Darussan da za a amfana da su a cin zaben Janar Buhari
Tabbas akwai muhimman darussa da za mu amfana da su, game da lashe zaben da Muhammadu Buhari ya yi, a shekarar 2015, ga wasu daga ciki: 1. Mulki Allah ne yake ba da shi, in banda haka da bai ci zabe ba, saboda kwace mulki a hannun mai shi da kamar wuya.2. Gaskiya da rikon […]
Tabbas akwai muhimman darussa da za mu amfana da su, game da lashe zaben da Muhammadu Buhari ya yi, a shekarar 2015, ga wasu daga ciki:
1. Mulki Allah ne yake ba da shi, in banda haka da bai ci zabe ba, saboda kwace mulki a hannun mai shi da kamar wuya.
2. Gaskiya da rikon amana suna da mutukar muhimmanci a rayuwa, Janar Buhari bai mallaki abin da zai iya tsayawa Kansila ba, amma saboda gaskiyarsa mutane sun zabe shi kyauta a matsayin shugaban kasa.
3. Komai yana da ajalin da Allah ya sanya masa, ya tsaya takara har sau uku a baya bai samu nasara ba, amma sai yanzu a karo na hudu.
4. Zalunci ba ya dorewa, na dade ina jin cewa Goodluck ba zai ci wannan zaben ba, saboda a sunnar Allah azzalumi ba ya karko.
5. Muhimmancin komawa ga Allah, tabbas talakawa sum jima suna rokon Allah ya kawo musu canji, ga shi kuma yi amsa musu.
6. Siyasar Najeriya ta fara canzawa, a kasa, a tsare, a raka, a jira, a fada , da talakawa suka yi yana nuna yadda mutane suka san
‘yancinsu.
7. Duk shugaban da yake bin maslahar kansa bai damu da ta talakawa ba, to zai iya rasa kujerarsa a lokacin da bai zata ba.