Dare: fim a kan siyasa da aikin jarida

A makon jiya ne Kamfanin shirya fina-finan Hausa da ke garin Kaduna mai suna Abnur Entertainment ya kammala daukar fim din ‘Dare’ a garin Kaduna.Fim ne mai dauke da jigon siyasa da kuma aikin jarida, inda ’yan wasa irinsu Adam Zango da Rabi’u Rikadawa da Tijjani Faraga da Nafisa Abdullahi da Maryam Booth suka taka […]

Dare: fim a kan siyasa da aikin jarida
Dare: fim a kan siyasa da aikin jarida

A makon jiya ne Kamfanin shirya fina-finan Hausa da ke garin Kaduna mai suna Abnur Entertainment ya kammala daukar fim din ‘Dare’ a garin Kaduna.
Fim ne mai dauke da jigon siyasa da kuma aikin jarida, inda ’yan wasa irinsu Adam Zango da Rabi’u Rikadawa da Tijjani Faraga da Nafisa Abdullahi da Maryam Booth suka taka rawar gani.
Labari ne a kan Alhaji Yawale (Rabi’u Rikadawa) da Alhaji Shehu (Tijjani Faraga), wadanda suke takarar gwamnan Jiharsu a karkashin Jam’iyyar APDM. Alhaji Shehu ya fi Alhaji Yawale farin jini  a wurin jama’a.
Al’amarin ya ba mutane mamaki a lokacin da aka zo taron jam’iyya sai Alhaji Yawale ya janye wa Alhaji Shehu. Ya yi hakan ne a cewarsa don a gudu tare a tsira tare. Ashe akwai lauje cikin nadi dangane da batun janyewar.
Akwai Nura (Adam A Zango) da A’isha (Nafisa Abdullahi) ’yan jarida da ke aiki a gidan talabijin. Wata rana A’isha tana kan hanyarta ta zuwa wurin aiki sai ta ga wadansu ’yan daba har sun fito da wata gawa sun jefar da da ita a cikin wani kango, sannan suka shiga motarsu suka bar wurin. Daga nan ta rika bin su a baya da motarta har suka shiga cikin wani gida. Ta yi wayon bin su har ciki, daga nan ta dauko kyamararta bayan ta rakabe a wani wuri, sannan ta rika daukar abin da yake wakana. Ana cikin haka sai Alhaji Yawale ya fito ya kuma rika magana da ’yan dabar, daga nan ya ce mutum na karshe da take ya ke so su kashe masa shi ne wannan babban abokin hamayyarsa Alhaji Shehu.
 Da ta gama ji sai ta juya za ta gudu bisa tsautsayi sai suka ji alamar tafiyarta. Nan da nan suka leko sai kuwa suka ganta har ta shiga motarta, kuma har sun gane ta, kasancewarta fittaciyar ’yar jarida ce. Nan fa suka bi ta. Sai ta kira abokin aikinta Nura, wanda shi ne saurayin Fatima (Maryam Booth) ’yar gidan Alhaji Shehu wanda ake so a kashe, Bayan ya dauka sai ta fada masa halin da ake ciki, ta kuma ce ya sanar da Alhaji Shehu, kasancewar a halin yanzu suna biye da ita. A haka ta samu ta shiga wata kwana ta boye kyamarar, sannan ta ci gaba da tuki. A nan suke kama ta su kashe ta.
Daga nan za a shiga dambarwa har zuwa karshen fim din.
Furodusan fim din Abdul Amart ya ce sun shirya fim din ne a ganin kamfaninsu wajen ganin ayyukansu sun shafi kowane bangare na rayuwa, ba wai su takaita ga jigon soyayya ba. Baya ga haka suna yin abin da ke tafiya da lokaci da kuma abin da masu kallo suke so.
Kamfani: Abnur Entertainment, Shiryawa: Abdul Amart,  Tsara Labari: Fauziyya D Sulaiman, Umarni: Adam A. Zango.