Dare Dubu Da daya (3)

A daidai lokacin da Frank Edgar a can Lardin Sokoto ke tattara labarai da tatsuniyoyi da tarihe-tarihen kasar Hausa ya ci karo da labaran da aka fada masa da baki, amma sai da ya bincika sai ya gane cewa ai labarai ne daga littattafan Larabawa, musamman Alfu Laila. Wannan ne ya sa ya shiga laluce, […]

Dare Dubu Da daya (3)

A daidai lokacin da Frank Edgar a can Lardin Sokoto ke tattara labarai da tatsuniyoyi da tarihe-tarihen kasar Hausa ya ci karo da labaran da aka fada masa da baki, amma sai da ya bincika sai ya gane cewa ai labarai ne daga littattafan Larabawa, musamman Alfu Laila. Wannan ne ya sa ya shiga laluce, har ya gano cewa tuni an fassara littafin cikin Hausa baki dayansa.

Daga baya ya wataya tsakanin garuruwan Argungu da Kabbi da Sokoto da yankin Zamfara ya tattaro fassarar da aka yi baki dayanta daga hannun malamai, ya adana a wuri daya ta yadda a lokacin ake da cikakken labaran Alfu Laila tun daga daren farko har na 1,001. Sai dai ba a buga su ba, sai yanzu da aka sake tace da gyara Hausar domin amfanin Hausawa.

Daga wannan aiki da aka yi an fahimci wani abu game da littafin na Alfu Laila, musamman abin da ya shafi kayan cikin sa da yawan mutane ke masu abubuwan tir da Allah wadai. Wannan yanayi za mu kalla a wannan bangare na sharhin.

Tun muna yara ba abin da aka horar da mu da shi irin kada mu matsi littattafan da za su iya bata mana tarbiya, musamman irin na Dare Dubu Da daya, wadanda a lokacin nan ba su wuce littafi na 1 zuwa na 5 ba. An ce ba komai cikin sa face batsa da ashararanci. kila shi ya sa ma ba a ci gaba da aikin fassara shi zuwa Hausa ba, kusan shekara 100 da soma aikin.

To amma da Allah Ya kai hannunmu kan cikakken labarin Dare Dubu Da daya cikin Hausa, muka shiga aikin fassara da tacewa tun daga dare na 1 zuwa 1,001 sai muka fahimci an yi wa wannan aikin littafin sanin damisar Bunu. Lallai akwai alamun batsa da sakin hannu wajen bayyana rayuwar mata da maza ko samari da ‘yan mata, amma sai muka lura cewa kashi 10 cikin 100 ne wadannan kalamai suke ciki, kusan kashi 90, ilimi ne da fadakarwa da nusarwa. Karanta su kuwa zai kara wa yara sanin duniya da guje mata da ilmin yadda za su tunkari rayuwa, har su girma.

Littafin Alfu Laila da muka sake tacewa cike yake da wakokin wa’azi da fadakarwa. Cike yake da jawabai masu ilmantarwa da suka shafi kimiyya da ilmin taurari da sanin labarin kasa da addinin Musulunci da babbar lamarin da ya shafi rayuwa da mutuwa.

Ga misali domin mu kara fahimta sosai daga baitocin da ke nuni da tashi in taimake ka a cikin littafin:

Tashi ka motsa ka bar nan wurin,

Gida ne na tsoro da halin tsiya.

Ka nemi wadata cikin duniya,

Akan kama zomo da son juriya.

Kasan duk wahala takan zan gudu,

Sauki yakan zo bayan shan wuya.

Wurin duk da an kaddara mutuwar,

Mutum za ya komo ba ya tirjiya.

Ina gargadin ka a kan sirrukanka,

Ka boye su gam-gam cikin zuciya.

Haka ta bangaren wa’azi da fadakarwa, dubi abin da wannan wakar ke cewa:

Ka duba alamu na karfinsu ne,

Da dai-dai da dai-dai duka sun mace.

Kai mai karatu a nan gun tsaye,

Ka dubi sadaukan ga duk sun wuce.

Shiga daga ciki ka dau darasi,

Na mazan jiyan nan da duk sun mace.

Mutuwa ta riske su babu shiri,

Ta murde ta watsar kamar dai a ce.

Ba su taka doro na wannan kasa ba,

Kamar masu cin kasuwa sun wuce.

Saboda haka muna iya cewa shi kowane aikin adabi a doron kasa yana zuwa ne da siffofi da kamannu iri daban-daban, wasu su kasance masu farantawa, wasu kuma su kasance masu bakantawa. Abin da yawancin al’umma ke yi shi ne su nazarci aiki domin tsince tsakuwa daga cikin aya. Yin haka yake taimakawa wajen amfani da wanda yake mai kyau, a kuma yi kaffa-kaffa da wadanda ba su da dadin ji ko karantawa. Shi aikin adabi a kullum rayayye ne, ba ya kuma mutuwa ta har abada.

Fatarmu ita ce Allah Ya sa wannan aiki da aka yi na sake fassara da tace wannan littafi na Alfu Laila ya kasance abin amfani gare mu da duk al’ummar Hausawa. Ba sai mun nanata ba, darussan da ke jibge a cikin littafin Alfu Laila ba na jiya ba ne, ba kuma na yau ba ne kurum, darussa ne da ke tare da mu har zuwa gobe da za a nade shimfidar kasa, lokacin da za mu koma ga Maiduka, mu amsa tambayoyi kan abin da muka tara da yadda muka yi amfani da su. Allah ya kara nuna mana gaskiya, a a matsayin gaskiya domin mu ci gaba da bin ta, ita kuma karya ya fayyace mana ita, domin mu ci gaba da guje mata! Amin!