daruruwan matasa sun yi zanga-zangar adawa da yunkurin tsige Gwamna Al-Makura
daruruwan matasa sun gudanar da zanga-zangar lumana a shekaranjiya Laraba don nuna adawa da yunkurin tsige Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura da Majalisar Dokokin Jihar take yi.Matasan sun sanya shinge a hanyar Mararraba da ke karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa wadda ita ce hanyar shiga Abuja daga Arewa, kuma sun gudanar da zanga-zangar […]
daruruwan matasa sun gudanar da zanga-zangar lumana a shekaranjiya Laraba don nuna adawa da yunkurin tsige Gwamnan Jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura da Majalisar Dokokin Jihar take yi.
Matasan sun sanya shinge a hanyar Mararraba da ke karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa wadda ita ce hanyar shiga Abuja daga Arewa, kuma sun gudanar da zanga-zangar a birnin Lafiya da garin Keffi da manyan hanyoyin da ke karamar Hukumar Akwanga suna dauke da kwalayen da aka rubutu goyon bayan Gwamna Al-Makura da suka hada da “Ku kyale mana Al-Makura.”
Matasan sun sassanya wuta wa tsofaffin tayoyi a yankunan da suka hada da Titin Fadar Sarkin Lafiya da Hanyar Doma da hanyar Keffi zuwa Mararraba kuma suka yi yunkurin datse hanyar tarayya ta Abuja zuwa Keffi kafin ’yan sanda su tsoma baki.
Masu zanga-zangar sun jawo cushewar ababen hawa a hanyar Keffi zuwa Abuja inda suke kiraye-kirayen majalisar ta dakatar da wannan yunkuri nata.
A ranar Litinin ce Majalisar Jihar ta umarci a ba Gwamna Al-Makura takardar sanar da shi yunkurin tsige shi bisa zargin aikata ba daidai ba..
Kakakin ’yan sandan Jihar Nasarawa, Ismaila Numan, ya ce rundunarsu ta kara yawan jami’an tsaro a manyan garuruwan jihar sakamakon zanga-zangar, kuma ya ce sun samu nasarar tarwatsa masu zanga-zangar kafin lamarin ya kazanta a garuruwan da lamarin ya shafa.
Mista Numan ya ce ba a samu asarar rai ko dukiya ba a yayin zanga-zangar inda ya tabbatar wa al’ummar jihar da niyyar rundunar na ba da cikakkiyar kariya ga rayuka da dukiyarsu.