Darasi na Ashirin da Daya

Isra’i da Mi’iraji Ma’anar Isra’i a takaice shi ne tafiyar da Mala’ika Jibril (AS) ya yi da Annabi (SAW) cikin dare daga Makka zuwa Masallaci Mai tsarki na Kudus (da ke kasar Palasdinu). Bayanin wannan tafiya ya zo a cikin Alkur’ani Mai girma, inda Allah (SWT) Yake cewa, “Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya yi […]

Darasi na Ashirin da Daya
Darasi na Ashirin da Daya

Isra’i da Mi’iraji

Ma’anar Isra’i a takaice shi ne tafiyar da Mala’ika Jibril (AS) ya yi da Annabi (SAW) cikin dare daga Makka zuwa Masallaci Mai tsarki na Kudus (da ke kasar Palasdinu). Bayanin wannan tafiya ya zo a cikin Alkur’ani Mai girma, inda Allah (SWT) Yake cewa,

“Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya yi tafiyar dare da BawanSa, daga Masallaci Mai alfarma zuwa ga Masallaci Mai nisa, wanda Muka sanya albarka a gefensa, domin Mu nuna masa daga ayoyinMu. Lallai ne Shi, Shi ne Mai ji Mai gani.” (Isra’i:1).

Shi kuma Mi’iraji yana nufin daukar Manzon Allah (SAW) daga Masallacin Kudus (Baitul-Makadis) zuwa matakai na sammai har zuwa ga fadar Allah don ganawa a tsakanin Annabi (SAW) da Ubangijinsa. Bayanin wannan tafiya da ganawarsa da Allah Ya fito a cikin Alkur’ani kamar haka:

“Kuma lallai ne ya gan shi, hakikatan, a wani lokacin saukarsa. A wurin da Magaryar Tukewa take. A inda taken, nan Aljarnar makoma take. Lokacin da abin da yake rufe Magaryar Tukewa ya rufe ta. Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ketare haddi ba. Lallai, tabbas (Annabinku) ya ga wadanda suka fi girma daga ayoyin Ubangijinsa.” (An-Najmi13-18).

Wannan al’amari, bisa kauli mafi rinjaye, ya auku ne shekara biyu da rabi kafin Hijirar Manzon Allah (SAW) daga Makka zuwa Madina. Malaman tarihi sun rawaito cewa an yi wannan tafiya ce ranar 27 ga watan Rajab a shekara ta 12 Bayan Aiko Manzon Allah (SAW). An yi kuma yi tafiyar ce  cikin dare daya zuwa da dawowa. Mala’ika Jibril (AS) ya tafi da Manzon Allah (SAW) a cikin dare, bisa saurin tafiyar haske, ya je ya yi Sallah a Baitul-Makadis sannan ya wuce matakai-matakai na sama, inda ya yi ta ganawa da Annabawan Allah (AS) har zuwa Magaryar Tukewa a wurin da shi Mala’ika Jibrilu ya jira Annabi (SAW) ya karasa zuwa ganawa da Ubangijinsa, sannan bayan kammalawa ya koma da Annabi (SAW) zuwa garin Makka, duk a cikin dare daya.

Koda yake Alkur’ani Mai girma ya tabbatar da wannan al’amari ne a takaice, amma cikakken bayanin abubuwan da suka faru ya bayyana ne cikin Sunnar Manzon Allah (SAW). Abubuwan da suka fito fili a wadannan bayanai su ne cewa ‘A cikin wani dare, Mala’ika Jibril (AS) ya je wajen Manzon Allah (SAW) ya dauke shi daga Dakin Ka’aba bisa wata dabba da ake kira Burak wadda take tafiya bisa gwargwadon saurin tafiyar haske, har zuwa Baitul-Makadis a Kudus. A nan ya tarar da Annabawan Allah (AS) da suka hada da Annabi Ibrahim da Annabi Musa da Annabi Isah (Alaihimus Salam) suna jiransa. Bayan Annabi (SAW) ya isa sai ya gaisa da su sannan ya yi musu limancin Sallah a masallacin. Bayan kammala Sallar tasu, sai Mala’ika Jibril (AS) ya sake daukarsa zuwa sama. A Sama ta Daya ya gaisa da Annabi Adam (AS) wanda ya tabbatar da Annabcinsa. Sai a Sama ta Biyu ya gaisa da Annabi Yahya (AS) da kuma Annabi Isah (AS). A kuma Sama ta Uku ya gaisa da Annabi Yusuf (AS), a Sama ta Hudu ya gaisa da Annabi Idris (AS), a Sama ta Biyar kuma ya gaisa da Annabi Haruna (AS). Da ya je Sama ta Shida kuma ya gaisa da Annabi Musa (AS) sannan a Sama ta Bakwai ya gaisa da Annabi Ibrahim (AS). Daga nan kuma aka dauki Manzon Allah (SAW) zuwa Sidratul-Muntaha, wurin da ke lullube da haske mai yawa. A wannan wuri ne aka nuna masa abubuwan al’ajabi masu dimbin yawa. A nan ne aka nuna masa cikakkiyar halittar Mala’ika Jibril aka kuma nuna masa wani wuri da ake kira Baitul-Ma’amur, wurin da a kowace rana mala’iku dubu saba’in suke shiga don yin Sallah.

A wannan wuri ne aka hau da shi wurin Allah Jalla Wa’ala wanda GirmanSa ya daukaka ya kusance Shi har sai da ya kai kusancin baka biyu. Sai Allah Ya yi wa BawanSa wahayi kuma Ya farlanta wa al’ummarsa yin Sallah sau hamsin a dare da wuni. Sai ya dawo har ya iso wurin da Annabi Musa (AS) yake sai ya ce masa me aka yi maka umarni? Ya ce salloli hamsin. Sai Annabi Musa (AS) ya ce: “Al’ummarka ba za su iya ba ka koma wurin Ubangijinka ka roke Shi Ya saukaka musu. Da Annabi (SAW) ya waiga wajen Jibrilu (AS) sai Jibrilu ya yi masa ishara da eh, idan ka so. Daga nan sai ya koma ya roki Allah a rage masa al’ummarsa ba za su iya ba, sai aka rage goma ya sake shudewa ta wurin Annabi Musa (AS) ya sake nanata maganarsa ta farko sai ya juya ya kara neman a rage al’ummarsa ba za su iya ba. Annabi (SAW) bai gushe ba yana saukowa Annabi Musa (AS) yana mayar da shi har sai da Sallah ta zama sau biyar a rana. Nan ma ya nemi ya koma a kara ragewar ya ce: “Hakika Bani Isra’ila sun kasa sun yi rauni suka bar abin da bai kai wannan ba. Amma sai Annabi (SAW) ya ce masa “Hakika ina jin kunyar Ubangijina na yarda na sallama.” A nan aka ba shi abubuwa guda uku, wato salloli guda biyar, aka saukar masa da ayoyi biyu a karshen Suratul Bakara, sannan aka yi masa alkawarin cewa dukan al’ummarsa za su samu rabon Aljannah face wanda Ya yi shirka da Allah wajen bauta kuma bai kaurace wa aikata munanan kaba’irai ba. Sannan an nuna wa Manzon Allah (SAW) Aljanna da ni’imomin da ke cikinta an kuma nuna masa gidan wuta da irin yadda ake azaba a cikinta. Bayan haka ne kuma aka dauke shi aka dawo da shi zuwa garin Makka, duk a cikin wannan dare.

A washegari da Manzon Allah (SAW) ya fito ya sanar wa wadansu mutane abin da ya faru da shi. An rawaito cewa da Ummu Hani, ’yar uwar Manzon Allah (SAW) ta ji wannan labari sai ta shawarce shi da kada ya sake gaya wa kowa wannan labari domin za su karyata shi, kuma a yi masa isgilanci. Amma Manzon Allah (SAW) bai kula da wannan ba, don haka ya bayyana wa jama’a abin da ya faru da shi. Nan da nan kuma mushirikai suka taru a gaban Dakin Ka’aba a karkashin jagorancin Abu Jahil suna tattauna wannan labari, suna dariya da isgilanci ga Manzon Allah (SAW) da mabiyansa.  Har ma aka samu wadansu da suka musulunta a baya sun kasa gaskata Annabi (SAW) a kan wannan al’amari kuma suka warware imaninsu, suka yi ridda.

Ganin haka sai Abu Jahil bisa tunanin  Sayyidina Abubakar (RA) zai shiga sahun wadanda za su karyata wannan batu, ya tura a sanar da Abubakar labarin abin da yake faruwa. Amma da jin wannan labari sai Abubakar (RA) ya ce “Idan dai har Annabi (SAW) ya ba da wannan labari to hakika wannan al’amari ya auku, don haka ya yi imani da labarin, yana mai cewa ai Annabi (SAW) ya fadi abin da ya fi haka ma kuma mun gaskata shi.” Wannan dalili shi ya sanya aka sanya wa Sayyidina Abubakar (R.A) lakabin As-Siddik.