Darasi ga masu kin amincewa da auren dole (6)

A bangaren tsohuwar budurwarsa Samira kuwa, daga baya ne ta samu labarin mahaifan Ibrahim sun aurar masa da ’yar uwarsa (Halima).  Da farko ta damu, amma da ta tuna yadda rayuwa take sai ta yi musu addu’ar fatar alheri saboda irin horarwar da ta samu a gida.  Mace ce da ta yi ilimin addini da […]

Darasi ga masu kin amincewa da auren dole (6)

A bangaren tsohuwar budurwarsa Samira kuwa, daga baya ne ta samu labarin mahaifan Ibrahim sun aurar masa da ’yar uwarsa (Halima).  Da farko ta damu, amma da ta tuna yadda rayuwa take sai ta yi musu addu’ar fatar alheri saboda irin horarwar da ta samu a gida.  Mace ce da ta yi ilimin addini da na boko, sannan ta san ya kamata.  Tana girmama na-gaba. Hasali ma Samira ba ta da kawar da za a ce tana fada da ita ko gaba ko wani abu.  Yarinya ce natsattsiya, son kowa, kin wanda ya rasa. Ga shi daidai gwargwado iyayenta suna da hali amma wannan bai sa ta dauki girman kai da jiji-da-kai ta dora wa kanta ba.

Mutane na mamakin yadda duk da dukiyar da Allah Ya hore wa mahaifanta amma kuma take da saukin kai. Ba ta taba wulakanta ko cin mutuncin wani ko wata a rayuwarta ba. Takan girmama duk wanda ta hadu da shi musamman wadanda suka girme ta. A haka ta taso da wannan tarbiyya har ta kai matakin da take ciki a halin yanzu.

Shakuwar da ta yi da Ibrahim a lokacin da suke makaranta da kuma yadda ta samu labarin an yi masa aure ba tare da ya sanar da ita ba, abin ya dan taba ta. Amma a cikin zuciyarta sai ta tuna da cewa ai matar mutum kabarinsa ce domin haka sai ta fawwala wa Allah komai. Ta rungumi kaddara kuma ta yi wa Ibrahim da kuma ita kanta addu’ar Allah Ya hada kowa da rabonsa. Daga nan ta shiga tunanin yadda za ta ci gaba da rayuwa. Amma dai ta yanke shawarar ba za ta sake yin soyayya da wani saurayi a nan kusa ba har sai ta dan huta, hankalinta ya koma jikinta.

A bangaren Ibrahim kuwa, bayan an  samu wasu watanni, sai Halima (amaryarsa) ta samu juna biyu.  Zo ka ga murna a tsakanin Ibrahim da matarsa Halima da kuma iyayensu. Kowa sai addu’a yake  Allah Ya sauke ta lafiya.

Da cikinta ya kai wata tara sai Halima ta fara nakuda.  A lokacin Ibrahim yana can asibitin da yake aiki aka kira shi a waya aka shaida masa halin da Halima take ciki.  Nan da nan ya sa aka dauko ta zuwa asibitin da yake aiki don ya duba ta. Kamar abin nan ne da Hausawa kan ce ‘tuwona maina’.

Nan Dokta Ibrahim ya shiga kokarin ceto ran matarsa Halima, amma cikin ikon Allah hakan bai yiwu ba don Allah Ya karbi abinSa tun kafin ta haihu. An yi asarar uwar da kuma dan da ke cikinta.

Za mu ci gaba insha Allahu

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08097015805