Darasi ga ’yan Najeriya
Garin Mubi, babbar cibiyar kasuwancin Jihar Adamawa, ya shiga cikin rudani ranar da ’yan Boko Haram suka far wa mutane, inda kowa ya yi ta tudun ceton rayuka. ’Yan ta’adda sun yi harbi kan mai uyw ada wabi, ind asuka halaka mutane da dama. Su kuwa wadanda suka tsira, sun yi ta shiga cikin kowace […]
Garin Mubi, babbar cibiyar kasuwancin Jihar Adamawa, ya shiga cikin rudani ranar da ’yan Boko Haram suka far wa mutane, inda kowa ya yi ta tudun ceton rayuka. ’Yan ta’adda sun yi harbi kan mai uyw ada wabi, ind asuka halaka mutane da dama. Su kuwa wadanda suka tsira, sun yi ta shiga cikin kowace irin mota ta samu,ba tare dala’akarin ta Kirista ce koMusulmi ko Ibo ko Bayarabe ko tad an Tibi ko Hausawa kai ko ma ta kowace kabila ce,ko mabiyin addini, shiga kawai aka rika yi don a samu a fice daga garin. Sojoji kuwa sun shige cikin motocin tare da fararen hula, inda sukarika rokon a ceci rayuwarsu; daruruwan mutanen da suka kasa samun motocin da za su gudu da su, sun shige cikin tsaunuka. A kokarin tsira da rayuwa da aka rika yi, babu wanda ya yi la’akari da addinin mutum ko kabilarsa kafin ya nemi taimakonsa. Hankoron neman tsira daga makiyi ya sanya an zama al’umma guda ba tare da nuna wariya ba. Bambancin kabilanci da addini ya yi kaura, abin da kawai ya rage shi ne mutumtakar dan Adam. Wadanda suka gudu Zuwa cikin tsasunuka, sun zauna tare da juna, sun tiamaki juna, don su gudu tare, su tsira tare.
Babban abin mamaki a cikin wannan al’amari, shi ne labarin Babban Hafsan tsaro, Eya Mashal Badeh, wanda dan asalin garin Mubi ne. inda aka samu rahoton cewa daf da za a kaddamar da hari a kan garin sai ya aiko jirgi mai saukar ungulu ya kwashe iyalansa daga garin. Gashi dai Babban Hafsan tsaro shi ne babban sojamafi girman mukami a Najeriya, kuma shi ke kula darundunonin sojojin ruwa da na sama da na kasa. Kafin zuwan ranar bakin ciki, an sha samun wani mutum daga Mubi da ke alfahari da cewa nan ne garin Babban Hafsan tsaro. Sai kuma gas hi ranar da ake bukatar taimajkonsa, sai ya kawashe iyalansa, ya kyale kowa ya yi ta kansa.. wannan na nuni da cewa yana da masaniya game da harin, a matsayinsa na babban kwamanda soja, mafi girman mukami, sai ya ki zuwa garin don jagorantar mutanensa a fagen yaki ko kuma ya bai wa al’ummarsa kariya. Sai kawai ya sadada a boye ya ceci iyalansa, har sojoji ma ya yi watsi da su don ba su da kwamanda mai kara musu kuzari da kwarin gwiwa,ta yadda za su tunkari ’yan ta’adda su kare al’ummarsa.
Darasin da ’yan Najeriya za su kowa daga wannan labara shi ne, a matsayinmu na mutane ba mu da wani abu da ya wuce makwaftanmu. A lokacin da kake buktar taimakon wani mutum, sai kawai ka kwankwasa kofar makwafcinka. Ga shi dai babu shugaban kasa ko gwamna ko dan majalisar dattijaiko minister da zai kawo maka dauki. To me zai sanya ka ci gaba da yaki da makwafcinka saboda wani ko wata da ba su damu kowaba sai iyalinsu kawai? Manyan mu na iya yaudarar mu game da hada addini ko kabila tare da su, amma tsawon lokacin sun nuna bas u damu da kowa ba. Sun yaudare mumuna ta kashe junanmu a rikice-rikicen kabilanci da na addini, a lokacin da suka hada kai wajen sace dukiyar mu.
Lokaci ya yi da za mu tashi tsaye, mu fadakar da juna, mu hada kai don yaki da babban makiyinmu. ’Yan siyasa su ne makiyanmu, ba makwaftanmu talakawa maza da mata da ke ta fafutika ba.
Shin a yanzu me mutanen Mubi za su yi alfahari da shikasancewar dan su shi ne Babban Hafsan tsaro? Idan ka je Otueke, inda Jonathan ya fito, akwai dimbin mutane da ke fama da talauci! Akwai dimbin talauci da wahalhalun rayuwa a garuruwan da daukacin gwamnoni da ministoci da ’yan majalisa da tsofaffin shugabannin kasa suka fito, a daidia lokacin da su da iyalansu ke watayawa da dukiyar da aka sameta ta hanyar tafka abin kunya. Ministar man fetur t akashe Naira biliyan 10 a hayar jirg8in samakawai. Irin wannan kudi za a iya amfani das u wajen shawo kan fatara da talauci a tsakanin al’ummomi da damada ke jihar ta. Stella Oduah ta sayi motoci biyu a kan Naira miliyan 120, a daidailokacin da mutane a garin da ta fito, wadanda ba za su mallakar Naira 500 din da za su ciyar da iyalansu a kowace rana ba.
Lokaci ya yi da za mu yi watsi da son ranmu! Mu goyi bayan mutum ko mace guda da ke da adalci don hidimta wa kowa da kowa a cikin kowace al’umma ba tare dala’akari da inda suka fito ba. A duk lokacin da wani ya fara yi maka magana a kan addini ko kabilanci, a yi watsi da shi kawai! Muna bukatar shugabannin da za su hada kanmu saboda tunaninsu na kyautata mutumtakar dan Adam fiye da kowane irin bambanci da ke tsakanin mu. Kuma duk wanda ya nuna gazawa a wajen jagorancin al’umma, lallai ku daina goyon bayan irin wnanan mutumin saboda kawai ya fito daga garinku.
Solomon Dalung na zaune ne a Jihar Filato.