Darussa 10 daga fim din ‘Gidan Aure’
Kamfanin Songs and Film Limited da ke Abuja ne ya shirya fim din ‘Gidan Aure’, wanda ya kunshi labari a kan ma’aurata, inda ya nuna matsalolin yau da kullum da ke gudana a gidajen ma’aurata, ba tare da kuma an yi hobbasar magance su ba.Labarin ne a kan ma’aurata Kabiru (Sadik Ahmad) da matarsa Maryam […]
Kamfanin Songs and Film Limited da ke Abuja ne ya shirya fim din ‘Gidan Aure’, wanda ya kunshi labari a kan ma’aurata, inda ya nuna matsalolin yau da kullum da ke gudana a gidajen ma’aurata, ba tare da kuma an yi hobbasar magance su ba.
Labarin ne a kan ma’aurata Kabiru (Sadik Ahmad) da matarsa Maryam (Fatima Yusuf) da kuma Misbahu (Ali Nuhu) da matarsa Basma (Nafisat Abdullahi).
Fim din na kunshe da darussa kamar haka:
1. Illar da ke cikin neman kudi da wadansu mata suke yi kafin mijinsu ya sadu da su, inda Maryam ta rika neman kudi a wurin mijinta Kabiru kafin ya sadu da ita.
2. Matsalar rashin iya biya wa mata bukatar wajen saduwa. Kamar yadda Misbahu ya kasa biya wa matarsa Basma bukatarta ta saduwa. A nan za a fahimci ba wai ciyarwa da shayarwa da muhalli da kuma tufartawa ke magance matsalolin mata ma’aurata ba, har da bangaren biyan bukatar saduwa.
3. Illar minshari a tsakanin ma’aurata ba tare da an kai ga yin bayaninsa ba. Misbahu ya rika yin minshari, inda hakan yake hana matarsa Basma barci, hakan kuma ya sanya take jin haushinsa.
4. Rashin tattauna matsala tsakanin ma’aurata.
5. Matsalar rashin iya girki daga bangaren mata. A fim din an ga irin halin da Basma ta shiga, inda Kabiru ya daina cin abincinta, ya koma ci a waje. Inda hakan ta sanya ya kamu da son Hafsat (Maimuna Wata Yarinya).
6. Yawan kawaici na sanya a cutar da kai, kamar yadda Misbahu ya rika minshari, ita kuma Basma ba ta iya girki ba, amma tsananin yadda suke son junansu ya sa suka kasa fada wa junansu abin da yake ci wa kowannensu tuwo a kwarya.
7. Muhimmancin malaman addini wajen warware matsalar ma’aurata, kamar yadda Malam Hashim (Rabi’u Rikadawa) ya taka muhimmiyar rawa, inda ya fito a matsayin malami da ke warware matsalar gidan Kabiru da matarsa Maryam da kuma gidan Misbahu da matarsa Basma.
8. Illar yaudara, inda Hafsat (Maimuna wata yarinya) ta rika yaudarar Khalid (Lawan Ahmad), duk da kasancewar ya biya sadaki. Daga baya Khalid ya gane cewa yaudararsa take, kasancewar hankalin Hafsat ya koma wurin Misbahu.
9. Muhimmancin hakuri a rayuwa. Khalid ya yi hakuri duk da abin da aka yi masa, inda a karshe ya ci riba.
10. Illar rashin binciken da iyayen ke yi dangane da rayuwar auren ’ya’yansu.
Yakubu M. Kumo da Habeeb Mu’azu ne suka rubuta labarin fim din. Kamal S. Alkali ya ba da umarni. Bashir Datti ya shirya shi.
’Yan wasan sun hada da: Ali Nuhu da Sadik Ahmad da Fatima Yusuf da Nafisa Abdullahi da Ladidi Fagge da Rabi’u Rikadawa da sauransu.