Darussan da muka koya a Sallar Layya ta bana

A daidai lokacin da kake karanta wannan rubutu, Babbar Sallah ta wuce. Yin sharhi kan yadda rinjayen Musulmi suka yi wannan Sallah yana da muhimmanci, domin zai ba da damar nazarin walwala da jin dadin jama’a a lokacin Sallar. Muhimman abubuwa biyu zan duba a lokacin Sallar:  Na farko shi ne, tsaro, na biyu walwala […]

Darussan da muka koya a Sallar Layya ta bana
Darussan da muka koya a Sallar Layya ta bana

A daidai lokacin da kake karanta wannan rubutu, Babbar Sallah ta wuce. Yin sharhi kan yadda rinjayen Musulmi suka yi wannan Sallah yana da muhimmanci, domin zai ba da damar nazarin walwala da jin dadin jama’a a lokacin Sallar.

Muhimman abubuwa biyu zan duba a lokacin Sallar:  Na farko shi ne, tsaro, na biyu walwala da jin dadin jama’a. A inda na yi tawa Sallar, wato tsakanin Katsina da Kano, zan iya cewa ta fannin tsaro, an samu gagarumin ci gaba. 

Fadace-fadacen ’yan banga da muka saba gani lokuttan Sallah, sun yi sauki. Abu na biyu, fashi da makami a kan hanyoyi da kan kazanta lokutan Sallah, su ma da sauki a wannan shekara. Masu kwacen waya da jakkunan ’yan mata (tunda da ma ’yan mata aka sani da al’adar rataye jaka) su ma ban ji abin ya kazanta ba. Gari kamar Kano, inda ake siyasar gaba da ta’addanci, wannan karon sun yi hawan daushe lafiya ba tare da yankar abokan hamayyar siyasa ba.Wannan ke nan.

Abu daya ya kawo wa Sallar bana cikas. Ba komai ba ne wannan shi ne bakin talauci da fatara da dimbin mutane ke fama da shi a Najeriya. 

Na farko an gudanar da wannan Sallah, a lokacin da ake tsakiyar damina, mafi-yawan albarkatun gona ba su kai ga nuna ba.A jihohin Arewa maso Yamma, kamar Arewacin Katsina, babu abin da manomi zai iya dauka ya sayar domin gudanar da bikin Sallar, sai dai in kansa zai saida. Mu dai nan har yanzu ba mu fara girbi ba, kuma koda mun girbe gero, to ai gero abinci ne ba kayan da za a dauka a kai kasuwa ba ne kamar nomi da zoborodo ko gyada wadanda su ne kayayyakin gona da a kan shuka domin a samun kudi a nan Arewacin Katsina inda na fi wayo.

Abu na biyu da koyaushe ke rage armashin bikin Sallah, shi ne, rashin albashin ma’aikatan gwamnati. Allah Ya albarkace mu da shugabanni wadanda ba su kaunar ma’aikata ko kadan. Da muna da adalan shugabanni masu hangen nesa, to da bai kamata a ce za a gudanar da Sallar Layya 21 ga watan albashi ba, amma a  ce, akwai ma’aikacin da bai samu albashi ba. Idan sun san ya kamata, to za su iya fara albashin tun 17 ga watan Agusta, kuma su kammala shi 20 ga watan.  

Wadannan shugabannin suna kallon ma’aikata a matsayin wani nauyi wanda in da akwai yadda za su yi, to da sun sauke shi baki daya. Wannan fa na faruwa a lokacin da duk da arzikin da Allah Ya hore mana, amma ya zama na banza, tun da kananan kasashe da ba su kai mu arziki ba, sun fi ma’aikatanmu watayawa da sakewa. A ra’ayina ina amfanin badi ba rai? Ina amfanin arzikin da wadansu ’yan kalilan din mutane ke morewa?  (Shugaban kasa, gwamnoni, ministoci, ’yan Majalisar Tarayya da na jihohi da masu ba su shawara). Abin da Minista ke amsa a wata ya ninka sau goma abin da ma’aikacin da ya shafe shekara 20 yana aiki ke amsa a wata. Wannan shi ne adalcin da ake ta farfaganda a kansa? Akwai gwamnonin da har fadi suke cewa, wai ai ba ma’aikata ba ne kawai a Najeriya. Wannan mai ilimi da gogewar duniya ke irin wannan magana.Amma, in ka ce yana da karancin ilimi sai ya ce ka muzanta shi, bayan mai ilimi shi ya kamata ya san muhimmancin malaman makaranta da malaman asibiti da alkalai da lauyoyi da akantoci da akawu da sauran rukunnan kwararru wadanda su ne injin ci gaban kowace irin al’umma. 

Babu wata al’umma a duniya da za ta ci gaba ba tare da ma’aikatan gwamnati ba. Su ne kwararru, su ne ke tsara manufofin tattalin arziki, kuma su ne masu aiwatar da shi. Su ne kwakwalwa da tunanin gwamnati, kuma su ne wani ke cewa ba su da amfani! Saboda lalacewa da cin hanci, gwamnatoci sun gwammace su je su dauko kwanzalta na haya masu zaman kansu. Wai wanda ke da kwararru, amma saboda wata boyayyiyar manufa, sai ya ketare ya dauko hayar odita, hayar injiniya, hayar safiyo, wadannan mutane duk akwai su a gwamnati, sakaci da ragwanci ya sa ba a amfani da su. Don haka su ma yanzu sun zama ’yan dumama benci.

Ba ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ba ne kawai ke ba su samu albashi ba. A cikin jihohi 36 da ke Najeriya, kadan ne suka iya biyan albashin ma’aikatansu. Cikin wadanda suka iya biya ma, akwai wadanda aka yi wa je-ka-ka-mutu, wato sai daren Sallar da La’asar sannan suka samu karaurawar  banki cewa albashin ya shiga. Fitar da kudin a wannan lokaci wani daga ne, don haka wadanda ba za su iya dambe a layin ATM ba, dole suka yi hakuri sai bayan Sallah. Wannan shi ne, an yi ba a yi ba, an ba karuwa gadin kwarto.

Wayyo ’yan fansho! ’Yan fansho bayin Allah. Allah kadai ke son ku ’yan fansho. Duk wani ma’aikacin gwamnati ko na  kamfanoni masu ci da kansu, karshen sa zai zama dan fansho. A lokacin karfi ya kare, kai furfura ta cika shi, gani ya ragu,tunani da kaifin hankali sun ragu, hannu na makyarkyata ko sa hannu ma sai dansa  ko dan uwansa ya yi masa. A wannan lokaci ya kamata a ce ana taimaka musu amma ban da karkashin mulkin Jari-Hujja irin na kasarmu Najeriya. A wannan lokaci, azzaluman shugabanni na kallo dan fansho a matsayin jalli-joga. Wadansu ma ba su da kudin sata sai na ’yan fansho. Daga 1999 zuwa yau, ’yan fanshon Najeriya sun ci ukuba, sun ga tashin hankali da azaba iri-iri. Wadansu sun mutu kan hanya, wadansu mota ta ture wajen kwaramniyyar karbo hakkinsu na shekara 35, wadansu sun mutu a karkashin gada da sunan neman guminsu. Har yanzu dai rayuwar dan fansho ta ki inganta, sai bijiro da manufofin keta iri-iri ake da suke kara jefa dan fansho cikin mawuyacin hali. A wannan Sallar ma, ba ta sauya zane ga wadansu ’yan fansho ba, domin cikin kunci da bacin rai suka yi bikin Sallah. Wadata ke sa a yi Layya, ibada mai dimbin lada, amma bana raguna sun yi kwantai, saboda ba a iya saye. Wdanasu sun share shekara guda suna tirke rago, amma sai dai asara suka tafka. Su ma ta nan, abincinsu ya nakasa. 

Akwai uwa uba, inda ba a yi ko tuwon Sallah ba. Muna ga tarin almajirai ko’ina a tituna ranar Sallah suna bara, a taimake su, su ci abinci kada yunwa ta kashe su. Alhamdulillahi, ko ba albashi, ko ba Layya, ko ba sabon dinki, da yawa sun yi bikin cikin koshin lafiya, kodayake ba za a rasa ’yar maleriya ta al’ada, wata olsa da ta zama jiki da sauransu ba. Allah Ya kyauta, Ya yi mana katangar karfe da kaskanci da wulakanci da talaucin duniya da Lahira amin. 

Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, Babban Sakataren kungiyar Myryar Talaka ta kasa

 08165270879