Darussa na hakika daga tabargazar Stella Oduah
Shi ke nan, haka za mu kare, kullum mu rika yin ihu bayan hari? Ga shi a yau muna kuka da wata ’yar siyasa, wacce a can baya ba a san ta ba a siyasance amma kawai saboda ta bayar da gudunmowa ga zaben Shugaba Goodluck a 2011, shi ke nan muna ji muna gani […]
Shi ke nan, haka za mu kare, kullum mu rika yin ihu bayan hari? Ga shi a yau muna kuka da wata ’yar siyasa, wacce a can baya ba a san ta ba a siyasance amma kawai saboda ta bayar da gudunmowa ga zaben Shugaba Goodluck a 2011, shi ke nan muna ji muna gani aka damka mata muhimmiyar ma’aikatar sufurin jiragen sama, ba mu ce komai ba, sai yanzu da ta tafka tabargaza.
Kamar yadda jita-jita ta cika ko’ina, an ce idan ka debe PDP, wacce ta kware wajen satar kuri’u, ka debe Hukumar Zabe ta kasa, ka debe jami’an tsaro, babu wacce ta taimaka wa Goodluck ya samu kujerarsa kamar Stella Oduah, wacce ta yi amfani da kungiyarta ta Neighbour2Neighbour ta yi gamgamin neman zaben nasa. Dalili ke nan fa aka saka mata da wannan mukami. Mun san da haka kuma muka kyale. Shin muna zaton kudin da ta zuba ba jari ba ne? Ya zama dole ne ta ci riba kuma ribar ce take ci a yayin da ta shirya tabargazar sayen motocin sulke biyu, kan Naira miliyan 225. Ya zama wajibi mu binciki wannan badakala, sannan mu koyi darussa na hakika daga gare ta, don nan gaba.
Muna sane da yadda shugabanni a kasar nan suke jajircewa su zuba dukiyarsu, su sanya karfinsu su bayar da goyon baya ga dan takara ko jam’iyyarsa, ba don komai ba sai domin amfanin da za su samar wa kansu. Amma duk da cewa muna gani kuma muka amince masu amma sai mu rika tsammanin wai ba za su ci amana ba, mu yi zaton za su yi wa kasa aiki, za su bi doka wajen tafiyar da al’amura. Ya kamata mu sake tunani, mu dauki misalin Stella Oduah, domin kauce wa faruwar haka.
Game da wannan batu na bahallatsar Naira miliyan 225, mun ji cewa fadar Shugaban kasa da Majalisun kasa sun yi alkawarin bicikar komai. To, amma muna zaton za su iya tsinana wani abu, koda kuwa an gano cewa lallai Ministar ta tafka barna da dukiyar al’umma? Shin barci muke yi a yayin da irin wadannan tabargaza da dukiyar al’umma take ta faruwa tun zamanin Obasanjo, har zuwa yau din nan?
Mun taba tsayawa ma mun tambayi kawunanmu cewa, ministoci nawa ne suke aikata irin wannan tabargaza? Shin ma’aikatu nawa ne a kasar nan suke zuba kudaden da ma’aikatunsu ke samarwa a matsayin kudin shiga ga kasa, balle ma a ce za a kididdige su? Ba zan yi mamaki ba, duk da wannan ihun da muke yi, idan aka kasa cimma wani abu mai kima daga wannan tabargaza da ake zargin minista Oduah da aikatawa.
Wani abin takaici ma shi ne, yadda Oduah ta raina hankalin ’yan Najeriya, inda take mayar da martani da kakkausar murya, a lokacin da ’yan kasa ke kuka da rashin ingancin harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya. A game da yawan hatsarin da ake samu a bangaren jiragen kuwa, maimakon ta bi kadi da diddigin yadda za a samu maslaha, sai ma ta bayyana cewa ‘ai hadari daga Allah yake kuma ba mai iya hana afkuwarsa.’
Mun yarda cewa komai aikin Allah ne amma dai ya zama wajibi duk wanda aka ba aiki, ya yi iyaka kokarinsa, sannan idan abu ya faru, sai a danganta shi ga Allah. Yanzu me za mu dauki mutumin da ya je hanyar jirgin kasa ya tsaya, jirgi ya zo ya dandake shi? Sai mu ce Allah ne Ya kashe shi?
Wani darasi da ya kamata Oduah da irinta su koya shi ne, su sani fa cewa sun amshi mukaman nasu ne da nufin su yi wa al’umma hidima. Don haka al’umma na bukatar a yi masu hidima cikin kana’a. Idan suna bukatar wani bayani kuma, dole ne a yi masu shi cikin tawali’u kuma da azanci.
Ba tabargazar sayen motoci kawai minista Oduah ta tafka ba, akwai batun hana amfani da filin saukar jiragen sama na Malam Aminu da ke Kano, inda ta haramta wa kafanonin sufuri na Emirates da Ethiopia da na katar su yi amfani da filin, ta shaida masu cewa wai sai dai su rika sauka a Inugu. Shin ba ta san cewa tun 1934 aka kafa wannan fili ba kuma yake harkokinsa? Sai yanzu ne za a dakile masa himma, saboda me? Ko dai wani sabon makirci ne ake kara shirya wa Arewa? Allah Ya sa shi ma Jonathan ba zai amince da haka ba, a ce za a kukumce tattalin arzikin Arewa. Allah Ya sa wannan aikin Oduah ne ita kadai, bai da hannu a ciki. Idan ba haka ba, yaya za a ce duk Arewa babu inda jirgi zai tashi zuwa wata kasa, sai dai Abuja kadai?
Lallai kam wannan ma wani darasi ne da ya kamata mu koya daga tabargazar minista Oduah kuma ya kamata ya ankarar da mu domin mu tashi tsaye domin taka wa duk wani jami’in gwamnati da ya nufi ruguza mana rayuwa burki.