Darussan da ke cikin azumin watan Ramadan (2)

Nau’o’in hakuri: Ibnu kayyim ya ce: “Hakuri bisa lura da abin da yake da alaka da shi ya kasu kashi uku: hakuri a kan bin umarnin Allah da ayyukan da’a har sai an aikata su. Da hakuri daga abubuwan da aka hana da sabo har a tabbatar ba a auka musu ba. Da hakuri kan […]

Darussan da ke cikin azumin watan Ramadan (2)
Darussan da ke cikin azumin watan Ramadan (2)

Nau’o’in hakuri:

Ibnu kayyim ya ce: “Hakuri bisa lura da abin da yake da alaka da shi ya kasu kashi uku: hakuri a kan bin umarnin Allah da ayyukan da’a har sai an aikata su. Da hakuri daga abubuwan da aka hana da sabo har a tabbatar ba a auka musu ba. Da hakuri kan kaddarori da abin da aka hukunta wa mutum har ya zamo bai fusata Allah a kansu ba.” (Mudarijus Salikina, Mujalladi na 2 shafi na 165).
2. Ramadan watan kyauta da kyautatawa da da’a da sadar da zumunta ne:
An karbo daga Ibnu Abbas (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance mafi kyauta a tsakanin mutane, amma ya fi yawaita kyauta a watan Ramadan lokacin da Jibrilu yake ganawa da shi, kuma yana ganawa da shi ne a kowane dare na Ramadan yana yi masa darasun Alkur’ani. Manzon Allah (SAW) ya fi iskar sarfa yawan alheri.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Ibnu Hajrin ya ce: “A cikinsa (Hadisin) akwai nuni cewa yawan darasu (karanta) Alkur’ani yana sabunta alkawari da karuwar wadatar zucci, kuma wadatar zucci sababi ce na yin kyauta. Kuma kyauta a shari’a, shi ne bayar da abin da ya dace ga wanda ya dace, ita ta fi sadaka. Har wa yau Ramadan lokacin bikin alherai ne, domin ni’imar Allah a kan bayinSa a cikinsa tana karuwa fiye da waninsa. Don haka Manzon Allah (SAW) ya kasance yana tasirantuwa da bibiyar Sunnar Allah a cikin bayinSa. Duk abubuwan da aka ambata na lokaci da abin da ake saukar da shi da mai saukarwa da muzakkira, suna kara yin kyauta da ilimi a wurin Allah.” (Fathul Bari, Mujalladi  na 1 shafi na 31).

Wuraren da ake yin kyauta da kyautatawa da aikin da’a da sadar da zumunta.
a). Ba mai azumi abin buda baki.
An karbo daga Zaidu Bin Khalid Aljuhanni (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wanda ya ba mai azumi abincin buda baki, zai samu lada kamar ladarsa ba tare da an rage komai daga ladan mai azumin ba.” Tirmizi da Ibn Majah da Darimi suka ruwaito.
b). Kyautata wa iyaye da sadar da zumunta:
An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Wani mutum ya zo wurin Manzon Allah (SAW) ya ce: “Wane mutum ne ya fi hakki a kaina wajen kyautata zamana da shi? Sai (SAW) ya ce: “Mahaifiyarka.” Ya ce, “Sai kuma wa?” Ya ce: “Mahaifiyarka.” Ya ce: “Sai kuma wa?” Ya ce: “Mahaifiyarka.” Ya ce: “Sai kuma wa?” Sai ya ce: “Sannan mahaifinka.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
An kabo daga Anas Bin Malik ya ce: “Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Wanda yake son ya ji dadi Allah Ya yalwata masa arziki, ko a jinkirta masa ajalinsa (ma’ana a sanya masa albarka), to ya sadar da zumuntarsa.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
Adda’u ya ce: “In kashe dirhami a tsakanin zumuntana ya fi min dadi da in ciyar da Dirhami dubu ga wasu daban.” Sai wani ya ce: “Ya Baban Muhammad! Koda zumuntana sun kai ni wadata?” Ya ce: “Koda sun kasance sun fi ka wadata.” (Makarimul Akhlak na Ibnu Abud Duniya, shafi na 62).
c). Sadaka da ciyarwa da sauran ayyukan alheri:
An karbo daga Abu Huraira (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Kowane sulhu ga mutane sadaka ne, duk wunin da rana ta fito in ka daidata tsakanin mutum biyu sadaka ne, kuma ka taimaki mutum a kan dabbarsa ka dora shi a kanta ko ka sauke masa kayansa sadaka ne. Kalma mai kyau sadaka ce, kuma kowane taki zuwa Sallah sadaka ne, kuma kawar da abin cutarwa daga hanya sadaka ne.” Buhari da Muslim suka ruwaito.
3. Ramadan watan jihadi da samun nasarori da budi:

Yakin Badar Babba:
Allah Madaukaki Ya ce: “Idan kun kasance kun yi imani da abin da Muka saukar a kan bawanMu a Ranar Rarrabewa, a Ranar da jama’a biyu suka hadu….” (k:8:41).
Urwata Bin Zubair ya ce kan fadinSa: “Ranar da jama’a biyu suka hadu” cewa “Ranar da Allah Ya rarrabe tsakanin karya da gaskiya, ita ce Ranar Badar. Ita ce ranar da Annabi (SAW) ya fara halartar yaki da kansa. Shugaban mushrikai ya kasance Utbatu Bin Rabi’ata, sai suka hadu ranar Juma’a goma sha tara ga watan Ramadan, kuma sahabban Manzon Allah (SAW) mazaje su dari uku da doriya, sai Allah Ya karya mushirikai a ranar, aka kashe fiye da mutum70 a cikinsu, aka kama wasu.” (dabari ya ruwaito a tafsirinsa, Mujalladi na 10 shafi na 9, kuma ana iya duba bayanin Hadisin kan yakin a cikin Siratu Ibnu Hisham, Mujalladi na 2 shafi na 606-633).

Bude Makkah:
An karbo daga Ibnu Abbas (RA) cewa Annabi (SAW) ya fita daga Madina a cikin Ramadan tare da mutum dubu goma, wannan a shekara ta takwas da rabi ne na isowarsa Madin, sai shi da wadanda suke tare da shi na daga Musulmi suka wuce zuwa Makkah, yana azumi suna azumi har ya isa Kadidu-wani ruwa ne a tsakanin Ashfan da Fudaida-sai ya sha ruwa su ma suka sha ruwa.” Buhari ya ruwaito.
Kuma daga gare shi cewa “Lallai Annabi (SAW), ya yi yakin Fathu (Bude Makkah) a cikin Ramadan ne” Buhari.
Bayan wannan Musulmi sun fafata yakin Aina Jalut da Tattar a karkashin Holaku Al-Maguli a ranar Juma’a 25 ga watan Ramadan suka samu nasara a kan Tattar. Albidaya wan Nihaya Mujalladin na 17 shafi na 403.
Kuma sun buga ranar Asabar ta farkon Ramadan ta shekara ta 702 Bayan Hijira a yakin da ake kira yakin Shakhab da Tattar yakin da aka ce Ibnu Taimiyya ya halarta kuma suka samu galaba. A duba Albidaya wan Nihaya na Ibnu Kasir Mujalladi na 18 shafi na 28 don ganin bayani kan yakin.
4. Ramadan watan Alkur’ani da tsayuwa:
Allah Madaukaki Ya ce: “Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa, yana shiriya ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa.”  (k:2:185).
Daga Ibnu Abbas ya ce: “An saukar da Alkur’ani a jumlatance a daren Lailatul kadar a cikin Ramadan zuwa saman duniya. Sai ya kasance idan Allah Yana nufin saukar da wani abu daga cikinsa ga duniya, sai Ya saukar har sai da ya kammala saukar da shi.” Buhari ya ruwaito.
Kuma daga gare shi (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance mafi kyautar mutane, amma ya fi yawaita kyauta a Ramadan lokacin da Jibrilu yake ganawa da shi, kuma yana ganawa da shi ne a kowane dare na Ramadan yana yi masa darasun Alkur’ani. Manzon Allah (SAW) ya fi iskar sarfa yawan alheri.” Buhari da Muslim suka ruwaito. Wannan ruwayar Buhari ce.
Annawawi ya ce: “Daga cikin hukuncin da za a iya fitarwa daga Hadisin akwai: Mustahabbancin yawan darasun (karanta) Alkur’ani a wannan wata mai albarka. Sharhin Muslim
Ibnu Hajrin kuma ya ce: “A cikin fa’idojin da Hadisin ya kunsa akwai: girmama Ramadan, saboda kebance shi da fara saukar da Alkur’ani a cikinsa….” (Fathul Bari, Mujalladi na 9 shafi na 45).