Darasin rayuwa daga labarin uba da dansa (2)

Ganin haka fa aka dauki yaron nan zuwa asibiti, aka kwantar da shi. Bayan wani lokaci likita ya tabbatar da cewa ya zama dole ya gutsure yatsun yaron, idan ba haka ba kuwa ciwon daji zai lahanta dukkansu. Haka fa aka yi, yaro ya koma mai dungulmi. Mahaifin yaro dai takaicin duniya ya ishe shi, […]

Darasin rayuwa daga labarin uba da dansa (2)

Ganin haka fa aka dauki yaron nan zuwa asibiti, aka kwantar da shi. Bayan wani lokaci likita ya tabbatar da cewa ya zama dole ya gutsure yatsun yaron, idan ba haka ba kuwa ciwon daji zai lahanta dukkansu. Haka fa aka yi, yaro ya koma mai dungulmi.

Mahaifin yaro dai takaicin duniya ya ishe shi, ya rasa sukuni, saboda wannan aika-aika da ya aikata, inda abin ya kara dugunzuma shi ma shi ne, sai da ya je asibiti rann an domin ganin halin da dan nasa yake ciki. Yaron na ganin babansa, bayan sun gaisa sai ya ce masa. “Baba, ka ga hannuna yadda ya koma, yaushe ne yatsuna za su dawo kamar yadda suke a da?”

Jin wannan bayani na dansa, sai hawayen takaici ya kwararo masa. Nan take ya tashi ya fita daga dakin jinyar, ya nufi motarsa da ya aje a waje. Yana isa wurin motar sai ya nufi daidai wurin da dan nasa ya karta masa, domin kuwa duk tsawon lokacin nan bai ma taba duba barnar da yaron ya yi masa ba. Da ya duba sai ya ga ashe yaron ba kartawa ya yi ba, rubutu ne ya yi mai ma’ana a jikin fentin motar. Ga abin da ya rubuta da Ingilishi: “Ina kaunarka babana!”

Ganin wannan kyakkyawan lafazi da yaron nan ya rubuta, ya sanya babansa ya kara rikicewa. Allah Sarki! Ashe ma ba barna ya yi ba, gyara ne ya yi, amma ga shi saboda saurin fushi, ya haddasa wa dansa nakasa! Mahaifin yaron ya shiga wani mawuyacin hali, hankalinsa ya gushe. Nan take ya bazama gida da gudu, ya hadiyi guba ya mutu. Takaici goma da gomiya!

Ko mun gane darasin da ke cikin wannan labari? Babban darasin da ya kunsa dai shi ne, mu rage ba dukiya daraja. Maimakon haka, mu rika daraja mutane. Da a ce maigidan nan bai shaku da son abin duniya ba, ba zai yanke wa wannan da nasa irin wannan mummunan hukunci ba.

Wani darasin kuma shi ne, mu daina zartar da hukunci a cikin gaggawa ko a lokacin da muke cikin fushi. Da a ce lokacin da yaron nan yake rubutu, mahaifinsa bai harzuka ba, da a ce ya kwantar da hankalinsa ya bincika, kila da bai yanke masa wannan hukunci ba. Don haka, mu tabbatar da cewa mun gudanar da bincike kafin zartar da kowane irin hukunci.

Kullum mu rika mutuntawa da daraja dan Adam, maimakon daraja dukiya. Mu kula da abin da muke tunanawa a zuciya, wannan zai sanya mu rika furta kalamai na kirki. Kalaman kirki kuwa su ke haifar da ayyukan kirki, a lokacin da ayyukan kirki kuma ke haifar da dabi’ar kirki. Ita kuwa dabi’ar kirki, ita ke haifar da nagartaccen mutum.

Allah Ya sanya mu dace, amin. Sai kuma mako na gaba idan Allah Ya kai mu, amin.

 

 

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos