Darasi ga masu kin amincewa da auren dole (7)

Nan fa hankalin Ibrahim ya yi matukar tashi.  Ya rika yin salati yana fadin:  “Daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma.”  Da kyar da jivin goshi aka shawo kan Dokta Ibrahim ta hanyar janyo masa ayoyi da Hadisan Manzon Allah (SAW) a kan ya dangana. Duk mai rai mamaci ne. “Kullu Nafsin Za’ikatul […]

Darasi ga masu kin amincewa da auren dole (7)

Nan fa hankalin Ibrahim ya yi matukar tashi.  Ya rika yin salati yana fadin:  “Daga Allah muke kuma gare Shi za mu koma.”  Da kyar da jivin goshi aka shawo kan Dokta Ibrahim ta hanyar janyo masa ayoyi da Hadisan Manzon Allah (SAW) a kan ya dangana. Duk mai rai mamaci ne. “Kullu Nafsin Za’ikatul Maut.”

Bayan kwana biyu komai ya lafa sai Dokta Ibrahim ya ci gaba da aikinsa da niyyar zai jima bai sake yin aure ba, domin a ganinsa da wuya ya sake samun mace  mai nagarta irin Halima. (Duk da lokacin da aka aurar masa ita bai so a ransa ba). Ka ga wannan ya zama tamkar wani darasi ga masu kin amincewa idan iyayensu sun yi musu auren dole.

Duk da haka akwai wadansu iyaye da suke yi wa ’ya’yansu auren dole saboda wata manufa ta neman abin duniya, musamman a vangaren mata inda sukan mayar da ’ya’yansu mata tamkar wata haja ta neman kudi. Sukan tilasta wa ’ya’yansu musamman mata kan su auri wani don su biya bukatarsu ta duniya kawai, ba don Allah suke yin haka ba.  A karshe sai ka tarar irin wannan aure tun ba a je ko’ina ba an samu matsala. Kai haka za ka rika samun labarin yadda wadansu matan kan kashe mazansu ta hanyoyi daban-daban.

Irin labaran da ake samu na yadda mata ke hallaka mazansu a yanzu, abin akwai tayar da hankali.  Mafi yawan masu aikata irin haka, idan ka bincika sai ka tarar an yi musu auren dole ne. Sai dai akwai wadanda ba don auren dole suke aikata irin haka ba, saboda son rai ne kawai da kuma hudubar Shaidan.

A vangare guda, ashe tsohuwar budurwarsa Samira ita ma ta zama Likita a wani asibiti da ke garinsu, kuma ba ta yi aure ba, tun  rabuwarta da Ibrahim. Saboda irin soyayyar da suka yi kafin su rabu a makaranta ya sa ta kasa natsuwa ta yi soyayya da wani namiji, ballantana ta yi maganar aure.  A kullum takan yi addu’ar Allah Ya zavar mata miji mafi alheri.

A can ne ta samu labarin abin da ya faru da tsohon saurayinta Ibrahim na rasuwar matarsa. Daga nan ta fara tunanin zuwa garin su Ibrahim don ta yi masa ta’aziyya, amma kafin nan sai ta yi shawara da iyayenta. Ta tabbatar hankalinsa zai yi matukar tashi idan suka yi ido biyu musamman ganin irin soyayyar da suka yi a baya amma ba su yi aure ba.

Da ta yi shawara da iyayenta, kuma ta shaida musu abin da ya faru da tsohon saurayin da ta yi mutuwar so, nan take iyayenta suka amince. Hasali ma, mahaifiyar Samira da wadansu daga cikin kannenta sun yanke shawarar za su raka ta garin su Ibrahim don su yi masa ta’aziyya.

Nan take suka sanya ranar da za su kai wa Ibrahim ziyara amma ba tare da sun sanar da shi ba.

Za mu ci gaba insha Allahu

Ahmed Garba Mohammed 08097015805