Darussa daga labarin rayuwar auren Kabir da Hafsat (2)

Assalamu alakum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban labarin da muka fara kawo muku makon da ya gabata:Ana cikin haka sai Hafsat ta fito dauke da wani faranti mai kunshe da kwanuka uku, ta ajiye a kan teburin da aka tanada don cin abinci, a zagaye da tebur din kujeru ne […]

Darussa daga labarin rayuwar auren Kabir da Hafsat (2)
Darussa daga labarin rayuwar auren Kabir da Hafsat (2)

Assalamu alakum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga ci gaban labarin da muka fara kawo muku makon da ya gabata:
Ana cikin haka sai Hafsat ta fito dauke da wani faranti mai kunshe da kwanuka uku, ta ajiye a kan teburin da aka tanada don cin abinci, a zagaye da tebur din kujeru ne guda hudu. Cikin sauri bayan ta ajiye sai ta nufi na’urar firij sannan ta rika fitowa da lemon gwangwani da na roba masu sanyi ta rika ajiyewa a kan teburin. Bayan ta ajiye ne kuma ta sake kwaso ’ya’yan itatuwa da suka hada da lemo da abarba da kankana da gwanda wadanda ta riga ta yanyanka su ta zuba a kan faranti ta ajiye. Daga nan muka nufi teburin don mu ci abinci, inda Kabir yake dauke da Khalid, Hafsat kuma ta rike hannun Humaira, haka na rika kallonsu cike da mamaki. Sai bayan mun isa teburin har ta bude kwanukan ne na gane tuwon shinkafa da miyar taushe ta girka, sannan a daya kwanon kuma farfesun kayan ciki ne. Yawun bakina ya tsinke na ji kamar na daka wasoso. Bayan ta zuba mana a cikin kananan farantin tangaran ne muka fara ba cikinmu hakkinsa.    
A gabana ta rika ba Kabir abinci har sai da ya koshi. Bayan mun gama cin abinci sai muka dawo kujerun falon muka zauna, a nan ne kuma na fara gabatar musu da tambayoyi don su cire mini jaki daga cikin duma.
Bayan na kalli Kabir da Hafsat ne suka fahimci akwai abin da nake so na tambaye su, sai suka tattara hankalinsu gare ni, hakan kuma ya sanya na fara magana: “A gaskiya na cika da mamaki ganin yadda rayuwarku ta sauya, bayan a baya kun kasa cire kitse daga wuta, ma’ana a baya kun kasance kamar doya da manja, inda wata rana na kira ku kamar Tom da Jerry. Mene ne ummul’aba’isin da ya sanya kuka daina sa-toka-sa-katsi?”
Kabir ya kalli Hafsat wadda a yanzu take murmushi. Bayan ya kalle ni ne sai ya fara magana: “Babban dalilin da ya sanya muka samu matsala tun farko shi ne, rashin fahimtar juna da kuma zargi. A baya daga zarar ban dawo aiki da wuri ba sai ta fara kananan maganganu, ta inda ta shiga ba tan a take fita ba,  a zatonta wai ina tare da wata ne. Na yi iya bakin kokarina don na fahimtar da ita ba haka ba ne amma ta gaza, hakan sai ya yi uwa da kaka wurin sanya haddasuwar matsalolin da muka yi fama da su a baya. Na rika kuntata mata a zuwan  tun da tana yi mini abin da ba na so to ita ma za ta ga abin da ba ta so, ai kuwa hakan sai ya zama kamar an kara wa wutar rikice-rikicen da muka yi fama da su fetur.” Ya yi shiru sannan ya kalle ta, a lokaci guda ya yi murmushi, bayan ta mayar masa da martani ne na tsaya ina kallonsu. A gefenmu kuma Khalid da Humaira suke wasa, inda ta boya a bayan kujera shi kuma ya bi ta don ya kamata. Hakan ya sanya muka yi murmushi.
Za mu ci gaba insha Allahu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno