuma dada masa martaba.
Duk da wannan tagara da harshen Hausa ya yi ta samu tun daga karni na 17, wannan takarda tana ganin cewa akwai sauran kasancewa a fagen daga. Dalilin haka ko shi ne, kalubalen da ya zo wa harshen gaba-da-gaba a wannan zamani, da rashin samun irin kaimin wadanda suka gabata suka sa, da kuma uwa-uba, rashin kishin kasa daga wadanda ya kamata su zama kan gaba a wajen nuna kishin harshensu. Sauran sassan takardar nan za su yi bayanin wadannan a matsayin ginshikanta.
Leko tarihi:
Kafa Baitul Hikma: A karni na 8 da na 9 ne halifofin Musulunci biyu, da da uba, suka kafa mashahurin gidan da ya zama tamkar jami’a. Halifa Haruna al-Rashid shi ne ya kafa Baitul Hikma a Bagadaza sannan da dansa, al-Ma’mun, ya hau gado ya ci gaba da inganta wannan wuri. Gidan ya kasance cibiyar fassara zuwa harshen Larabci na ayyukan da aka rubuta a zamanin wasu daulolin da aka yi kafin zuwan Musulunci, kamar Farisa (Iran) da Girika. Haka kuma ko bayan yin fassara, Gidan Hikima ya kasance wurin mudali’a da aiwatar da bincike. Wuri ne inda masana daban-daban suke kai caffa, su gina ilmi, su kuma ciyar da kasa gaba ta fuskar kere-kere da fadada ilmi a fagage daban-daban.
Darasi: Babban darasi ta fuskar harshe da za a kula da shi a sakamakon kafa Gidan Hikima shi ne, harshen Larabci ya karu da kalmomi musamman wadanda suka shafi bangarorin ilmi daga wasu al’ummomi da harsuna. Wannan ya samu tun daga farkon ayyukan gidan kuma amfanin ya ci gaba har zuwa yau. Haka kuma tattare da wasu dalilai daban, kafa Gidan Hikima ya kara fito da martabar harshen Larabci a idon duniya. A yau harshen yana daya daga cikin harsuna shida na Majalisar dinkin Duniya a hukumance. Sauran biyar din su ne, Sinanci da Ingilishi da Faransanci da Rashanci da Isfaniyanci.
Dangane da harshen Hausa kuwa, sai dai watakila a yi masa gori da cewa, da a ce masu shi sun yi wani abu makamancin Gidan Hikima, da tuni ya fada Majalisar dinkin Duniya, ya ce guminsa yake ci!
Sabbin kalmomi da bunkasar harshe a karni na 17 zuwa na 19: Wannan tarihi ba a boye yake ba. Sanin kowane dalibin Hausa ne cewa masanan wadannan karnoni sun yi gagarumar rawa wajen habaka da bunkasa harshen Hausa. A karni na 17 ne ake karfafa zaton cewa malaman addinin Musulumci ne suka fara dabbaka Hausa a kan takarda. Haka kuma su ne suka fara kirkiro rubutattun wakokin Hausa. A karni na 18 da na 19 ko an sami bunkasar rubutattun wakokin Hausa. Wadannan wakoki sun taimaka ga bunkasar harshen ta fuskar inganta adabi da kuma karuwar sabbin kalmomi daga Larabci da Fulatanci. Kalmomin da suka shafi addini sun shiga Hausa saboda babbar manufar jaddada addinin Musulumci ta malaman wancan zamani. Kalmomin Fulatanci ko sun shiga Hausa saboda malaman da suka rubuta wakokin mafi yawansu Fulani ne da suka ji Hausa. Haka kuma da yawa daga wakokin an fassaro su ne daga Fulatanci, kasancewar da yawa daga marubutan Fulani ne. Ta fuskar adabi kuwa, an sami karuwar bullar salailai da ka’idoji daga adabin Larabci, kamar amfani da ramzi wajen bayyana tarihin lokacin da marubucin waka ya rubuta ta.
Darasi: Malaman karni na 17 da na 18 da na 19, duk kauna da da’a da kishin addininsu da kuma jama’arsu, su suka sa su ba da wannan gudummawa ga harshen Hausa. Da ba su yi haka ba da watakila sai a karni na 20 da na 21 ne harshen zai fara ganin yunkurin yin haka, da watakila ‘watakilar’ ta yi ma harshen dumu-dumu. Misali, da watakila kalmomin da ke da tushe daga Ingilishi da Faransanci ne kurum harshen Hausa zai yi tinkaho da su, kamar wasu takwarorinsu. Watakila da harshenmu bai zamar wa takwarorinsa ‘dokin iska dan Filinge ba!’ Tilas harshen Hausa da Hausawa har kullum su kasance masu godiya ga magabatan nan na karnonin 17 zuwa 19. Ya kamata su nuna hikima irin ta wadannan magabata ta dauko kalmomi daga harsuna su ara wa harshen Hausa cikin hikima da kwarewa.
Rawar da Turawa suka taka: Kodayake Hausawa kan ce, ruwa ba ya tsami banza, suka kuma kirkiro makamancin wannan karin magana don su bi zamani suka ce, Bature bai aikin banza, duk da haka ba za a rasa abin a yaba ba dangane da rawar da Turawa suka taka wajen bunkasa harshen Hausa. Tabbas! Kishin kasashensu da al’adunsu da kuma son ganin sun cin ma manufofinsu ga rayuwa, su suka sa su taka rawar ga bunkasa harshen Hausa.
Cikin littafinsa da aka ambata a dure na 1, Yahaya (1988) ya fadi cewa Turawan Denmak ne suka fara rubuta Hausa da rubutun boko a karni na 18. Baturen da ya fara haka kuwa shi ne B. G. Niebuhr saboda dalilin zahiri na sha’awa. Tun daga wannan karni na 18 ne Turawa suka ci gaba da rubuta Hausa cikin rubutun boko kamar yadda suka yi ga sauran harsunan Afirika da suka sadu da su. Da suka ci kasar Hausa da yaki suka kafa mulkin mallaka a farkon karni na 20, sai kuma suka taka rawar masu mulki, suka kakkafa cibiyoyin samarwa da bunkasa littattafan Hausa cikin rubutun boko don su ji dadin mulki, kuma su kauce wa koyon rubutun ajami wanda da shi ne Hausawa ke rubutun Hausa tun kafin Turawan su zo.
Masana tarihin ilmin boko a Najeriya kamar Babs Fafunwa, da su kansu Turawa sun sani cewa makarantun da Turawa suka bude sun bude su ne don su sami ’yan kasa masu kama musu, su ji dadin mulki.
Darasi: Darasin da za a iya fahimta da shi a nan shi ne, Turawa sun taka rawa ga habakar harshen Hausa don suna kishin ganin cewa manufofin kasashensu sun samu. Wadannan manufofi sun hada da leken asirin kasar Hausa da yin ciniki da kuma mallake kasar Hausa. Wadannan su ne manufofinsu mafi girma.
Idan haka ne me zai hana su ko masu harshen Hausa su rungumi irin wannan kishi?
Rawar da ’yan kasa suka taka: Ko shakka babu cewa Hausawa ’yan kasa, musamman na farko, sun taka muhimmiyar rawa a fagen raya da bunkasa harshen Hausa. Sun lura da cewa harshen nasu na bukatar shiga cikin sahun sauran harsunan duniya da suka ci gaba. Shugabanni kamar Sardaunan Sakkwato kuma Firimiyan Jihar Arewa, Alhaji Ahmadu Bello, da Alhaji Abubakar Tafawa balewa, Firayim Ministan Najeriya na farko, da malaman makarantun boko na farko kamar Alhaji Abubakar Imam da Malam Sa’adu Zungur da Malam Mu’azu Hadeja, duk sun ba da gudunmawa ta bangarori da dama, kamar kafa kafafen yada labaru don amfani da harshen Hausa, ya yadu a duniya, da rubuta littattafan adabi kamar labarai da wakoki da wasannin kwaikwayo.
Samar da jami’o’i masu koyar da harshen Hausa wani fage ne na raya harshen. A cikinsu ne da manyan makarantu aka samu hazikan malamai masu kishin Hausa wadanda suka tashi tsaye don su ga harshen Hausa ya cin ma wancan matsayin na bunkasa. Wasunsu sun aiwatar da bincike suka gano hikimomin da ke cikin harshen, wasu sun kirkiro masa kalmomin nazari, a yayin da wasu suka karfafa kishin harshen.
Darasi: Kishin harshen Hausa da hazaka da sadaukar da kai su ne darasin da za a iya gani ga wadannan shugabanni na karni na 20 da na 21. Shin mu da muke ’ya’yansu da jikoki da tattaba-kunensu za mu kiyaye mu gado su? Fatar wannan takarda ke nan. To amma fa akwai bata-gurbi cikinmu, tsuntsayen da ke kukan gidan wasu tsuntsaye daban! Wadannan suna cikin abubuwan da takardar za ta kawo a bangare na gaba.
Za mu kammala a makon gobe
Dokta Aliyah, [email protected] da Sakina [email protected] malamai ne a Sashen Koyar da Harsunan Najeriya, Jami’ar Jihar Sakkwato