Darussan da ke cikin azumin watan Ramadan (1)
Bayan mun nazarci ayoyin da suka yi magana kan azumin watan Ramadan yana da kyau mu nazarci wasu darussa da za mu iya dauka daga azumin watan Ramadan. Wannan domin mu dada fahimtar hikimar da ke cikin wannan wata mai daraja ne.Daga cikin darussan da za mu iya dauka a cikin azumin watan Ramadan akwai:1.Ramadan […]
Bayan mun nazarci ayoyin da suka yi magana kan azumin watan Ramadan yana da kyau mu nazarci wasu darussa da za mu iya dauka daga azumin watan Ramadan. Wannan domin mu dada fahimtar hikimar da ke cikin wannan wata mai daraja ne.
Daga cikin darussan da za mu iya dauka a cikin azumin watan Ramadan akwai:
1.Ramadan watan hakuri ne:
Assabru, wanda ke nufin hakuri da Hausa, shi ne kamewa. Arragib ya ce: “Hakuri shi ne kamewa a lokacin tsanani.” Kuma ya ce: “Ana kiran azumi da hakuri saboda kasancewarsa kamar nau’insa ne.” (Almufradat, shafi na 474). Dalili Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ku nemi taimako da yin hakuri, da Sallah:…” (k:2:45). Ibnu Jarir ya ce: “An ce ma’anar hakuri a nan na nufin azumi ne. Domin azumi wata ma’ana ce daga cikin ma’anonin hakuri a wurinmu.” (Tafsirin dabari, Mujalladi na 1 shafi na 259).
Ramadan da hakuri:
An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Watan hakuri da kwanaki uku a kowane wata azumin shekara ne.” Nisa’i ya ruwaito. Suyudi ya ce: “Watan hakuri shi ne watan Ramadan. Asalin hakuri kamewa ne, sai aka kira azumi da hakuri saboda abin da ke cikinsa na kame rai daga ci da sha da aure. (jima’i). (Sharhin Sunnanu Nisa’i).
Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce ga wanda ya zo yana neman ya rika azumi kullum cewa: “Ka azumci watan hakuri da akalla rana daya a kowane wata….” Abu Dawuda da Ibnu Majah suka ruwaito.
Ramadan makarantar koyon hakuri ne:
Don haka Ramadan makarantar koyon hakuri ne kamar yadda Ibnu Rajab Al-Hambaliy ya ce: “Mafi falalar nau’o’in hakuri shi ne azumi. Domin ya tara hakuri kan abubuwa uku; shi hakuri ne wajen yin da’a ga Allah Madaukaki da hakuri wajen barin sabon Allah. Saboda bawa yakan bar sha’awoyinsa saboda Allah alhali ransa yana jayayya da shi kan haka. Don haka ne Hadisi ingantacce ya zo cewa lallai Allah Madaukaki Yana cewa: “Kowane aiki na dan Adam nasa ne ban da azumi. Shi kam nawa ne, Ni zan saka a kai. Domin ya bar sha’awarsa da abincinsa da abin shansa saboda Ni.” Buhari da Muslim suka ruwaito. Kuma a cikinsa har wa yau akwai hakuri kan kaddara mai wahala da za su iya shafar mai azumi na daga yunwa da kishin ruwa. Manzon Allah (SAW) ya kasance yana kiran watan azumi watan hakuri.” (Jami’ul Ulumi wal Hikami, Mujalladi na 1 shafi na 26).