Darussan rayuwa bakwai daga abubuwa bakwai
Tare da sallama ga ma’abuta karanta wannan fili namu na Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, a wannan makon kuma, za mu duba wasu abebadai ne guda bakwai wadanda suna yi mana ishara ne ga rayuwarmu. Babu shakka za mu iya koyon wasu sirrika na rayuwa guda bakwai daga abubuwan nan guda bakwai.Wadannan abubuwa kuwa, […]
Tare da sallama ga ma’abuta karanta wannan fili namu na Sinadarin Rayuwa, Assalamu alaikum. Bayan haka, a wannan makon kuma, za mu duba wasu abebadai ne guda bakwai wadanda suna yi mana ishara ne ga rayuwarmu. Babu shakka za mu iya koyon wasu sirrika na rayuwa guda bakwai daga abubuwan nan guda bakwai.
Wadannan abubuwa kuwa, muna da su a gidajenmu, kuma kullum muna tare da su, sai dai kila abin da ba mu sani ba shi ne, a kullum sai sun koya mana darasin rayuwa, alhali ba mu ankara ba. Abubuwan nan su ne, rufin dakin da muke kwanciya a cikinsa. Na biyu, fankar da ke reto a saman dakin namu. Na uku, shi ne agogon da ke kafe ko like a bangon dakinmu. Na hudu shi ne, madubin da ke aje a dakinmu, wanda a kullum muke dubawa. Na biyar, ita ce tagar da ke like jikin dakinmu. Na shida, ita ce kalandar nan da ke manne jikin bangon dakinmu. Na bakwai kuma shi ne, kyauren da muke amfani da shi wajen rufe dakin namu idan za mu fita daga cikinsa.
Bari mu binciki wadannan abubuwa guda bakwai, domin mu ga irin darussan da muka ce suna koya mana a kullum rana ta Lillahi. Idan muka kalli rufin dakinmu, kullum abin da yake fada mana shi ne, mu yi burin hawa sama, yadda za mu kasance donono a saman kowa da komai, watau kamar yadda shi kansa rufin ya zama a saman ginin dakin gaba daya. Ke nan, a rayuwarmu, idan muka yi burin zama a sama, za mu mike tsaye ne domin neman hanyoyin samun haka. Idan muka hau sama, za mu zama tamkar inuwar da ke kare rana daga dukan raunananmu, kamar dai yadda rufin daki ke ba mu aminci, yana kare mu daga zafin rana, yana kare mu daga iska mai cutarwa, yana kare mu daga ruwan sama da sauransu.
Abu na biyu, watau fanka, kullum darasin da take koya mana shi ne, mu kasance cikin sanyi da aminci a zukatanmu. Watau kada mu rika daukar rayuwa da zafi, mu kasance masu aminci da bayar da aminci ga junanmu. Kamar dai yadda ita fanka take, kullum burinta ta huro iska mai dadi da aminci ga mai ita.
Abu na uku, watau agogo, a kullum da yake tillawa, gaya mana yake cewa lallai lokaci abu ne mai muhimmanci, kada mu rika bata shi a aikin banza. Idan ya tafi, ba zai dawo ba, don haka mu daina yin tadar nan ta African Time (halin dan Afirika na bata lokaci ).
Abu na hudu, watau madubi, a kullum yana yi mana nuni da cewa, duk abin da za mu aikata, mu duba tukunna. Watau mu yi nazarain dacewa ko rashin dacewarsa, kyawunsa ko akasin haka, kafin mu aikata. Kamar dai yadda idan mun yi kwalliya muke duba madubi kafin mu fita waje, watau domin mu gyara inda bai daidai ba. Rayuwa ma na bukatar haka.
Ita kuwa taga, a kullum tana gaya mana cewa, mu leka duniya, domin a cikinta ne za mu koyi ilimi mai yawa. Idan ka zauna gida, ba za ka ga komai ba, domin Hausawa ma sun ce na zaune bai ga gari ba, masu hikima kuwa suka ce tafiya mabudin ilimi.
Kalandar da ke like a bangon dakinmu kuwa, a kullum tana gaya mana cewa, mu zama cikin shiri, mu zama daidai da zamanin da muke ciiki. Wannan yana da muhimmanci, domin kuwa bai kamata ka yi aikin jiya a yau ba, ko kuma ka yi aikin gobe a yau ba. Abin ba zai yi daidai ba.
kyauren daki kuwa, a kullum idan ka zo bude shi, cewa yake ka tura da karfi, domin ka bude shi. Ke nan, al’amuran rayuwa sai da kokari da aiki tukuru sannan ake samun nasara. Duk kyauren da ka jure turawa da kwankwasawa da karfi, lallai wata rana zai bude maka, ka shiga dakin. Ke nan, idan dai kana nema, wata rana za ka samu.
Babban darasinmu na yau shi ne, lallai mu kasance muna rayuwa cikin lura da natsuwa, da neman ilmi. Kuma kada mu sake mu yi rayuwar zaman kashe wando. Allah Ya sanya mu dace, amin!