Darasi ga masu wulakanta dangi saboda matansu (2)
Bayan sun kammala karatun sakandare, sai shi ma kanin mahaifin Allah Ya yi masa rasuwa. A haka dai rayuwa ta yi musu zafi. A nan ne Suleiman ya shiga neman aiki, inda ya samu aikin kwadago yana kula da kansa da kuma kaninsa. A haka Suleiman ya ci gaba da yin karatu a makarantar gaba […]
Bayan sun kammala karatun sakandare, sai shi ma kanin mahaifin Allah Ya yi masa rasuwa. A haka dai rayuwa ta yi musu zafi. A nan ne Suleiman ya shiga neman aiki, inda ya samu aikin kwadago yana kula da kansa da kuma kaninsa.
A haka Suleiman ya ci gaba da yin karatu a makarantar gaba da sakandare shi da kaninsa Nasir.
Cikin ikon Allah, Suleiman ya samu nasarar kammala karatu har ya yi bautar kasa, yayin da Nasir kuma ya samu cikas don haka ya kasa ci gaba da yin karatu saboda rashin biyan kudin jarrabawa. Hakan ta sa ya kyale yayansa Suleiman ya ci gaba da karatu yayin da shi kuma ya koma kasuwa ya rungumi sana’a don rufawa juna asiri.
Bayan Suleiman ya kammala bautar kasa ne sai Allah Ya ba shi aiki a wani kamfani. Kafin ka ce kwabo ya samu daukaka, aka ba shi matsayin Manaja. Lokaci kankane ya sayi katafaren gida suka koma shi da kaninsa. Ya sayi motar hawa ya ci gaba da fantamawa. Rayuwa dai ta yi kyau.
Bayan wani lokaci sai Suleiman ya yi aure, kuma suka tare a gidan, yayin da kaninsa Nasir ya koma bangaren yara (Boys kuarters) tun da yayansa Suleiman ya yi aure.
Ana cikin haka ne da tafiya ta fara nisa, sai Nasir ya fara samun sabani da matar yayansa, musamman a kan irin wadansu dabi’u da ya ga tana yi, ta hanyar kokarin mallake mijinta ko ta halin ka-ka. Ya lura matar wansa ba ta son ta ga ya rabe shi, duk da kasancewarsu uwa daya, uba daya musamman a wajen yi masa wata kyauta, amma a bangarenta sai ya lura ta kwaso wasu daga cikin ’yan uwanta sun tare a gidan, kuma yayansa ne yake daukar nauyinsu. Wasa-wasa sai Suleiman ya fara juya wa Nasir baya. A da yakan yi shawara da shi, amma daga baya sai dai ya ji ya zartar da wani hukunci ba tare da ya shawarce shi ba. Ma’ana ya koma shawara da matarsa ce kawai shi kuma ya daina kula shi.
Hankalin Nasir ya fara tashi, sai ya fara neman hanyar da zai bi don ya dawo da yayansa Suleiman a kan hanya, amma ina! Suleiman ya yi nisa, ba ya jin kira.
Wata rana bayan Suleiman ya fita sai Nasir ya kalubalanci matar yayansa gaba-da-gaba kuma ya nuna mata bacin ransa a kan abin da ke faruwa a gidan. Bayan Suleiman (mijinta) ya koma gida ne sai ta fada masa gaskiya da karya wai Nasir ya ci mata mutunci. Ba tare da bincike ba sai ya kira Nasir ya umarci ya kwashe kayansa, kuma ya bar masa gida. Nasir ya yi bakin ciki, kuma bai bata lokaci ba ya tattara kayansa ya bar gidan, ya koma gidan wani abokinsa ne da suke kasuwanci tare.
Tun daga nan Suleiman bai sake neman kaninsa Nasir ko sanin halin da yake ciki ba, ya shiga holewa tare da matarsa da kuma ’yan uwanta a gidan.
Za mu cigaba
Za a iya tuntubar Ahmed Garba Mohammed a 08028797883