Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (1)

Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako, mun kalato muku wani labari ne, wanda ke dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara. Wani bawan Allah ne ya samu kansa cikin rikicin rayuwa, rikici da kidimewar da suka nemi […]

Darussan rayuwa daga labarin Malam Baba (1)

Assalamu alaikum ya ku ma’abuta shafin Sinadarin Rayuwa. Yaya aka ji da dawainiyar al’amuran rayuwa? A wannan mako, mun kalato muku wani labari ne, wanda ke dauke da darussa masu yawa, masu daidaita rayuwa zuwa ingantacciya kuma mai nasara.

Wani bawan Allah ne ya samu kansa cikin rikicin rayuwa, rikici da kidimewar da suka nemi hallakar da shi da duk abin da ya mallaka. Wannan mutum, Allah Ya wadata shi da abubuwa masu yawa na alheri, domin yana da ilimi da sana’a da gida na kansa, inda yake zaune da iyalinsa. Amma duk da haka ya kasa samun farin cikin rayuwa. A kullum yana cikin damuwa da tunani, wanda haka ya sanya ba ya da hakuri ko juriyar duk wani abin bakin ciki ko wata jarrabawar rayuwa da ta fuskance shi. Yakan yi fada ko ya bata da abokai ko makwabta saboda rashin jituwa komai kankantarsa, koda kuwa shi ne sanadin faruwarsa. Wannan rikicewa da ta samu wannan bawan Allah, har ta dauki aniyar zauta shi.

Wata rana yana cikin tafiya, sai Allah Ya hada shi da wani mutum mai hikima, wanda ya fahimci rayuwa sosai. Sakamakon mu’amalar da suka yi ta takaitaccen lokaci da wannan kidimammen mutum, sai mai hikimar nan ya fahimci mafi yawan matsalolin da ke yi masa tarnaki; ya dauki kudirin taimaka masa da shawara, yadda zai magance wadannan matsaloli da suka dabaibaye shi.

Malam Baba (mai hikima) ya samu shawo kan Baban Larai (mai fuskantar matsalar rayuwa). Sun samu wuri mai inuwa sun kebe da niyyar nazari da neman mafita ga al’amarin da ke damunsa.

“Kamar yadda na fara gaya maka matsalolina jiya,” inji Baban Larai, ya fara bayyana wa Malam Baba abin da ke wahalar da shi a rayuwa. “Na rasa abin da ke damuna, a kullum cikin bakin ciki nake.”

“Wane irin bakin ciki kuma? Daure ka yi mini bayani dalla-dalla, ta yadda zan fahimci matsalolin, sannan in san shawarwarin da zan ba ka, domin magance su,” inji Malam Baba.

Har Baban Larai ya buda baki zai yi magana, sai Malam Baba ya dakatar da shi, a yayin da ya sake buda baki yana cewa: “Abu ne da masana ke fada, suna cewa idan mutum ya sani kuma ya gano matsalolinsa, to ya samu rabin maganinsu. Babbar matsala ga likita ita ce idan ya kasa gane cutar da ke damun majinyacinsa. Don haka, kada ka boye mini duk abin da ke damunka, ni kuma insha Allahu zan san irin matakin da za ka dauka domin shawo kansu.”

“Na farko dai, ni a kullum gani nake na fi kowa fuskantar matsalar rayuwa. Nakan tuno matsalolin da na fuskanta tun shekaru masu yawa da suka gabata. Nakan tuna kura-kuran da na yi, da yin nadamar me ya sanya ma na aikata su. Ciwon wadannan kura-kurai da na aikata sukan dabaibaye mini zuciya, wanda haka kan kidima ni da bakin ciki.”

Za mu ci gaba

 

 

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos