Darasin zaben jihar Ekiti
A Najeriya ba safai ne dan takarar da ya sha kaye a zabe yake amincewa da haka ba, balle kuma a ce zai gaggauta taya abokin takararsa murna sakamakon nasarar da ya samu. Amma Gwamnan Jihar Ekiti, Dokta Kayode Fayemi bai gwada irin wannan halin ba, bayan bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi […]
A Najeriya ba safai ne dan takarar da ya sha kaye a zabe yake amincewa da haka ba, balle kuma a ce zai gaggauta taya abokin takararsa murna sakamakon nasarar da ya samu. Amma Gwamnan Jihar Ekiti, Dokta Kayode Fayemi bai gwada irin wannan halin ba, bayan bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar da aka yi a makon jiya. Ya yi kyawun kai, ya kuma kawar da kidahumancin da ke dabaibaye ‘yan siyasar kasar nan. Ya mika wuya ga tsohon gwamnan jihar, Cif Ayodele Fayose, sa’anan kuma ya yi masa mubaya’a, ba tare da juyayi ko turarrabin komai ba. Ta haka ne Gwamna Fayemi ya dara tsara a harkokin siyasa, ya kuma nuna shi wayayye ne, mai aiki da ilminsa da basirarsa don kare mutuncin jiharsa da kuma daukaka matsayin mutanensa. Ya ki kwatanta halayya irin ta ‘yan siyasan da ke sanya kafafu suna shure sakamakon zabe, sa’annan su koma gefe guda suna kokarin tsokalo sama da kara. Hakan ya ba ‘yan Najeriya da yawa mamaki matuka, kuma rungumar kaddarar da ya yi ya sa an fahimci cewa ana iya yin siyasa ba da gaba ba a kasar nan.
Wannan al’amari ya sa ‘yan Najeriya jinjina wa Dokta Kayode Fayemi, domin ya ki yarda da gutsuri-tsoma, ko tunzurin da zai tayar da gagarumar rigimar da za ta janyo masifun da za su kare kan jama’arsa. Saboda haka nan sai ya ki bayar da dama ga masu son haddasa fitina su kai ga biyan bukatunsu cikin ruwan sanyi. Ya fahimci cewa abin da arziki bai yi ba, tsiya ba ta wanzar da shi ba. Duk masifun da za su biyo bayan tozarta sakamakon zaben ba za su yi wani tasiri ba, hasali ma kara tabarbara al’amura za su yi, daga karshe a zo ba a dauri kashi ba, amma an bata igiya.
Abin da ya afku a Jihar Ekiti a makon jiya ya nuna cewa ‘yan Najeriya, ko kuma a ce ‘yan shiyyar Kudu-maso-Yamma, sun fara guje wa al’amuran da suka wakana a jamhuriya ta farko da ta biyu, wadanda suka sanya shiyyar yin kaurin suna a siyasance, hakan kuma ya jefa su cikin tsananin wahalar da har yanzu suke fama da illolin da ta haddasa musu.
Dambarwar siyasar da ta biyo bayan zaben Majalisar dokokin Jihar Yamma a Jamhuriya ta farko, tsakanin magoya bayan Cif Obafemi Awolowo da kuma Cif Samuel Ladoke Akintola ta bakanta jihar a idanun duniya, kuma hakan ya janyo mata koma baya a harkokin mulki da na siyasar kasar nan. Haka nan kuma a Jamhuriya ta biyu an tayar da kura tsakanin magoya bayan Cif Akin Omoboriwowo na Jihar Ondo, dan takarar jam’iyyar National Party of Nigeria, NPN, wanda aka ce ya kayar da tsohon ubangidansa, Cif Makel Ajasin na jam’iyyar Unity Party of Nigeria, UPN, har ta kai ga kone-konen dimbin gidaje da kashe-kashen rayuka bila-adadin.
Mutanen Jihar Ekiti, wacce aka kirkiro daga tsohuwar Jihar Ondo da ta shahara wajen ba-ta-kashin siyasa na sane da haka, sun kuma fahimci cewa sakamakon zaben makon jiya zai iya haddasa gagarumar fitinar da za ta iya kone jihar kurmus, kuma kowane bangare tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar APC da kuma na PDP na iya tayar da kurar da za ta kasance kwatankwacin ta yakin Badar. Shi ya sa Gwamna Kayode Fayemi ya guji mayar da jiharsa filin daga, har a yi amfani da rundunonin askarawan da aka jijjibge a wurare daban-daban a Ado-Ekiti don kar a zubar da jinin wadanda ba su ji, ba su gani ba, babu kuma abin da za a yi, sai dai a yi ta kuka, a gaji, a yi Allah Ya isa. Ita kuwa Allah Ya isa ba ta komai da dan biri sai dai ta kara masa tsawon bindi.
Shi ya sa da suka fahimci haka sai suka mayar da fadan da ya fi karfinsu wasa. Ta haka ne aka wanye lafiya, kamar irin na mai wasa da macijin tsumma, sojoji na can nesa, jama’a kuma na ci gaba da harkokinsu na neman abinci cikin lumana da kwanciyar hankali. Idan ma har akwai wasu abubuwan da ba su ke nan ba, wadanda suka wakana lokacin zaben, ko kuma suka biyo bayan sakamakonsa, Gwamna Kayode Fayemi ya ce shi da jam’iyyarsa sun tattara bayanai game da haka, za a kuma tura su ga hukumomin da suka dace don bin bahasi.
Wannan babban darasi ne ga ‘yan Najeriya, musamman ma ga jama’ar Arewa, wadanda ake bugunsu, a kuma hana su kuka, watau a tattafka magudin zaben da zai canja ra’ayinsu, a kuma riga su tayar da fitinar da za a dafa masu don a tabbatar sakamakon bogin da aka tsara ya tabbata. An ga yadda ta kaya a zaben shugaban kasa da na gwamnoni a wasu jihohin Arewacin kasar nan, inda aka tunzura jama’a da gangan don su tayar da kayar baya, daga bisani kuma aka samu sukunin yin amfani da askarawa don hana su kusantar wuraren tsara sakamako da bayyana shi don a yi cuwa-cuwar da ake so. Daga bisani aka tayar tarzoma, aka ce su ne salsalarta, aka yi ta karkashe su da kokkona muhallansu. Yanzu dai gani ga wane ya isa ishara, kuma idan gemun danuwanka ya kama wuta sai ka aske naka dungurungum.