Darussa daga Hadisin Matafiya Uku

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika Kuma madalla da Shi da Ya sanya mana ni’imarSa, cikin gane al’amurran rayuwa a misalai daga karantarwar Alkur’ani da Hadisan ManzonSa.  Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon […]

Darussa daga Hadisin Matafiya Uku
Darussa daga Hadisin Matafiya Uku

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai. Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu, Wanda da ni’imarSa kyawawan abubuwa suke cika Kuma madalla da Shi da Ya sanya mana ni’imarSa, cikin gane al’amurran rayuwa a misalai daga karantarwar Alkur’ani da Hadisan ManzonSa.  Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Manzon Allah, Annabi Muhammadu dan Abdullahi (Sallallahu Alaihi Wasallam), wanda Allah Ya aiko shi ya kasance jinkai ga talikai, kuma manuni gare su wajen samun abubuwan more rayuwar duniya da Lahira. Amincin Allah ya tabbata ga alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi gurabunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  
Lallai ne, mafi kyawun cikar zance shi ne Littafin Allah (Alkur’ani), kuma mafi alherin shiriya ita ce ta Annabi Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam). Mafi sharrin al’amari shi ne wanda aka kirkire shi cikin addini; duk abin da aka kirkira cikin addini bata ne, dukkan bata kuma karshenta wuta. Allah Ya kare mu daga gare ta. Amin.
Bayan haka, yau makalarmu za ta yi tsokaci ne don samun darussa daga wani Hadisi da ya yi bayanin wadansu waliyan Allah guda uku da suka yi tafiya, har ta kai su ga (shiga) wani kogo, inda suka samu mafaka don su kwana su huta, sannan su wuce su ci gaba da tafiyarsu. Suna cikin kogon ne kuwa wani katon dutse ya gangaro ya toshe musu kofar kogon, ta yadda ba su da wata hanya ta fita. Sai suka rasa yadda za su yi, saboda haka suka ce, babu yadda za a yi su fita, sai dai su roki Allah ta hanyar tawassuli (jingina) da ayyukan alherin da kowanensu ya aikata a rayuwarsa, don su samu Allah din Ya taimaka musu su fita! Za mu ga yadda ta kaya, insha Allah!
In Allah Ya so, kuma cikin taimakonSa, za mu fitar da Hadisin, kamar yadda aka sanya shi a cikin shahararren littafin nan na Imamu Abu Zakariyya, Yahya bin Sharf An-Nawawiy, wato Riyadussalihina Min Kalami Sayyidil Mursalina, sannan mu bi mu ga wani abu daga cikin sharhin da ke kunshe a kan kowane abin tawassuli da aka yi amfani da shi wajen samun hanyar fita daga cikin kangin toshiyar bakin kogon. Allah nake roko Ya yi mana sakayya da abin da yake daidai a cikin mukalar, Ya gafarta mana kura-kuran da ka auku, amin.
Shi wannan Hadisi ya zo a karkashin Babin Ikhlasi (tsarkake aikin ibada don Allah kawai) da halarto da (kyakkyawar) niyya a cikin dukkan ayyuka da zantuka da halaye na bayyane da boye, wanda aka fara budewa da ayar Alkur’ani ta 5, a cikin surar Bayyinah, inda Allah Yake cewa, “Kuma ba a umarce su da komai ba, face bauta wa Allah, suna masu tsarkake addinin gare Shi, masu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsayar da Sallah kuma su bayar da zakka, kuma wannan shi ne addinin wadanda suke a kan hanyar kwarai.”

Yadda Hadisin Matafiya Uku yake:
An samo daga Baban Abdurrahman, Abdullahi dan Umar dan Khaddab (Allah Ya yarda da su), ya ce, ‘Na ji Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), yana cewa, “Wadansu mutum uku daga cikin wadanda suka zo kafin ku (suka gabace ku, wato mutanen da), sun yi tafiya har sai da suka kai yammaci, saboda haka suka nemi wajen hutawa su kwana, sai suka kai wajen wani kogo, suka shige cikinsa, sai wani dutse ya mirgino ya rufe musu bakin kogon, ta yadda ba su da wata hanyar fita. Sai suka ce, “To lallai, yadda al’amari yake ba abin da zai tseratar da mu daga wannan dutse, sai dai mu roki Allah Ta’ala (muna tawassuli) da kyawawan ayyukanmu. Sai daya da cikinsu ya ce, “Ya Ubangiji, na kasance ina da iyayena biyu (uwa da uba), wadanda suka tsufa kwarai, kuma na daukar wa kaina (na yi alkawari), cewa ba na gabatar da kowa da komai a kansu ba, na cikin iyalina ko abin da ya shafi wata dukiyata, in dai bukatarsu ta taso. Wata rana sai neman wata itaciya ya same ni, na kuma tafi neman, ban koma na biya musu bukatarsu ba, har sai da suka yi barci. Ko da na dawo na tatso musu abin shansu, sai na zo na iske sun rigaya sun yi barci, ba su farka ba, ni kuma na kyamaci in tayar da su daga barcin, alhali suna cikin hutawa, kada in yanke musu ita; kuma sai na ki ba kowa daga cikin iyalina abincinsu kafin na iyayen nawa. Saboda haka sai na zauna alhalin abin shan nan yana hannuna, ina dakon (sauraron) su farka don in shayar da su, har sai da alfijir ya keto. A tsakanin wannan lokaci da nake dakon su farka, kananan yarana suna ta kukan yunwa da bukata a gefena, ban ko kula su ba, ina dai sauraron tsofaffin nan nawa su farka tukunna, sannan in shayar da su.
Haka dai na jira har sai da suka farka, sannan suka sha abin shan nasu. Ya Allah Ubangiji! Idan na aikata wannan al’amari da na aikata don neman yardarKa ne, Ka bude mana abin da muka kasance a cikinsa na toshewar kofar kogo da wannan dutse ya yi mana.” Sai kuwa dutse ya gusa (muskutawa ko matsawa) kadan, amma duk da haka dai ba za su iya fitowa ba.
“Sai wani daga cikinsu (wato na biyunsu ke nan) shi kuma ya ce, “Ya Ubangiji, yadda al’amari yake shi ne na kasance ina da wata ’yar baffana, wadda take mafi soyuwar mutane a wurina; (a wata ruwayar an ce), “Na kasance ina son ta kamar yadda mutum yake da tsananin so ga mata,” saboda haka na nemi in sadu da ita, amma sai ta ki (na yi juyin duniyar nan, na nace mata dai, amma ta ki). Ana nan haka, sai da wata shekarar tsanani ta same ta, ta kasance ba yadda za ta yi ta fita cikin wannan tsanani da ya takura ta, sai ta zo gare ni neman taimako, sai na ba ta Dinari dubu ashirin a kan sharadin lallai sai mun kebance, ni da ita (don in biya bukatata), sai ta amince. To, har sai da na kai gare ta don in biya bukatata din; (a wata ruwayar cewa aka yi) “yayin da na kai tsakankanin kafafunta,” sai ta ce, “Ka ji tsoron Allah, kada ka keta wannan hatimi, sai da hakkinsa (sai lokacin da aka halatta maka shi).”
Jin haka ya sa na yi gaggawar barin ta, na nesanta da ita, alhali ita ce mafi soyuwar mutane gare ni, kuma na bar mata dinarin da na ba ta. Ya Allah Ubangiji! Idan na aikata wannan al’amari da na aikata don neman yardarKa ne, Ka bude mana abin da muka kasance a cikinsa na toshewar kofar kogo da wannan dutse ya yi mana.” Sai kuwa dutse ya gusa (muskutawa ko matsawa) kadan, ta yadda duk da haka dai ba za su iya fitowa ba.”
Ina ganin bari mu kwana a nan, sai mako na gaba, in Allah Ya kai mu, sai mu dora. Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!