Darussan da ke cikin watan azumin Ramadan 1
Ranar Asabar da ta gabata ne al’ummar Musulmi suka fara azumin watan Ramadan. Hakan na zuwa ne bayan sanarwar ganin jaririn watan a garin Birnin Kebbi da Gwandu a jihar Kebbi ranar Juma’ar da ta gabata. A lokacin da yake jawabi ga manema labarai a madadin Sarkin Musulmi, Shugaban Kwamitin Ganin Watan Farfesa Sambo Waliy […]
Ranar Asabar da ta gabata ne al’ummar Musulmi suka fara azumin watan Ramadan. Hakan na zuwa ne bayan sanarwar ganin jaririn watan a garin Birnin Kebbi da Gwandu a jihar Kebbi ranar Juma’ar da ta gabata. A lokacin da yake jawabi ga manema labarai a madadin Sarkin Musulmi, Shugaban Kwamitin Ganin Watan Farfesa Sambo Waliy Junaidu ya bayyana cewa ranar ce ta zo daidai da 1 ga watan Ramadan na skekarar 1435 BH.
Azumtar watan na tara, na Kalandar Musulunci wajibi ne kuma daya ne cikin rukunnan Musulunci biyar. A lokacin azumin da yake farawa daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana, ana bukatar a kaurace wa ci da sha da kuma duk wani abu da ya jibanci jima’i a kowacce rana har zuwa karshen watan. Azumtar watan ya samo toshe ne daga wata aya cikin al-kur’ani Mai Girma wato k:2:183 inda Allah (SWT) ke cewa: “Ya ku wadanda suka yi imani! An wajabta azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke daga gabaninku, tsammaninku, za ku yi takawa, ”. Ana so Musulmi su sadaukar da lokacinsu wajen gudanar da ibada tukuru a baki dayan watan.
Bayan daurace wa ci da sha da sauransu da aka bukaci mai azumi ya yi, ana kuma bukatarsa ya kasance mai hakuri da haba-haba da taimako da kuma ayyukan alheri ga jama’a musamman ma ga marasa hali. An kwadaitar da masu azumi alfanun ba da sadaka da ciyyarwar musamman ta hanyar gayyatar sauran mabiya addinai don yin bude baki tare da su. Gudanar da irin wadannan ayyukan alherin a watan Ramadan na da matukar tasiri wajen wanzar da fahimtar juna da hadin kai musamman la’akari da yanayin da kasar nan ke ciki.
Azumi ya kamata ya sa wa mai yin sa hakuri da juriya da dangana saboda yadda wanda ke yinsa yake jure wa yunwa da kishirwa. Wanda ka iya sa ya shi ya tuna da cewa akwai dimbin jama’a da ke rayuwa a haka a fadin duniya. Muhimmancin watan wanda ya banbanta da sauran watannin Kalandar Musulunci shi ne bukatar saukaka al’amura bangaren yadda ake ci da sha da kuma yadda ake tafiyar da rayuwa. Yana kuma koyar da tattali da hani kan yin albazaranci . Musulmi a Najeriya ba tare da la’akari da shugabanni ne su ko mabiya ba, ya dace su yi amfani da wannan watan don guje wa cin-hanci da karbar rashawa da suka yi wa kasar nan daurin dabaibayi kuma hakan zame mata shamaki a fatanta na zama kasa mai dogaro da kanta da aniyyar shiga jerin kasashen da suka ci gaba.
Dalili da wannan matsalolin rashin tsaron da Najeriya ke fuskanta wadanda ba a taba gani ba a tarihinta, ya dace Musulmi da sauran mabiya addinai daban-daban su nuna hikima da kuma hakuri da juna. Ga malamai da suke aikin gabatar da Tafsirin al-kur’ani Mai Girma, ya kamata su san cewa su jagorori ne kuma masu saitawa da tankwarawa ra’ayoyin al’umma tare da la’akari da yanayin da kasar ke ciki. Yakamata malamai su guje wa fadin kalaman batanci ko na tunzura jama’a a lokacin Tafsiransu. Zai dace a ce sun yi amfani da watan wajen ilmantar da mabiya kan hanyoyin da za su iya bayyana kokensu ba tare da tada zaune tsaye ba. Ya kamata kuma su ja hankalin wadanda suke ganin an masu ba daidai ba, da su karbi bukatar sulhu da gwamnati, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya yi sulhu da Hudaybiyyah.
Lokacin watan Ramadan ba lokaci ba ne na cin kazamiyyar riba. Ba wata ne da ’yan kasuwa za su yi rige-rigen kara farashin kayayyakin masarufi da aka fi matukar bukata a lokacin azumi ba.
Muna wa daukacin al’ummar Musulmi fatan kasancewa lafiya a wannan watan na Ramadan.