‘Darasi ga mahaifi’
Barkanmu da warhaka Manyan gobe. Yaya karatu? Tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Darasi ga mahaifi’. Labarin na nuni yadda dan cikin mutum zai iya sanya shi a hanya idan ya kauce. A sha karatu lafiya.An yi wani mutum mai suna Mallam Bello, makeri ne mai yawan shaye-shaye […]
Barkanmu da warhaka Manyan gobe. Yaya karatu? Tare da fatan kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Darasi ga mahaifi’. Labarin na nuni yadda dan cikin mutum zai iya sanya shi a hanya idan ya kauce. A sha karatu lafiya.
An yi wani mutum mai suna Mallam Bello, makeri ne mai yawan shaye-shaye da kuma rashin girmama mahaifinsa Shehu. Shehu ya tsufa sosai kuma ko tashi bai iya yi saboda tsufa ga shi dansa Bello ba ya ciyar da shi yadda yakamata.
Bello yana da da Nuhu wanda yake shiri da Kakansa Shehu kuma ba ya jin dadi game da yadda mahaifinsa ke walakanta masa Kaka kuma abin na ba shi takaici saboda ba zai iya magana ba.
Ran nan Shehu na cin abinci sai kwanonsa ya fadi har ya fashe. Ganin haka, sai Bello ya yi masa fada kamar zai buge shi.
Washegari Shehu ya samu katako ya kera wani kwano. Sai mahaifinsa ya ce da shi me zaka yi da wannan kwanon katakon? Sai yace yana kera masa ne domin idan ya girma ba sai ya rika zaginsa ba kamar yadda yake wa Kakansa. Wannan magana ta baiwa Bello mamaki tun daga ranar bai sake kuntatawa tsohonsa ba.