Daruruwan ’yan APC sun koma NNPP a Kano

Jami’yyar ta ce ta yi murna da samun ƙarin magoya baya a ƙaramar hukumar.

Daruruwan ’yan APC sun koma NNPP a Kano

NNPP

Jam’iyyar NNPP a Karamar Hukumar Wudil, a Jihar Kano, ta samu ƙarin magoya baya, inda daruruwan ’ya’yan Jam’iyyar APC suka koma jam’iyyar.

Da ta ke karɓar waɗanda suka sauya sheƙar, Shugabar Riƙo ta Ƙaramar Hukumar Wudil, Hajiya Bilkisu Yusuf Indabo, ta bayyana farin cikinta ganin yadda NNPP ta samu ƙarin magoya baya.

Ta ce, wannan ya tabbatar da irin kyawun jagoranci na Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma jagoran jam’iyyar Injiniya Rabi’u Kwankwaso.

Sai dai ta tabbatar wa waɗanda suka sauya sheƙar cewa sun yi zaɓi na ƙwarai, sannan ta ba su tabbacin za a yi tafiya da su ba tare da nuna bambanci ba.

Shugabar ta kuma bayyana waɗanda suka sauya sheƙar cewa, Jam’iyyar NNPP da ma ta al’umma ce, kuma mai son ganin ci gaban al’umma ce.

Amma ta yi kira ga al’umma da su tabbatar cewa a zaɓen 2027 sun zaɓi Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso a matsayin Shugaban Ƙasa.

Da yake jawabi, Shugaban Matasan Jam’iyyar APC a madadin sauran waɗanda suka sauya sheƙar, Malam Zakarai Gidan Dabino, Kofar Yamma Wudil, ya ce sun ƙuduri aniyar komawa NNPP ne, domin ganin yadda Gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugabar Ƙaramar Hukumar Wudil suke tafiyar da tsarin jagorancinsu na tausaya wa al’umma da kuma samar musu da abubuwan more rayuwa.

Ya ce cikin ƙanƙnin lokaci a Ƙaramar Hukumar Wudil, shugabar ta yi abubuwa da tunda aka samar da karamar hukumar ba a taba samun shugaban da ya yi haka ba.

Sauran waɗanda suka yi jawabi a wajen taron, sun bayyana goyon bayansu ga Jam’iyyar NNPP da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sun ce gwamnan yana tafiyar da salon mulkinsa irin na Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ta hanyar sauya akalar yadda a baya ake nuna halin ko-in-kula ga ci gaban rayuwar talaka.