Darasi ga masu wulakanta dangi saboda matansu (1)
Masu bibiyar wannan shafi a kowane mako, ina yi muku sallama irin ta addinin Musulunci, assalamu alaikum. Kamar kullum yau ma mun kawo muku wasu muhimman batutuwa da suke ci mana tuwo a kwarya don fadakarwa mu taru mu gyara ko mu nemo mafita don mu gudu tare mu tsira tare. Yau za mu yi […]
Masu bibiyar wannan shafi a kowane mako, ina yi muku sallama irin ta addinin Musulunci, assalamu alaikum. Kamar kullum yau ma mun kawo muku wasu muhimman batutuwa da suke ci mana tuwo a kwarya don fadakarwa mu taru mu gyara ko mu nemo mafita don mu gudu tare mu tsira tare.
Yau za mu yi tsokaci ne a kan abin da ke damunmu a wannan lokaci inda wadansu mata ke mallake mazansu ta yadda hakan ke sa a wasu lokuta mazan ke aikata wasu abubuwa da ba su dace ba musamman cin fuska ko rabuwa da ’yan uwansu saboda ‘son’ da suke yi wa matansu ko da ba a kan hanya ta kwarai suke ba.
Mafi yawan irin wadannan mata da ke aikata irin haka suna yi ne saboda dalilai na kashin kansu. Ba su son wani na kusa da mijinsu ya rabe shi. Wadansu matan sukan raba mazansu da iyayensu. Sukan mana cewa da iyayen ba su haife shi, sun ba shi tarbiyya, sun dauki nauyinsa har ya girma ya zama mutum ba, da ba ta samu damar aurensa ba. Kuma abin takaicin sai a tarar da irin wadannan mata suna tattallin ’yan uwansu da iyayensu bayan watsi da na bangaren miji, sun wulakanta su. A gaskiya mata masu aikata irin wannan su sani hakan bai dace ba. Idan aka leka irin wadannan gidaje, za a tarar dangin matar suna kece-raini wajen yin abin da suka ga dama saboda ita ke juya akalar gidan, mijin ya zama hoto ko rakumi da akala. Kai akwai gidajen da za a tarar ’yan uwan matar ne suka yi kaka-gida, suka mamaye komai. Duk abin da suke so ake yi musu, su hau duk irin motar da suke bukata, su ci duk irin abincin da suke so, su sanya duk irin tufafin da suka so, a kai su duk irin makarantar da suke so amma a bangaren ’yan uwan mijin abin ba haka yake ba.
Sai a tarar babu wani daga cikin dan uwansa ko ’yar uwarsa da suka isa su shiga gidan su mike kafa. Saboda matarsa takan rika kyara da tsangwamarsu da nuna musu cewa gidan mijinta ne kuma ba su da ta cewa, don haka ba su isa su yi wani abu ba tare da yardarta ko amincewarta ba. Irin haka kan sa masu zuciya daga dangin mijin su daina ziyartar gidan. Su da dan uwansu sai dai hange daga nesa. Kuma irin wadannan maza a karshe sukan daina ziyartar gidajensu na asali, su tare a gidajen surukansu.
To abin tambaya shi ne, me ke kawo irin wannan dabi’a daga irin wadannan maza? Akwai abubuwa da dama kamar yadda bayanai suka nuna. Wadansu matan sukan mallake mazansu ne ta hanyar bin malaman tsibbu ko bokaye. Sannan mafi yawa daga cikin irin wadannan mata suna yi ne don su mallake dukiyar mijin tun kafin ya rasu. Wani lokacin kuma wadansu mazan ne ke da matsala, suna aikata haka ne saboda wasu dalilai na kashin kansu domin irin son da suke nuna wa matansu. Sun gwammace su rabu da ’yan uwansu a kan matansu. Amma da wani abu na rashin jin dadi zai samu mijin, to ’yan uwansa ne farko zai fara nema su kai masa dauki. Hakan ya nuna ’yan uwansa ba su jin dadinsa sai dai kawai idan ya shiga matsala ya nemi taimakonsu.
A kan haka ne na samu labarin yadda wani magidanci ya kori dan uwansa daga gidansa saboda matarsa ba ta shiri da kanen nasa, alhali akwai kannenta a gidan suna holewarsu ba tare da wata matsala ba. Hasali ma mijin ne ya dauki nauyin karatunsu da sauran dawainiyarsu, an ce har motoci ya saya musu suna fantamawa alhali ya kasa biya wa kanensa da suke uwa daya, uba daya kudin makaranta don ya ci gaba da karatu.
Ga yadda labarin ya kasance: A wani gari wadansu magidanta sun haifi ’ya’ya maza biyu, wa da kane. Ana kiran Yayan da Sulaiman yayin da ake kiran kanen da Nasir. Iyayensu sun rasu ne a lokacin da Sulaiman ke da shekara 8 yayin da Nasir ke da shekara 6 a duniya. Tun daga lokacin suka fara fuskantar kalubalen rayuwa. Sun ci gaba da rayuwa ne a karkashin kulawar kanen mahaifinsu da Allah bai ba shi haihuwa ba.
Za mu ci gaba
Za a iya tuntubar Ahmed Garba Mohammed ta: 08028797883