Darussan labarin Hannatun Keffi

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A makon jiya muka kammala kawo muku labarin Hannatun Keffi, sannan muka bukaci ku aiko mana darussan da kuka koya daga labarin. Don haka a wannan makon za mu sanya sakonnin da kuka aiko mana da su ne.Za mu fara da sakon Khadija Sani Bello, Kano […]

Darussan labarin Hannatun Keffi
Darussan labarin Hannatun Keffi

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A makon jiya muka kammala kawo muku labarin Hannatun Keffi, sannan muka bukaci ku aiko mana darussan da kuka koya daga labarin. Don haka a wannan makon za mu sanya sakonnin da kuka aiko mana da su ne.
Za mu fara da sakon Khadija Sani Bello, Kano 08142283208 wanda ya ce: “Labarin Hannatun Keffi ya koya mini iyaye su daina auren dole. Mahaifiyarta ce ta jawo mata abin da ya same ta saboda son kudi. Allah Ya shirye mu baki daya.”
Ahmad Bature, Kano 08061624030: “Labari ya koya mini hakuri da kuma riko da kaddara, sannan mu kasance masu wadatar zuci.”
Abubakar Adam Musa Gwammaja, Kano 070329627450: “Labarin ya fahimtar da ni illar  rashin yin karatu a rayuwa.”
Usaini Yaro Kasuwar Arts da ke Hanyar Jirgin sama a Jabi, Abuja: Labarin ya koya mini hakuri a kan duk budurwar da ta ce ba ta sonka, to ka hakura da ita.”
Isma’il Alkyabba, Funtuwa: “Gaskiya labarin ya koya mini darussa da dama; daga ciki akwai yin tawakkali da jajircewa na ganin iyaye sun bar ‘ya’yansu su nemi ilimin addini da na zamani.  Kwadayin abin duniya da mahaifiyar Hannatu ta nuna shi ne ya jefa ‘yarta a halin da ta tsinci kanta a ciki.”
Maman Aiman, Funtuwa, Jihar Katsina: “Assalamu alaikum, tabbas na koyi darasi daga labarin Hannatun Keffi. Ya nuna cewa mafi yawancin matsalolin da ke faruwa cikin al’umma iyaye mata ke haddasa su. Don Allah iyaye mata a rika kula, a bar jefa ‘ya’ya ga halaka. Ba a zaman aure cikin jin dadi sai da so da yardar juna.”
Musa Ahmad, Kano: “Assalamu alaikum, labarin ya koyar da darussa masu yawa, amma darasin da ya fi jan hankali na shi ne: akwai hadari sosai ka auri matar da ba ta sonka, tun da ga shi Hannatu har ta kashe Alhaji Ibrahim saboda kiyayyar da take yi masa. Darasi na biyu da na koya kuma shi ne, ka aura wa ’ya’yanka uwa tagari, kasancewar a labarin mun gane cewa mahaifiyar Hannatu ce ta janyo duk abin da ya faru.”
Sunusi Musa, Kano, 08131994078: “Labarin ya koya mini matukar budurwa ta nuna maka ba ta sonka to akwai matsala. Ya kamata iyaye su rage son abin duniya, su rika ba ’ya’yansu mijin da suke so matukar yana da addini da sana’a.”
Maman Adam, Bauchi: “Labarin ya koya mini tsananin zafin ran uwa ba ya kai uwa da ‘yarta ga nasara.”  
Aminu M. MaiAdu’a, 07038243900: “Labarin ya koya mana darussa da dama. Na farko dai shi ne illar son abin duniya yake rufe wa uwaye ido su ba da ’ya’yansu ga wanda bai dace ba, sai kuma hukuncin da Hannatu ta dauka na kisa, to da ta yi tawakalli ta kuma roki Allah da Ya yi mata canji mafi alheri.”
Abdullahi Sa’id, dan Hausa, Kano: “Assalamu alaikum, labarin ya koya mini illar son zuciya da son duniya da kwadayi da taskun da soyayya take jefa ma’abota yinta, kamar yanda ta jefa Khalid bai ji ba, bai gani ba.”
Nazeef Yakubu Gidado, Bauchi: “Laba-rin ya koya mini darussa kamar haka: illar auren jahila, illar auren dole da kuma rashin hakuri.”  
Musa Ibrahim Tudun Wada dankade, Jihar Kano: “Assalamu alaikum, labarin ya koyar da ni illar auren matar da ba ta sonka, amma kuma inda adalci ya kamata a sassauta mata hukunci daurin rai-da-rai musamman ma tun da ta rage mugun iri, na mijinta matsafi.”
Safiyya Gafai: “Tabbas na koyi darussa masu yawa daga labarin Hannatun Keffi, musanman yadda mahaifiyarta take da kwadayin abin duniya, wanda ya haddasa ta ba da ’yarta ga mai asiri. Ashe kuwa ka ga da talaka da mai kudi duka Allah ne ya yi su, don haka nake kira ga iyaye su rika barin ’ya’yansu na auren wadanda suke so.”