Darasi daga rikicin Kaduna
Hargitsin da ya faru a wani yanki na Jihar Kaduna har ya watsu zuwa cikin garin Kaduna ya koyar da wadansu muhimman darusa da ya kamata duk mai hankali ya lura da su. A duk lokacin da rikici ya tashi ana mayar da shi na addini ne, musamman a yankin Arewacin kasar nan, duk kuwa […]
Hargitsin da ya faru a wani yanki na Jihar Kaduna har ya watsu zuwa cikin garin Kaduna ya koyar da wadansu muhimman darusa da ya kamata duk mai hankali ya lura da su.
A duk lokacin da rikici ya tashi ana mayar da shi na addini ne, musamman a yankin Arewacin kasar nan, duk kuwa da cewa mabiya addinan suna zaman lafiya a tsakaninsu, amma sai wadansu zauna-gari-banza su tayar da fitina kuma su ce addininsu suke karewa. A sakamakon haka ne matasa suke tare hanya suna zakulo wadanda ba addininsu daya ba suna kashewa tare da kona dukiyoyinsu, ba tare da sun yi wani laifi ba, laifinsu kawai shi ne suna bin wani addini daban da na wadannan matasan da suka fada hannunsu.
A wannan karon, a yayin rikicin na Kaduna wadansu bayin Allah sun yi kokari wajen kare mabiya addinin da ba nasu ba daga halaka. Misali, akwai wani wanda aka yi hira da shi a Sashin Hausa na BBC da ya bayyana yadda ya kubutar da wadansu mabiya addinin Kirista daga halaka, lokacin da ya gansu a firgice cikin motarsu da aka farfasa gilasoshinta suna neman hanyar da za su shiga barikin soja, amma da ya fahimci idan suka wuce za su fuskanci matsala sai ya bude kofar gidansa suka shiga tare da motarsu, matarsa kuma ta taimaka wa matan da suturarta. Ana cikin haka sai wadansu matasa suka samu labarin cewa ya boye Kiristoci a gidansa don haka suka fado gidansa da nufin halaka Kiristocin nan, amma Allah Ya taimake shi ya kira jami’an tsaro kuma ya yi sa’a suka zo da sauri suka ceci wadannan Kiristocin suka kai su barikin soja.
Wannan bawan Allah ya bayyana cewa duk da mawuyacin halin da ya shiga bai yi nadama ba, domin saboda tsorata lokacin da matasan suka shiga gidansa za su yi ta’adi sai da matarsa ta suma.
Haka kuma akwai wani direban motar haya mai suna Jibiril Usman wanda ya bayyana a wata hira da aka yi da shi cewa ya dauko fasinja guda shida daga Kano zai kai su Abuja kuma fasinjojin dukkansu Kirista ne ’yan kabilar Ibo, lokacin da ya shiga garin Kaduna ya bi ta hanyar bayan gari, yayin da ya isa daidai wurin da ake kira Asikolaye sai ya gamu da matasan da suka tare hanya suna neman wadanda suke ganin ba Musulmi ba ne, shi kuma da ya ga haka sai ya kudurta aniyar yin iyakar kokarinsa don ya kubutar da fasinjojin nan nasa wadanda ba Musulmi ba, da yake shi dan gari ne a Kaduna, sai ya tuna da wani ofishin ’yan sanda da ke kusa da wurin da suke, saboda haka sai ya yi karfin hali wajen ganin ya tafi da fasinjojin nan can, a yayin wannan yunkurin ne matasan nan suka taso masa suna dukan motarsa suka ce dole sai ya tsaya, da ya ki tsayawa sai wani matashi ya caka masa wuka a hannu, amma duk da haka ya ki tsayawa har sai da ya kai su ofishin ’yan sandan. Allah Ya taimake shi ya mika su ga ’yan sanda lami lafiya, shi ne kawai aka raunata.
Ya bayyana cewa bai yi nadamar abin da ya yi ba, duk da halin da ta shiga, hasali ma dai ya ce ya gwammace shi ya rasa ransa domin fasinjojin nasa su tsira, domim ya san zai samu kyakkyawan sakamako a lahira, maimakon ya kyale a halaka su ya je lahira ya hadu da mummunan sakamako saboda ya taimaka wajen halakarsu.
A yankin Sabuwar Tasha da ke Kaduna kuma wani mabiyin addinin Kirista ne ya kubutar da wani Musulmi mai gyaran takalmi (shoe shiner), wanda ya fada wani gida ya shige cikin wurin da ake ajiye suturu (wardrobe) ya buya a yayin da rikicin ya taso, nan ya zauna har kusan kwanaki uku, wanda ya sanya ya galabaita, ya fita hayyacinsa. A cikin wannan halin ne wannan Kiristan ya gano shi, ya taimaka masa ya farfado, sannan ya nemo wani shugaban Hausawa wanda ya gane shi ya dauke shi zuwa wurin ’yan uwansa. Da wannan Kiristan mugu ne, da sai dai kawai ya karasa shi, amma da yake mutumin kirki ne sai ya tamaka masa ya tsira da ransa.
Sai kuma shi uban gayya, Gwamna Jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa’i, wanda ya je Abuja domin yi wa Shugaba Buhari bayanin halin da jihar tasa ke ciki, a kan hanyarsa ta dawowa ne da ya iso daidai tsohon wurin da ake karbar kudi daga masu ababen hawa (toll gate) kusa da Kaduna sai ya tarar da motaci sun taru, da ya tambaya sai aka ce masa ai matasan Gonin Gora ne suka tare hanya. Nan take ya wuce gaba ya ce sauran matafiya su biyo shi, yana isa Gonin Gora sai ya ga matasa sun sanya tayoyi sun tare hanya, suna ganinsa sai suka watse suka gudu, amma jami’an tsaro suka bi su suka kamo wadansu daga cikinsu, aka je aka tsare su, kuma ya tsaya a wurin har sai da motocin matafiya suka wuce. Wannan kokari da gwamna ya yi ya burge mutane, saboda wannan jajircewar da ya yi ya taimaka wajen tsirar da rayukan mutane da yawa, domin wannan wurin ya yi kaurin suna wajen halaka matafiya da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a duk lokacin da wani rikici ya tashi a garin Kaduna.
Wannan tu’annatin da matasa ke yi wa matafiya a Gonin Gora ya yi kama da irin wanda yake faruwa a yankin Dura Du na yankin Karamar Hukumar Jos ta Kudu, inda natasan kabilar Birom suke tare motocin matafiya suna kashe su ba tare da sun san abin da yake faruwa ba, laifinsu kawai shi ne su Musulmi ne da suka fito daga wata kabila da wadannan matasan suke kyama.
Haka kuma kokarin da Gwamna el-Rufa’i ya yi na zagayawa duk wuraren da ake rikicin ya taimaka kwarai wajen kwantar da rikicin, wanda hakan da ya yi ya jawo masa yabo, hatta daga abokan adawa na siyasa.
Irin wannan kokarin ne ya kamata shugabanni su rika yi a lokacin rikici, maimakon su zauna a rika kawo masu rahoton halin da ake ciki.
Daga abubuwan da suka faru, za a fahimci cewa duk rikicin da ake yi babu wanda yake da alaka da addini, wadansu zauna-gari-banza ne masu son satar kayan jama’a suke tayar da fitina sai su jingina shi da addini. Domin a rikicin da aka yi a Kaduna matasa sun rika farfasa wa mutane motocinsu suna sace masu waya, ba tare da bambantawa cewa mai motar Musulmi ne ko Kirista ba. A yankin Sabuwar Tasha kuma an samu rahoton cewa matasan sun rika fasa wa ’yan kabilar Ibo shaguna suna sata. Watau dai wadansu ne ke kokarin tayar da fitina domin su samu damar yin sata.
Ya kamata shugabannin addini na Musulunci da Kirista su rika wayar da kawunan matasa cewa duk wanda ya kashe wani a irin wannan rikicin wuta ce makomarsa idan ya mutu, idan kuma ya kwashi kayan mutane to sata ya yi.
Ya kamata kowa ya fahimci cewa tashin hankali ba ya yi wa kowa amfani, sai da zaman lafiya ne ake iya tafiyar da komi na rayuwa.