Darasi ga masu wulakanta dangi saboda matansu (3)

Tafiya ta yi nisa sai rayuwa ta fara canzawa Suleiman, bayan ya rasa aiki, a wani tankade da rairaya da ma’aikatarsa ta yi.  Rage ma’aikata aka yi kuma hakan ya shafi Suleiman. Hakan ta sa Suleiman ya shiga mummunan yanayi.  Ba a dade ba ya sayar da kadarorinsa ciki har da gidan da yake ciki […]

Darasi ga masu wulakanta dangi saboda matansu (3)

Tafiya ta yi nisa sai rayuwa ta fara canzawa Suleiman, bayan ya rasa aiki, a wani tankade da rairaya da ma’aikatarsa ta yi.  Rage ma’aikata aka yi kuma hakan ya shafi Suleiman.

Hakan ta sa Suleiman ya shiga mummunan yanayi.  Ba a dade ba ya sayar da kadarorinsa ciki har da gidan da yake ciki inda suka koma gidan haya.  Duk ’yan uwan matarsa da ke gidan suka watse, kai hasalima, matarsa ita ma da ta lura harkoki sun tsaya sai ta nemi ya sake ta, da ma Allah Bai ba su haihuwa ba.   Sai da ta tilasta shi ya sake ta daga nan ya ci gaba da rayuwa.

Abin ka da ikon Allah, ashe Nasir ya zama hamshakin mai arziki a kasuwancin da yake yi.  Ashe ya yi katafaren gida, yana da motocin hawa da na neman kudi.  Ya gina kamfanin da ya bunkasa har ya bude rassa a wurare da dama, hasalima har kasashen ketare yake fita don yin kasuwanci.

Wata rana sai kamfanin Nasir ya yi talla a jaridu yana neman ma’aikata.  Ba tare da sani ba sai Suleiman wanda yake neman aiki ruwa a jallo ya rubuta takardar neman aiki (Application). Suleiman ya yi sa’a yana daya daga cikin wadanda aka nema don a gana da su kafin a tantance wadanda za a dauka aiki a kamfanin Nasir.  Hakan ta faru ne ba tare da sanin Suleiman ko Nasir ba. 

Bayan an dauki sababbin ma’aikata ne ciki har da Suleiman sai aka nemi za su gana da shugaban kamfanin Nasir don su san shugabansu.

Bayan an kai su dakin ganawa da baki ne sai aka ce su zauna kafin shugaban kamfanin (Nasir) ya same su don ganawa da su.  Shigar Nasir ke da wuya sai ya nemi sababbin ma’aikatan da aka dauka su kimanin 10 da kowa ya gabatar da kansa.  Suleiman na daga kai sai ya hada ido da kaninsa Nasir.  Hankalin Suleiman ya yi matukar tashi.  Ya kasa cewa komai sai hawaye ne kawai ke zuba daga idanunsa.  Nan take Nasir ya koma ofis ya umarci a kira masa Suleiman.  Suleiman ya same shi, duk jikinsa ya yi sanyi.  Yana shiga ya zube kasa ya shiga neman kaninsa Nasir ya yafe masa a kan cin fuskar da ya yi masa.  Nasir ya nemi jin yadda abubuwa suka faru da wansa Suleiman har ya koma yana neman aiki.   Ya fada masa yadda ya samu karayar arziki har matarsa ta rabu da shi.  Nan dai Suleiman ya gane irin kuskuren da ya tafka wajen ci wa kaninsa mutunci saboda matarsa.

A nasa bangaren Nasir ya bayyana masa irin halin da ya shiga bayan Suleiman ya kore sa.  Amma cikin ikon Allah ya hadu da wani bawan Allah da ya samu labarin abin da ya same shi, kuma shi ne sanadiyyar samun arzikinsa.  Ya ce bawan Allah da ya yi masa haka, Allah Ya yi masa rasuwa amma Nasir ne ya ci gaba da daukar dawainiyar iyalinsa.  Hasalima ya yanke shawarar auren daya daga cikin ’ya’yan marigayin ne don ya ci gaba da karfafa zumunci.

Nan dai suka yafe wa juna, kuma Nasir ya ba Suleiman matsayin Manaja a kamfanin.  Sai daga baya ne ma’aikatan kamfanin suka fahimci  ashe Suleiman dan uwa ne ga shugabansu Nasir.  

A rana daya aka yi bikin Nasir da Suleiman, kuma Nasir ne ya gina wa Suleiman sabon gidan da ya tare da sabuwar matarsa kamar yadda Nasir shi ma ya tare a gidansa da sabuwar amaryarsa.

Daga nan Suleiman ya shiga yin nadama a kan abin da ya aikata wa kaninsa Nasir a baya.  Yau ga shi rayuwa ta canza, kaninsa da ya wulakanta shi ne ya rufa masa asiri.  A nan ya gane lallai dan uwa, dan uwa ne.

Da wannan labari nake jan hankalin magidanta da su rika shiga taitayinsu.  Su daina wulakanta ’yan uwansu saboda matansu.  Ba a ce su daina nuna wa matansu kauna ba, amma su sani kowa da irin matsayin da yakamata su ba shi.  Mutum zai iya rabuwa da matarsa amma ba zai taba rabuwa da danginsa ba. 

Yakamata wannan ya zama darasi ga masu wulakanta dangi saboda matansu.

Ahmed Garba Mohammed 08028797883