Dare mafi tsada a cikin rayuwar Musulmi
Daren lailatul kadari kamar yadda mu Hausawa muka fi kiransa, shi ne dare mafi tsada a cikin kowace shekara ta Allah kamar yadda malamai daban-daban suka bayyana a cikin tafsirin surar Alkur’ani ta (97 aya ta 3.) Haka ma hadisai da dama sun tuzgo suna magana akan wannan dare mai alfarma. A cikin waccan ayar, […]
Daren lailatul kadari kamar yadda mu Hausawa muka fi kiransa, shi ne dare mafi tsada a cikin kowace shekara ta Allah kamar yadda malamai daban-daban suka bayyana a cikin tafsirin surar Alkur’ani ta (97 aya ta 3.) Haka ma hadisai da dama sun tuzgo suna magana akan wannan dare mai alfarma. A cikin waccan ayar, Allah Mai girma da daukaka ya bayyana muna cewa, Lailatul kadari tafi wata dubu alkhairi. Duk wani abu da za mu aikata na alkhairi, tun daga kan karatun Alkur’ani mai girma, sallar nafiloli, ambaton Allah da sauransu a wannan dare, to ya fi alkhairi bisa ga yin wata dubu muna aikata su. To Allah Ya sa mu dace.
Da yawa malamai sun tafka muhawara akan ko yaushe ne Lailatul kadari? Amma dai tare da haka kowa ya yarda a cikin wannan wata ne mai alfarma! Sai dai wace rana ce? Nawa ne ga wata? Nanne inda aka samu rabuwar bakin maluma. Wasu malamai dai sun yi tsayinsu cewa wannan dare boyayye ne, kawai dai mutum ya yi ta biyar watan na Ramadana da yin ibada yana mai raya dare-rai har Allah Ya say a dace da wannan dare.
Akwai malamai da ke da ra’ayin cewa daren Lailatul kadari yakan fado ne a daren farko na watan Ramadana, wasu kuma suka ce bakwai ga wata, wasu kuma suka ce 19. Sai dai duka wadannan zantukan suna da rauni. Mafi girma da karfi tare da shahara, shi ne hadisin da Bukhari ya ruwaito, Manzo mai tsira da aminci ya ce mu yi kirdadon wannan dare a cikin kwanaki goma na karshe. Wannan hadisin kuma ya kara samun kwari
da hadisin Ubayy dan Ka’ab da ya nuna daren yakan zo ne a daren 27 na watan Ramadana. Wannan kuma ita ce maganar da mutane da malamai da yawa suka tokare akanta. Babban abin bukata dai shi ne, mutum ya kasance farke yana mai ibada ga Allah tare da rokon bukatunsa, saboda kasancewar wasu mala’aikun Allah muhimmai kan sauko a wannan dare domin gabatar da ayukka daban-daban. Ciki kuwa harda diyautawa daga shiga wuta tare da jiran mutum ya roki bukatarsa a amsa masa. Buhari da Muslim sun ruwaito cewa, Manzon Allah mai tsira da aminci ya ce: ‘’Duk wanda ya sallaci LAILATUL kADARI yana mai imani tare da fatar samun sakamakonsa, Allah zai yafe masa dukkan zunubansa da suka gabata. Tirkashi! Kunji fa!
Allah zai yafe masa dukkan zunubansa da suka gabata! Muna fatar AllahYa sa mu dace da wannan dare. Babbar addu’ar da ya fi dacewa dai mu mayarwa hankali da yi a wannan dare, ita ce addu’ar da Annabi SAW ya koyar da Nana Aisha AS a lokacin da ta nemi haka. Manzon Allah ya umurce ta da karanta “Allahumma innaka `afuwwun tuhibbul `afwa fa`fu `annee” ma’ana ‘’Ya Allah Kai mai afuwa ne, kana son afuwa, ka yi min affuwa’’ Wannan ita ce addu’ar da ya fi dacewa mu lizamta a kowane dare cikin wannan wata, musamman kwanaki goma na karshe da aka fi tsammanin samun wannan dare a cikinsu. Uwa uba daren ashirin da bakwai.
Idan da ni ne kai! Bayan wannan addu’ar da ke sama, zan samu wata ‘yar gajeruwar takarda, sai in samu wuri in zauna a natse bayan an sha ruwa, in kwantar da hankalina sosai da sosai, ina mai tunanin ababen da nake neman biyan bukatarsu a wajen Allah. Ta haka zan rika rubuta su daya-bayan-daya har zuwa iya abin da nake iya tunawa. Wannan kuma saboda kasancewar rayuwar dan Adam da take cike da mantuwa. Sai dai wannan kawai ba zai wadatar ba, akwai bukatar sauran ababe guda uku
1.Samun wuri mai natsuwa kuma mai natsar da zuciya a lokacin gabatarda wannan muhimmiyar addu’a! Ina ma laifin cikin masallaci? In ma so samu ne ai shiga itikaf ma zai fi. Amma dai bukatar ita ce, samun cikakkar nutsuwa da mayar da hankali kacokan zuwa ga Allah. Sai mutum ya fara bi daya bayan daya yana gayawa Allah bukatunsa.
2. Yin tunani matuka game da hanyar da za a bi domin samun abinda aka roki Allah. Misali: Idan na roki Allah Ya shiryar da ni akan hanyarsa, to tun daga wajen da nake wannan addu’ar, cilas ne ya zamo akwai kudurin komawa makaranta da kuma lizimtar bauta wa Allah a cikin zuciyata! Wanda kuma yake rokon Allah Ya hore masa abinda ya yi aure, sai ya kasance a cikin zuciyarsa akwai tunanin hanyar da zai bi halastacciya ta samun wannan abin larurar, kamar yin wata sana’a koda kuwa sana’a ce da ake ganin mai yin ta ba zai iya tsinanawa kansa komai ba. Idan dai muka roki Allah a wannan dare da zuciyaya budadda, lalle za mu sha mamaki.
3. Aiwatar da ababen da aka saka a zuciya za a aiwatar. Mai neman shiriya ya lizimci zuwa makaranta tare da wuraren da ake ambaton Allah, mai neman kudin aure yayi kasuwa ko wani wajen mai kama da ita, mai neman aiki sai ya dauki takardunsa zuwa ofisoshi da sauran ma’aikatu…… Kada mu manta fa, wannan dare shi ne dare mafi tsada a cikin rayuwar musulmi.
Nasir Abbas Babi 08033186727/08095653401