Darussa daga littafin Gwaidayara na Taskar Tatsuniyoyi
Sunan Littafi: Gwaidayara (Da Wasu Labarai) Shekarar Wallafa: 2009 Kamfanin Wallafa: Gidan Dabino Publishers, Kano-Najeriya. Lambar Hakkin Mallaka: 978-37416-3-2 Yawan Shafuka: 67 Farashi: Ba a bayyana ba Tatsuniya […]
Sunan Littafi: Gwaidayara (Da Wasu Labarai)
Shekarar Wallafa: 2009
Kamfanin Wallafa: Gidan Dabino Publishers, Kano-Najeriya.
Lambar Hakkin Mallaka: 978-37416-3-2
Yawan Shafuka: 67
Farashi: Ba a bayyana ba
Tatsuniya na nufin dogo ko gajeren kirkirarren labari mai dauke da darussan rayuwa da ake labartawa ga al’umma, musamman yara da matasa, maza da mata da nufin ilimantarwa, fadakarwa da kuma nishadantarwa. A kasar Hausa, an yi ittifakin cewa dattijai sun shahara wajen amfani da tatsuniya wajen cusa tarbiyya da halayen kwarai da nishadantar da ’ya’yansu da jikoki tun can zamanin zamunna, inda kuma aka samu tabbacin cewa an fara rubuta tatsuniyoyin Hausa cikin ajami, bayan da Hausawa suka hadu da Larabawa da kuma haruffan Romawa, bayan zuwan Turawan Mulkin Mallaka nahiyar Afirka.
Gwaidayara shi ne littafi na 7 daga cikin jerin littattafai 14 da ke kunshe cikin Kundin Taskar Tatsuniyoyi da Dokta Bukar Usman OON ya tattara, ya rubuta.
“A cikin ’yan shekarun da suka shige ne na waiwayi wadannan tatsuniyoyi. Na je Biu musamman na yi bincike domin in samo mutanen da suka san irin wadannan tatsuniyoyi na da. Na yi haka ne domin ganin yadda yawancin yaran yanzu kan fara karatun boko tun suna ’yan shekara uku a duniya, kuma idan sun koma gidajensu sai wadansu su shiga kallon fina-finai a bidiyo da talabijin, ko su sa wakokim Makosa na mutanen kasar Kwango.” Abin da marubucin ya fada ke nan a shafi na di, kan dalilinsa na tattara tatsuniyoyin nan, inda hakan muhimmin abu ne na taskace al’adun gargajiya na Malam Bahaushe.
Gwaidayara na kunshe da babi-babi guda tara, wadanda suke dauke da tatsuniyoyi mabambanta guda tara da ke koya darussan rayuwa daban-daban, tare da nishadantarwa gami da adana al’adun Hausa.
Babi na Daya, daga shafi na 5 zuwa na 12, yana kunshe da tatsuniyar Gwaidayara, wacce ke ba da labarin wani magidanci mai mata hudu, wanda ya kasa yin adalci ga ’ya’yansa mata hudu, inda ya mayar da sauran ’ya’yansa uku ’yan lele, ’yan mowa, alhali ya nuna wa Gwaidayara wariya, ya mayar da ita ’yar bora. Daga karshe dai Allah Ya yi mata fatahi, ta auri Yarima dan Sarki, ta zama attajira wacce daga karshe ita ta zama sanadiyyar arziki ga iyayenta da sauran kishiyoyin mahaifiyarta da kuma su kansu ’yan uwan nata uku.
Akwai darussa masu yawa a cikin tatsuniyar Gwaidayara, wadanda suka hada da cewa babu kyau ga magidanci ya nuna wariya ga ’ya’yansa, kamar yadda mahaifin Gwaidayara ya yi. Tatsuniyar kuma na nuna muhimmancin ladabi da biyayya ga iyaye, cewa suna kawo wadata da arziki ga mai yin su. Dubi dai yadda ladabi da biyayya ga iyaye suka samar da arziki, wadata da farin ciki ga Gwaidayara – arzikin da ya yi bunkasa har ya shafi iyayenta da ’yan uwanta gaba daya.
Haka kuma, tatsuniyar na fassara karin mganar da ke cewa, ka ki naka duniya ta so shi, ka so naka duniya ta ki shi. Wannan darasin ya bayyana ne, yadda aka nuna wa Gwaidayara wariya, aka ki ta a gida, sai duniya ta so ta. A hannu daya kuma aka nuna wa ’yan uwanta uku kauna da soyayya a gida, sai duniya ta ki su. Wannan ya nuna mana cewa lallai ne iyaye su rika koya wa ’ya’yansu ladabi da biyayya, su horar da su ba tare da wariya ba, wanda haka zai sanya su zama masu aikata ayyukan kwarai a waje.
Akwai kuma darasin tauhidi a cikin wannan tatsuniya, cewa mutum ba shi ke ba da arziki ko farin ciki ga wani ba. Allah ne kadai Mai yin haka ga wanda Ya so kuma a lokacin da Ya so. Dubi dai yadda Ya azurta Gwaidayara, duk da cewa iyayenta ba su sonta kuma Ya kaskantar da ’yan uwanta, duk da cewa iyayenta suna nuna musu gata.
Haka kuma an samu wasu tsofaffin kalmomi da aka adana a wannan babi, wadanda suka hada da ‘Gomiya daya da biyar’ da ke nufin 15. Akwai kalmar ‘Gaskami’ wacce ke nufin kunun dorawa.
A Babi na Biyu daga shafi na 13 zuwa na 17, wanda ke dauke da tatsuniyar ’Yar’auta Da Kogin Rantsuwa, yana ba da labarin wasu iyali ne, inda cikin ’ya’yansu maza da mata su 9, ’yar autarsu ta yi rashin gaskiya, ta dauki kifin babansu ta cinye ba tare da izininsu ba. Wannan dalili ya sanya kogin rantsuwa ya cinye ta.
Wasu daga cikin darussan da tatsuniyar ke kunshe da su, sun hada da cewa abu ne mai kyau ga iyaye ko shugabanni su hukunta na kasa da su da suka aikata laifi, kamar dai yadda aka hukunta ’Yar’auta da ta aikata rashin gaskiya. Darasi na gaba shi ne, hukunta marar gaskiya na gyara mutum kuma hukuncin ba zai hana shi zama mutumin kirki ba a gaba, musamman idan ya gyara, kamar dai yadda hakan ya faru ga ’Yar’auta daga bisani. Wani darasin kuma shi ne, nuna muhimmancin yin bincike idan ana neman sanin gaskiya. Dubi yadda aka yi bincike har aka gano mai laifi cikin yara tara, wanda da ba don binciken da aka yi ba, zai yi wuya a gano mai laifin, wanda hakan kan iya sa wa a hukunta wani can daban.
Babi na Uku da ke cikin shafi na 19 zuwa na 26, yana kunshe ne da labarin Kurege da Biri. Labari ne da ke dauke da hikimomi da dabarun zaman duniya. An adana tsofaffin kalmomi a cikinsa, musamman ma sunayen dabbobin daji da na gida da tsuntsaye daban-daban da kuma irin halayensu, rayuwarsu da dangantakarsu. Irin wadannan kuwa sun hada da kurege da biri da kaza da kyanwa/muzuru da kare da kura da damisa. Sunan itacen kargo ma saninsa na da muhimmanci.
Wasu daga cikin darussan tatsuniyar sun hada da cewa mazambaci da maci amana ba za su kai ga nasara mai dorewa ba a rayuwa. Dubi yadda biri ya karkare rayuwarsa, musamman wajen neman aurensa, inda ya ha’inci kurege. Haka shi ma kurege ya wahala saboda yadda ya zambaci wasu domin cimma burinsa. Tatsuniyar kuma na nuna cewa, duk abin da mutum zai yi, to ya sanya hikima da basira da kwarewa wajen yin sa. Dubi irin hikimomin da kurege ya rika gabatarwa, a yayin da ya nufi cimma burinsa.
Babi na Hudu kuwa ya faro ne daga shafi na 27, ya karkare a shafi na 30 kuma yana dauke da tatsuniyar Kogi Mai Cinye Makaryata. Labarin wani mutum ne mai ’ya’ya 12, inda cikinsu daya ya cinye kadanyar babansa kuma ya yi karyar cewa ba shi ne ya cinye ba. Daga karshe dai ya hallaka, inda kogin da ke maganin makaryata ya cinye shi.
Babban darasin wannan tatsuniya dai na nuna illar yin karya da kuma illar yin munafunci, kamar yadda yake nuna muhimmancin gudanar da bincike idan ana neman gaskiyar wani al’amari.
Tatsuniya ta biyar kuwa mai taken Sarki Gizo da Kwarkwata, ta fito ne a Babi na Biyar, daga shafi na 31 zuwa na 37. Tana ba da labarin wani tsoho ne mai gona, wanda ya tausaya wa wata kwarkwata, inda ita kuma ta saka masa, ta rika yi masa gadin gonarsa. Wannan karimci da mai gona ya yi wa kwarkwata ya haifar masa da dinbin arziki da farin ciki a rayuwa.
Akwai sunayen kwari da halittu da ganyaye da aka adana a cikin wannan tatsuniya, wadanda suka hada da kwarkwata da kyankyaso da kiyashi da fara da kudan zuma da kunama da sari-kutuf da rina, da kwarkwasa da harawar wake. Haka kuma akwai darussa da ke bayyana cewa duk wanda ya tausaya wa wani, shi ma zai samu tausayi daga wani wurin, kamar yadda manomi ya tausaya wa kwarkwata, wanda haka ya sanya shi ma ya samu tausayi da arziki daga Sarki Gizo. Haka kuma akwai darasin da ke nuna muhimmancin yin adalci a kowane al’amari, musamman ma ga shugabanni. Haka akwai tsoratarwa dangane da yin zalunci, musamman idan muka yi la’akari da abin da ya yi ta samun fadawan sarki, har da shi kansa sarkin, lokacin da suka yi ta kokarin zaluntar mai gona, lokacin da suka nufi dibar harawar wakensa.
Babi na Shida kuwa ya faro ne daga shafi na 39 kuma ya kare a shafi na 46. Yana kunshe da tatsuniyar Talume, wacce ta yi ta hakilon neman biyan bukata daga abubuwa daban-daban har ta kai ga cimma muradunta. Akwai muhimman darussa da ke kunshe a wannan tatsuniya, wadanda suka hada da cewa zomo ba ya kamuwa daga zaune. Haka kuma yadda Talume ta yi ta biyan bukatun wasu kafin su biya mata tata bukatar, hakan na nuna cewa al’amrin duniya cude-ni-in-cude-ka ne. Irin kalubalen da ya samu Talume daga bisani yana nuna cewa wanda bai ji bari ba, zai ji hoho. Fuskantar wahala da kalubale ba su hana a karshe a samu sakamako mai kyau, hakan ta bayyana ga al’amarin Talume.
Tatsuniya ta 7 mai taken Ladi da Dodo kuwa ta fito ne a cikin Babi na 7, wanda ya fara daga shafi na 47 kuma ya karkare a shafi na 51. Tatsuniyar tana ba da labarin yadda ta kwashe ne a tsakanin kyakkyawar yarinya mai suna Ladi da kuma wani azzalumin dodo da ya nufi cutar da ita. Daga karshe dai Ladi ta samu agajin al’umma, aka cece ta kuma aka kashe dodon gaba daya.
Darussan da za a iya tsinkaya a wannan tatsuniya sun hada da cewa akwai sakamako ga wanda yake bijire wa umarnin iyaye. Wannan ya fito ne dangane da abin da ya samu Ladi, inda ta ki bin umarnin iyayenta, ta fita daji da kawayenta, duk da cewa iyayen nata sun ce kada ta tafi. Akwai kuma darasin da ke nuna muhimmancin zaman lumana da al’umma, wanda ke haifar da samun agaji idan wani akasi ya faru. Hakan ya bayyana, yadda al’umma suka taru suka tallafa wa Ladi ta tsira daga dodo saboda mutuncin iyayenta.
Tatsuniyar Darajar Neman Sani ta fito ne a Babi na 8 a littafin, wanda ya faro daga shafi na 53 zuwa shafi na 58. Labarin wadansu magidanta ne da suka dade da aure amma ba su samu haihuwa ba sai daga bisani. Bayan sun haifi yaronsu da suka rada wa suna Maishuni, sai suka tura shi neman ilimi. Ya kuwa samu karatu mai yawa, wanda kuma shi ya yi masa jagora ya zama hamshakin attajiri.
A takaice dai wannan tatsuniya tana ishara ce kan muhimmancin ilimi a rayuwa, musamman da yake ilimi shi ne gishirin rayuwa, wanda yake gadar wa mutum kowane irin arziki a rayuwa. Hakan ta tabbata ga yadda rayuwar Maishuni ta kasance.
Babi na Tara kuma na karshe a littafin yana dauke ne da tatsuniyar Dan Buwaila da Bangorinsa. Babin ya faro ne daga shafi na 59 kuma ya karkare a shafi na 67. Labarin wata mata ce mai ’ya’ya biyu, mace da namiji, inda aka ci garinsu da yaki. Matar sai ta dauki diyarta mace suka tsira daga mahara, ta bar namijin mai suna Dan Buwaila, wanda shi kuma ya samu taimakon wata itaciya har ya shahara kuma ya zama mai taimakon mahaifiyarsa da ’yar uwarsa.
Darussan da tatsuniyar ke nunawa sun hada da cewa bai kamata iyaye su nuna wariyar jinsi ba tsakanin ’ya’yansu. Akwai darasin da ke fassara karin maganar da ke cewa hassada ga mai rabo taki ce. Wannan ya wanzu ne yadda mutane suka yi ta nuna wa Dan Buwaila hassada da kyashi amma duk da haka ba su hana shi samun arziki mai yawa ba. Haka kuma akwai darasin da ke nuna muhimmancin jajircewa wajen gwagwarmayar neman halal, kamar dai yadda Dan Buwaila ya rika yi har ya samu kyakkyawar makoma a rayuwa.
Babu shakka littafin Gwaidayara ya kayatar sosai, musamman ma yadda aka yi masa dab’i mai inganci, sannan aka inganta shafukansa da zanen hotuna masu jan hankali ga mai karatu.
Marubuci Dokta Bukar Usman ya yi matukar kokari kuma ya cancanci yabo na musamman dangane da wannan aiki da ma wasu da dama da ya gabatar.