Darussan labarin Hannatun Keffi (2)
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon za mu ci gaba da sanya sakonnin da kuka turo ne kan labarin Hannatun Keffi, labarin da muka dauki makonni shida muna kawo muku. Za mu fara da sakon Asma’u Adamu Saleh Hadejiya Fantai wanda ya ce: “Labarin Hannatun Keffi ya koyar da […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. A wannan makon za mu ci gaba da sanya sakonnin da kuka turo ne kan labarin Hannatun Keffi, labarin da muka dauki makonni shida muna kawo muku.
Za mu fara da sakon Asma’u Adamu Saleh Hadejiya Fantai wanda ya ce: “Labarin Hannatun Keffi ya koyar da ni abubuwa masu yawa, don haka nake so ku ci gaba da kawo mana ire-irensu.”
Fatima Zarah Umar, Kaduna, 08100509357: “Assalamu alaikum, hakika labarin abin dubawa ne, domin shi so wani abu ne na daban wanda Allah kan dora wa bawanSa, wanda ga shi ya yi sanadin da ya sa Hannatu ta rasa farin cikin rayuwarta gaba daya, kuma wannan babban kalubale ne ga dukkan wata ‘ya mace mai hankali cewa, hakuri da karbar rayuwa a duk yadda ta zo maka, ba lallai abin da kake so kake samu a rayuwa ba. A karshe ina ba iyayen mu shawara da su bar mu mu auri zabin mu komai talaucinsa, don samun farin cikinmu da kwanciyar hankali, don babu amfanin badi babu rai, kamar yadda ta kasance ga Hannatu.”
Nafisa Musa, Kano: “Labarin ya koya mini jin maganar iyaye wajibi ne, domin da Hannatu ta yi hakuri da ba ta rasa mahaifinta ba, sannan iyaye mata ya kamata su daina tirsasa wa ’ya’yansu don su auri wanda ba sa so, saboda son zuciyarsu. Abin da mahaifiyar Hannatu ta yi bai dace ba.”
Hajiya Hafsat, Minna: “Labarin ya koya mini darasi kamar haka: A bar ’yan mata su auri wanda suke so, a daina kwadayin abin duniya, shi kuma mahaifin Hannatu ya yi sakaci da ya bari matarsa ta fi karfinsa, zan iya cewa shi ne ummul’aba’isin duk abin da ya faru.”
Rahma M Sani, Zariya: “Labarin ya kunshi darussa kamar haka: 1 karancin tarbiyya. 2 Rashin hakuri 3 Illar talla 4 Rashin tawakkali da kuma rashin mika wa Allah lammura, wanda daga ba ya kan haifar da da-na-sani.”
A’isha dankano, Jega 08167798054: “Labarin ya koya mini darussa kamar hakuri, saboda da ta yi hakuri ta bar wa Allah komai da duk hakan ba ta faru ba. Iyaye su daina kwadayi, domin da mahaifiyarta ba ta yi mata auren dole ba, da hakan ba ta faru ba, sannan Hannatu ba ta yi biyayya ba, duk da cewa so ne ya rude ta.”
Malama Hauwa Jigawa (KHS): “Wannam labari yana dauke da darussa masu yawa, kamar a wurinmu iyaye mata idan muka yi nazari cikin labarin, komai ya faru ne sakamakon kwadayin mahaifiyar Hannatu. Idan aka duba mahaifinta ya yi bakin kokarinsa. Na biyu illar tallar, na uku kisan kai.”
Abba Anas, Barno 07038274780: “So kake mu ce kada iyaye su yi wa ’ya’yansu auren dole, haka nne amma na fi ganin laifinta da rashin tausayinta fiye da na mahaifiyarta.”
Amatullaah Mahmud, Yobe, 08030589931: “Labarin ya koya mini kada na wulakanta dan Adam duk yadda yake, na rungumi kaddara alkhairi ko akasinsa, sannan na kyautata wa iyaye a kowane hali don samun yardar Ubangiji.”
Shehu Sani Kantudu, Kano, 08031805594: “Labarin ya koya mini gane illar son kudi, domin an rasa rai uku.”
Garba Okene, Jihar Kogi: “Labarin ya koya mini: duk wani da namiji ya guji auren wacce ba ta sonsa. Akwai soyayya ma yaya aka kare da su.”
Ummi Bala Sulaiman, Jos: “Labarin ya ba ni tausayi, kuma ya koya mini darasi. Idan aka ce za a yi mini auren dole, to guduwa zan yi, ba zan ma zauna ba ballantana haka ta faru da ni, amma ba zan yarda in fada hannu banza ba. Allah Ya rufa mana asiri.”
Mun kammala