Darussan da na koya yayin aikin fim a kasar Sin – Saima Muhammad

Saima Muhammad na daya daga cikin ‘yan Najeriya da suka halarci kasar Sin aikin dora murya a fina-finan kasar guda hudu, ta bayyana yadda suka gudanar da aikin da kuma darussan da ta koya.  Ta ce ta kasance daya daga cikin wadanda suka yi aikin ne wata rana ta je harkokinta Cibiyar Al’adun Gargajiya ta […]

Darussan da na koya yayin aikin fim a kasar Sin – Saima Muhammad

Saima tare da Malama Maryam a dakin daukar muryaSaima Muhammad na daya daga cikin ‘yan Najeriya da suka halarci kasar Sin aikin dora murya a fina-finan kasar guda hudu, ta bayyana yadda suka gudanar da aikin da kuma darussan da ta koya. 

Ta ce ta kasance daya daga cikin wadanda suka yi aikin ne wata rana ta je harkokinta Cibiyar Al’adun Gargajiya ta U.K Bello, sai ta tarar da taron mutanen da akasarinsu ‘yan kungiyar fim din Arewa Film Makers Association reshen Jihar Neja ne. “A nan na lura da gwaji ne ake yi musu da harshen Hausa. Na kasa hakuri na samu wasu daga cikin mutanen ko ina iya shiga a gwada ni? Sai jagoran ya tambaye ni ko na iya Hausa? Na ce masa ina kokari gwargwadon hali. Sannan ya tambaye ni idan an bukaci in je wurin shirya fim zan je? Na ce masa, eh idan har Allah Ya nufa kuma iyayena suka amince. Nan take ya ce in je in nemi Malam Labaran S.K. Bayan na same shi ya yi mini tambayoyi, ya kuma amince a gwada ni. Daga nan suka ba ni wata takarda mai dauke da rubutun kasar Sin tare da fassarar Hausa. Aka nemi in karanta, da na yi nazari a hankali sai na lura da cewar akwai matsala, sai an gyara Hausar. Suka nemi in gyara in karanta. Na gyara na kuma karanta. Bayan na gama sai suka dauki muryata da kuma hotona don a hada a tura musu can kasar Sin. Kammala wannan gwajin ke da wuya, aka nemi in fara shirin tafiya. Na shaida wa iyayena kuma suka amince tare da yi mini addu’ar samun sa’a. Haka muka ci gaba da shirye-shirye har ranar tafiya ta zo inda muka shiga jirgin Egypt Air inda muka yada zango a kasar Masar, daga nan kuma sai kasar Sin.” Inji ta.
Ta ce, su shida ne suka yi wannan tafiyar. Akwai Isah Sa’idu Bwada da Muhammad Yahaya da Muhammad danladi da ita daga Jihar Neja. Sai Fati kasim da Maryam Baba Lawan jarumar fim din Hausa daga Jihar Kano, sai Nasiru Sani daga Jihar Filato.
Bayan sun isa ko an ba su horo ne game da aikin da za suka yi? Sai ta ce: “Babu wani horon da aka ba mu, domin an tura musu muryoyinmu da hotunanmu da aka dauka tun daga gida, don haka sun dauka muna da kwarewar da ta kamata. Mun isa Sin ranar wata Lahadi; ranar Litinin muka hadu a ofis aka jibge mana manyan littattafai da ke dauke da rubutun Sinanci tare da fassarar Hausa aka ba kowa. Bayan haka, aka rarraba wa kowa rawar da zai taka da sunayen wadanda za a kwaikwayi muryoyinsu. Sunayen sun hada da Yuhao da Susu da sauransu. Da na shiga dakin daukar murya, sai aka hada ni da wata ‘yar kasar wadda ta iya harshen Hausa, su ne suka yi ta kula da yadda aikinmu ke tafiya.”
Ta ce, sun yi aiki na awa 12 kowace rana, daga karfe 9 na safe zuwa 9 na dare, bayan sun yi aiki sai huta, an tanadar musu abubuwan biyan bukata.
Dangane da abubuwan da suka burge ta kuma sai ta ce “Abu na farko da ya burge ni da wannan aikin shi ne akwai wadatar kayan aiki. Ma’aikatansu suna ba aikinsu muhimmanci, sannan sun iya rarrashin mutum ya saki jiki ya yi aikinsa yadda za a samu biyan bukata.”
Ta ce ta koyi darasin ya kamata mutum ya kasance mai alfahari da harshensa a kowane lokaci, ya dauki al’adarsa da mahimmanci, sannan ya daina wasa da aikinsa.